Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gasar kofin duniya 2026: Ingila za ta kara da Mexico a zagayen ƴan 16
Takaitaccen Bayanin Wasa
Key Events
Ingila
- H. Kane Goal 75 minutes, Goal 86 minutes
Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo
- B. Cipenga Goal 7 minutes
Taƙaitattu
- Ingila za ta kece raini da Congo DR a zagayen ƴan 16 a gasar cin kofin duniya ta 2026
- Ana sa ran Declan Rice zai buga wa Ingila karawar a matakin dan wasan tsakiya
- Duk wadda ta yi nasara a wasan nan za ta fuskanci Mexico a filin Azteca a fafatawar zagayen ƴan 16
- Ko akwai ƙasar da za ta iya taka wa Faransa birki a gasar bana?
- Belgium za ta fafata da Senegal a daren yau a karawar zagayen ƴan 32
- Tawagar Faransa ta kai zagayen ƴan 16 a gasar kofin duniya tare da Mexico da kuma Norway
- Bayan Messi da Ronaldo – sabbin matasan da ke haskawa a gasar cin kofin duniya
- Sakamakon wasannin da aka buga Talata: Faransa 3-0 Sweden; Mexico 2-0 Ecuador; Ivory Coast 1-2 Norway
- Duk abin da ya kamata ku sani kan Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026
Rahoto kai-tsaye
Mohammed Abdu da taimakon AI
, FT: Ingila 2-1 DR Congo
Wadannan kwallaye biyu a daren yau da Kane ya ci sun mayar da shi a cikin yan takarar kyautar takalmin zinare a gasar bana.
Yadda Ingila ta ci kwallo na biyu da ya kaita zagayen yan 16, Ingila 2-1 DR Congo
Yadda aka gara kwallon, England 2-1 DR Congo
Ingila za ta fafata da Mexico a zagayen yan 16, Ingila 2-1 DR Congo
Ingila za ta fafata da Mexico a zagayen yan 16 a Azteca a Mexico ranar Litinin.
An tashi wasan, Ingila 2-1 DR Congo
Ingila ta kai zagayen yan 16, bayan doke DR Congo 2-1 a wasan yan 32 a gasar cin kofin duniya.
DR Congo ce ta fara cin kwallo tun a minti na bakwai da fara wasa daga baya Ingila ta farke a zagaye na biyu ta kuma kara na uku.
An yi karin minti shida, Ingila 2-1 DR Congo
Ingila ta yi canjin dan wasa, Ingila 2-1 DR Congo
Declan Rice ya nuna alama yana fama da ciwo, nan da nan Tuchel ya saka John Stones ya maye gurbinsa..
, Ingila 2-1 DR Congo
Wannan shi ne kwallo na 13 da Harry Kane ya ci a gasar cin kofin duniya jimilla. Kuma na biyar a wannan gasar cin kofin duniya ta 2026, saura ɗaya ya kamo Messi mai shida a raga, ya yi kan-kan-kan da Mbappe masu biyar-biyar a raga..
GOAL - England 2-1 DR Congo, Harry Kane
Kyaftin din tawagar Ingila ya ci kwallo mai kyau a tsakanin masu tsaron bayan DR Congo kuma daf da gida haka ya karbi kwallo ya kuma buga ko kallon raga bai yi ba, amma hakan ya ci kwallon ta fada ragar DR Congo - wadda take neman ganin samu ta rasa.
, Harry Kane (75 mins)
Inda Ingila ta farke sai kai kora take gidan DR Congo, amma ta kasa samun damar kara kwallo na biyu.
Wissa yana daga can sama, yana fatan ya samu kwallo ya tsinke zuwa gidan Ingila.
GOAL - England 1-1 DR Congo, Harry Kane
Harry Kane ya farkewa Ingila kwallon da kai, kuma ta huɗu a gasar nan kuma ta hudu a zagayen ziri daya kwale.
Wasan ya koma sabo.
, Ingila 0-1 DR Congo
Ana ci gaba da wasan, amma har yanzu Ingila ba ta samu wata gagarumar dama ba tun bayan da suka sha ruwa aka ci gaba da wasan.
An koma wasan bayan shan ruwa, Ingila 0-1 DR Congo
Ingila ta yi canji, inda ta cire mai tsaron baya, Djed Spence ta maye gurbinsa da dan gaba, Eberechi Eze.
Kenan Ingila za ta ci gaba da kai hari kenan.
An busa hutun shan ruwa, England 0-1 DR Congo
DR Congo ta tsare bayanta da kyau sosai, har yanzu Ingila na neman farke kwallo kafin ta sa me za ta yi nan gaba.
DR Congo ta sauya dan wasa, Ingila 0-1 DR Congo
Nathanael Mbuku ya fita daga wasan an kuma sac Meschack Elia madadinsa a DR Congo.
Ingila ta yi sauyin yan wasa biyu, Ingila 0-1 DR Congo
Ingila ta fitar da Noni Madueke da Marcus Rahford ta kuma maye gurbinsu da Anthony Gordon da kuma Bukayo Saka.
, Ingila 0-1 DR Congo
Kowanne lokaci za a iya fara canjin yan wasa kowacce tawaga tana da damar yin canji biyar-biyar, amma da yake wasa da saura sai an yi taka tsantsa, wata kila a tashi a minti 90 ko kuma ya kai 120.
, Ingila 0-1 DR Congo
Ingila na rike kwallo tana rabawa hagu da dama da tsakiya, Rashfod ya buga cikin gidan DR Congo, amma ta yi yawa ta yi waje.
, Ingila 0-1 DR Congo
Rashford ya kara samun dama ya buga da karfi amma golan DR Congo ya taba ya kuma fadi kasa kwallon na sama, mai tsaron bayan DR Congo ya buga, babu wani hadari a wannan lokacin.

