Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 11/12/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 11/12/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Ibrahim Kakangi, Abdullahi Bello Diginza da Aisha Sharif Bappa

  1. Gobara ta haifar da asarar miliyoyin naira a kasuwar Alaba Rago da ke Legas

    Wata gobara da ta tashi a safiyar ranar Laraba a kasuwar Alaba Rago da ke jihar Legas, ta haddasa asarar miliyoyin naira.

    Cikin wata sanarwa da hukumar agajin gaggawa ta jihar ta fitar, ta ce gobarar ta tashi ne cikin dare.

    Har kawo yanzu ba a san abin da ya haddasa gobarar ba.

    A cewar, babban sakataren hukumar agaji ta jihar, Dr Femi Oke-Osayintolu, jami'an hukumarsu sun isa kasuwar da wuri bayan kiraye-kirayen wayar da aka rika yi musu daga kasuwar.

    Ya ce, koda isar jami'an nasu sun tarar wutar ta fara cin shaguna.

    Jami'an hukumar kashe gobara ma sun isa wajen akan lokaci inda basu yi wata-wata ba suka fara kashe wutar a cewar jami'in hukumar agajin.

    Ya ce, akwai mutanen da suka yi kokari wajen kashe wutar ma.

  2. Wani matashi ya caka wa mahaifiyarsa wuƙa a Bayelsa

    Ana zargin wani matashi dan shekara 22 mai suna Godwin daga yankin Elebele a karamar hukumar Ogbia da ke jihar Bayelsa da cakawa mahaifiyarsa wuka bayan ya gaza samun nasarar amfani da ita wajen yin tsafi.

    A cewar wasu majiyoyi, mutumin da ake zargin ya dawo garin ne makonni kalilan da suka wuce bayan ya yi bulaguro na tsawon watanni a makwabciyar jihar inda ya je wajen wata matattara ta 'yan Yahoo da ake kira da HK.

    Da yake tabbatar da lamarin, shugaban kungiyar matasa na kauyen Elebele, Kwamared Precious Okala, ya shaida wa manema labarai cewa an kira shi da misaln karfe 6 na yammacin ranar da lamarin ya afku inda daga zuwansa wajen ya tarar da gawar wata mace kwance cikin jini da kuma danta nata wanda matasan garin suka daurewa hannu a gefe.

    Ya ce, " Makwabtan yaron sun ce sun ji ana ta kai ruwa rana a ranar da zai aikata ta'asar inda dadabniya ta yi yawa tsakaninsa da mahaifiyar tasa daga bisani kuma suka ji shiru ashe ya caka mata wuka ne a cikinta lamarin da ya yi ajalinta.

    A bangare guda kuma, an mika mutumin da ake zargin zuwa ga rundunar 'yan sandan jihar ta Bayelsa.

    Mai magana da yawun rundunar, Musa Mohammed, ya ce an mika lamarin ga hannun sashen binciken manyan laifuka na jihar don gudanar da cikakken bincike.

  3. Adadin mutanen da ake fataucinsu a duniya ya karu - MDD

    Ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai yaki da muggan kwayoyi da manyan laifuka ya ce adadin mutanen da ake fataucinsu a duniya ya karu da kashi ashirin da biyar cikin dari tun kafin barkewar cutar Korona.

    A cikin rahotonta na baya-bayan nan, wanda ya tattaro bayanai daga shekarar 2022, hukumar ta ce fataucin yara na karuwa a kasashe masu karfin tattalin arziki, kuma galibi ƴan mata ne suka fi yawa cikin wadanda ake safara.

    Rahoton ya kuma ce an samu karuwar wadanda ake tilastawa yin aikin dole.

    Ya ce a yankin kudu maso gabashin Asiya, gungun kungiyoyin masu aikata laifuka na safarar mutane masu ilimin fasaha, tare da tilasta musu yin zamba ta Intanet

  4. Isra'ila ta tabbatar da hari kan sansanin sojin ruwan Syria

    Isra'ila ta tabbatar da kai wasu hare-hare kan sansanin sojin ruwan Syria, a wani bangare na kokarin da ta ke wajen lalata kayayyakin sojin kasar bayan faduwar gwamnatin Assad.

    Cikn wata sanarwa, rundunar sojin Isra'ila, ta ce jirgin ruwanta ya isa gabar ruwan Al-Bayda da Latakia a daren ranar Litinin, inda aka jibge jiragen ruwa 15.

    BBC ta tabbatar da wasu hotunan bidiyo da suka nuna yadda wani abu ya fashe a gabar ruwan Latakia lamarin da aka ga jiragen ruwan da ke wajen duk sun lalace.

    Rundunar sojin ta Isra'ila ta kuma ce jiragen samanta na yaki sun kai wasu hare-hare 350 sassan Syria, yayin da sojojinta na kasa kuma ke nausawa cikin wuraren da suka mamaye wadanda ke tsakanin Syria da kuma tuddan Golan.

    Tun da farko, wata kungiyar kare hakkin dan adam dake Birtaniya mai suna Syrian Observatory for Human Rights, ta ce ta kiyasta hare-hare 310 da Isra'ila ta kai tun bayan hambarar da gwamnatin Assad da 'yan tawaye suka yi.

  5. Shugaban Jamus na ziyarar aiki a Najeriya

    Shugaban ƙasar Jamus, Frank-Walter Steinmeier na ziyarar aiki a Najeriya.

    Mista Steinmeier ya isa Najeriya ranar Talata da daddare, nda ya samu tarbar ministan Abuja, Nyesom Wike bayan saukarsa a filin jirgin saman Abuja.

    A ziyarar da ake sa ran ta kwana uku ce, Shugaban na Jamus zai gana da Shugaba Bola Tinubu na Najeriya da kuma shugaban hukumar Ecowas, Alieu Omar Touray a Abuja.

    Daga nan Mista Steinmeier zai wuce birnin Legas inda zai gana da wakilan kasuwanci da jami'an ƙungiyoyin fararen hula da na al'adu, ciki har da Farfesa Wole Soyinka, kamar yadda gidan Talbijin na Channels ya ruwaito.

  6. 'Yansandan Koriya ta Kudu sun kai samame ofishin shugaban ƙasar

    'Yan sanda a Koriya ta Kudu sun kai samame ofishin shugaban ƙasar, a wani ɓangare na bincike kan yunƙurinsa na ayyana dokar soji a ƙasar a makon da ya gabata.

    An kama wasu daga cikin manyan jami’an gwamnatin Yoon Sook Yeol da kwamandojin soji bisa zarginsu da hannu a yunƙurin aiwatar da dokar.

    Har yanzu dai Koriya ta Kudu na cikin ruɗanin siyasa bayan yunƙurin ayyana wannan dokar a makon jiya.

    An hana Shugaba Yoon barin ƙasar, yayin da ake bincikensa kan aikata laifin cin amanar ƙasa amma har yanzu ya ci gaba da kasancewa kan karagar mulki.

  7. Biden ya soki aniyar Trump ta haraji kan manyan ƙawayen Amurka

    Shugaba Biden na Amurka ya kare ci gaban da ya samu a fanni tattalin arziki ya kuma ƙalubalanci gwamnatin Trump mai zuwa da ta ci gaba da inda ya tsaya.

    Da yake jawabi a Washington, Mista Biden ya yi tir da shirin Mista Trump na ɗora haraji kan manyan abokan kasuwancin Amurka, Mexico da Canada da kuma China.

    Yayin da ake ganin Mista Trump ya lashe zaɓen ne saboda tsadar rayuwa da ta yi wa Amurkawa dabaibayi, Shugaba Biden ya ce Mista Trump zai gaji tattalin arziki mafi ƙarfi a tarihin Amurka.

  8. Assalama alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar Laraba, ta Bawa ranar samu, kamar yadda Hausawa ke yi mata kirari.

    Yau ma kamar kullum mun fito domin fara kawo labaran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya daban-daban, musamman Najeriya da makwabtanta.

    Kuna iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.