Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 09/02/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 09/02/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Gwamnan Kano ya naɗa sabon sakataren gwamnatin jihar

    Abba Kabir Yusu

    Asalin hoton, Kano State Govt

    Bayanan hoto, Sabon sakataren tsohon ma'aikacin gwamnatin ne

    Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya naɗa Umar Farouk Ibrahim a matsayin sabon sakataren gwamnatin jihar.

    Cikin wata sanarwa da Sakataren yaɗa labaran gwamnan, Sanusi Barure Dawakin Tofa ya fitar, ya ce gwamnan ya zaɓi Umar Ibrahim ne bisa ƙwarewar da yake da ita a fagen aikin gwamnati.

    Gwamnan ya ce yana fatan sabon sakataren gwamnatin zai taimaka wajen inganta harkokin gwamnatin jihar.

    "Muna sa ran zai taka muhimmiyar rawa wajen ciyar da gwamnatin jihar gaba, don cimma manufofin da ta sa a gaba", in ji sanarwar.

    A watan Disambar shekarar da ta gabata ne Gwamna Abba ya sauke tsohon sakataren gwamnatin jihar, a wani garambawul da ya yi wa majalisar zartarwarsa.

    Naɗin sabon sakataren zai soma aiki ne daga gobe Litinin 10 ga watan Fabrairu, a cewar sanarwar.

    Wane ne sabon sakataren gwamnatin?

    Umar Farouk Ibrahim ya samu digirinsa na farko a fannin kimiyyar siyasa a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya a shekarar 1985.

    Ya fara aiki a shekarar 1987 zuwa 2023 lokacin da ya yi ritaya bayan shafe fiye da shekara 30 yana aiki, kuma ya riƙe manyan muƙamai ɓangarori daban-daban a fadin jihar, ciki har da babban sakataren dindindin a ofishin sakataren gwamnatin jihar daga 2001 zuwa 2015.

    Haka kuma ya riƙe irin wannan muƙamin a ma'aikatar ayyukan gwamnatin jihar daga 2015 zuwa 2016.

    Ya kuma riƙe muƙamin sakataren gwamnatin jihar na riƙo har sau biyu a 2013 da 2014 a lokacin da sakataren gwamnatin na wancan lokacin ya tafi hutu.

    Ya kuma kasance cikin manyan kwamitocin gwamnati daban-daban.

  2. Sallama

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da hutun ƙarshen mako.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci, domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

    Sai ku ci gaba da kasancewa da mu, a wannan shafi da za mu ci gaba da sabunta muku labaran.