Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 11/12/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 11/12/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Ibrahim Kakangi, Abdullahi Bello Diginza da Aisha Sharif Bappa

  1. Rufewa

    Masu bibiyarmu a wannan shafin, a nan muka kawo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni da muke yi kai-tsaye na yau, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu ɗaura.

    A madadin sauran abokan aiki, Isiyaku Muhammed ne yake cewa mu kwana lafiya.

  2. Ƴansanda sun kama gomman magoya bayan zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Ghana

    Ƴansandan Ghana sun kama sama da mutum 100 - yawanci daga ɓangaren jam'iyyar hamayya masu goyon bayan zaɓaɓɓen shugaban ƙasar, John Mahama bisa zargin sun tayar da zaune tsaye bayan zaɓe.

    An zargi magoya bayan Mahama ɗin ne da kai farmaki kan wasu kadarorin ƙasar, da sace-sace, tare da jikkata wasu sojoji da ƴansanda.

    An kuma zargi matasan da ƙona wasu ofisoshin hukumar zaɓe saboda jinkirin sanar da sakamakon zaɓen.

    Mahama dai ya fito ya yi Allah-wadai da sace-sacen, sannan ya yi kira ga shugaban ƙasa Nana Akufo-Addo da jami'an tsaro su ɗauki mataki.

    Mahama dai ya lashe zaɓen ƙasar ne da kashi 56.6 na ƙuri'un ƙasar, inda ya doke mataimakin shugaban ƙasar, Bawumia, wanda ya samu kashi 41.6 na ƙuri'un.

  3. Sojoji sun kama masu garkuwa da mutane tare da ƙwato alburusai a Filato

    Dakarun sojojin da aikin soji na musamman na ‘Operation SAFE HAVEN’ sun sanar da kama masu garkuwa da mutane tare da ƙwato alburusai a ƙaramar hukumar Bassa a jihar Filato da ke arewacin Najeriya.

    A wata sanarwa da kakakin aikin na Operation Safe Haven, Samson Nantip Zhakom, ya fitar, ya ce, "sojojin sun kai farmakin ne a maɓoyar masu garkuwa da mutanen, inda suka samu nasarar kama wasu ƴanbindiga a yankin Rafiki."

    Ya ce sun kuma kama alburusai guda 439 da wasu makamai.

    Sanarwar ta ƙara da cewa sun yi aikin na musamman domin tabbatar da mutane sun samu sukunin gudanar da hidindimun kirsimeti da sabuwar shekara.

  4. Rikicin daba ya ɗaga hankalin mutane a Kano

    A jihar Kano, har yanzu ana ci gaba da zaman ɗar-ɗar a wasu unguwanni sakamakon rikicin ƴandaba da ya dawo a wasu unguwanni tun a ƙarshen mako.

    Ko a jiya da daddare ma sai da aka gwabza a yankin Ƙofar Mata da Zango inda lamarin ya ya yi sanadiyar jikkata wasu.

    Rikicin na baya-bayan nan ya taso ne bayan kammala wasan ƙwallon ƙafa tsakanin Kano Pillars da Katsina United, inda bayanai suka nuna cewa ƴandaba sun riƙa auka wa mutane a cikin unguwa.

    Rikicin daba ya daɗe yana ci wa mutanen Kano tuwa a ƙwarya, inda lokaci zuwa lokaci yake tashi tsakanin ƴan unguwanni, inda rikicin ya zama kamar na sari-ka-noƙe.

    A wani rubutu da kakakin ƴansandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Litinin, ya ce,: "Kwamishinan ƴansandan Jihar Kano, CP Salman Dogo Garba ya shiga unguwarnin Ƙofar Mata, Yakasai, Rimi da Zango a yau, ya bada umarnin gudanar da bincike da kama duk wanda yake da hannu kan rikicin daba a unguwarnin."

  5. Waɗanda suka rasu a zanga-zangar Mozambique sun karu zuwa 110

    Mutum 34 ne suka rasu a zanga-zangar bayan zaɓe a Mozambique a makon jiya, kamar yadda ƙungiyoyin sa kai na ƙasar suka bayyana.

    Wannan ya sa adadin waɗanda suka rasu ya ƙaru zuwa 110 a zanga-zangar wadda ta ɓarke tun bayan babban zaɓen ƙasar a watan Oktoba.

    Sai dai har yanzu hukumomi a ƙasar ba su tabbatar da adadin waɗanda suka rasu ɗin ba.

    Ƙungiyar Amnesty ta tabbatar da mutuwar mutanen, inda ta yi kira ga gwamnati da ta kawo ƙarshen abin da ta kira amfani da ƙarfi kan masu zanga-zanga.

    A ranar 24 ga Oktoba ne hukumar zaɓen ƙasar ta sanar da ɗantakarar jam'iyyar Frelimo, Daniel Chapo a matsayin wanda ya lashe shugaban ƙasar da kashi 71 na ƙuri'un da aka kaɗa, amma ɗantakara mai zaman kansa, Venancio Mondlane wanda ya samu kashi 20 na ƙuri'un ya ce shi ne ya lashe zaɓen, amma aka masa maguɗi.

  6. Sojojin Najeriya sun ceto mutum huɗu da aka yi garkuwa da su a Delta

    Sojojin Najeriya sun ce sun ceto mutum huɗu da aka yi garkuwa da su a jihar Delta bayan musayar wuta da suka yi da ƴanbindiga.

    A wata sanar da mataimakin daraktan hulɗa da jama'a na rundunar, Emmanuel Onoja ya fitar, ya ce, "sojojin Najeriya sun ceto mutum huɗu a wata maɓoyar masu garkuwa da mutane a dajin Ugbolu da ke jihar Delta."

    Ya ce sojojin sun kai farmakin ne a ranar Litinin, 9 ga watan Disamba, bayan sun samu rahotannin sirri kan ayyukan ƴanbindigar.

    Ya ce sojoji sun kai mutanen asibiti domin a duba lafiyasu, sannan suka miƙa ga su iyalansu.

  7. Ƴanmajalisar wakilai na kudancin Najeriya sun goyi bayan ƙudurorin haraji

    Gamayyar ƴanmajalisar wakilai daga kudancin Najeriya sun bayyana goyon bayansu ga ƙudurorin haraji na Tinubu.

    Ƴanmajalisar sun bayyana haka a zantawarsu da manema labarai ranar Talata bayan tattaunawar da suka yi a gidan mataimakin shugaban majalisar wakilai, Benjamin Kalu.

    Sun ce suna maraba da ƙudurorin, sannan suka ce za su bai wa ƙudurorin duk goyon bayan da suke buƙata domin inganta tattara harajin ƙasar, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

    Shugaban gamayyar ƴanmajalisar, Nicholas Mutu, ya ce za su gana da duk waɗanda abin ya shafa domin tabbatar da an tafi da kowa.

  8. 'Gudun wuce ƙima ne ke jawo haɗurra a Najeriya'

    Hukumar kare haɗura ta Najeriya da ake kira Road Safety ta ce yawan lodi da gudun wuce ƙima da direbobi ke yi shi ke haifar da yawan haɗura da ake fama da su a irin wannan lokaci na ƙarshen shekara a Najeriya.

    Shugaban hukumar na ƙasa Malam Shehu Muhammad ne ya bayyana hakan, a wani ɓangare na shirye-shiiryen da suke yi na tun karar lokutan hutu a duniya.

    Wannan na zuwa ne daidai lokacin wata motar haya ɗauke da fasinjoji 14 ta yi haɗari a kan hanyar Hadeija da ke jihar Jihar Jigawa, wadda rahotanni suka ce mutum 14 ne cikin motar da aka yi wa loadin wuce iyaka.

  9. Ƴanbindiga sun kashe sojojin Nijar fiye da 90

    Wani mummanan hari da ake zargi ƴanbindiga ne suka kai ya yi sanadiyar kashe sojojin Jamhuriyar Nijar sama da 90 da fararen hula fiye da 40.

    Wasu majiyoyi daga ƙasar sun ce ƴanbindigar sun kai hare-hare ne a ƙauyen Chatoumane, da Anzourou a lokaci guda dukkansu a yankin Tillaberi.

    A ɗaya daga cikin hare-haren da ake tunanin ya fi muni, ƴanbindigar, waɗanda suka saje da fararen hula sun buɗe wuta kan sojoji a kasuwar ƙauyen Chatoumane, amma kuma sojoji ba su samu damar mayar da wutar ba saboda gudun kashe waɗanda babu ruwansu.

    Wasu majiyoyi daga ƙasar sun ce an kashe sojoji 91 da fararen hula 43 - amma ana tunanin har da ƴanbindigar a ciki.

    Har yanzu hukumomi a ƙasar ba su ce komai ba game da hare-haren.

    A watan Yunin da ya gabata, an kashe aƙalla sojoji da fararen hula 20 a wasu hare-hare da ƴanbindigar suka kai a kusa da iyakar ƙasar da Burkina Faso.

    Nijar ta haɗa alaƙar tsaro da Mali da Burkina Faso ne bayan ficewa daga ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma wato Ecowas.

  10. Kayayyakin da aka shigo da su daga Malta sun kai na naira biliyan 766.81 a ƙarshen 2024

    Kuɗin da aka kashe domin shigo da man fetur daga ƙasar Malta ya ƙaru zuwa N766.81 a rubu'i na uku na shekarar 2024, kamar yadd alƙaluma hada-hadar ƙasashen waje da hukumar ƙididdiga ta ƙasa NBS suka nuna.

    Duk da cewa rahoton bai tantance waɗanne irin kayayyaki ne aka shigo da su daga Malta ba, amma lamarin ya ja hankalin mutane saboda zargin da Aliko Dangote ya yi a baya cewa ana shigo da man fetur daga ƙasar.

    Sai dai bincike y nuna cewa babu bayanin shigo da wani kaya daga Malta a rubu'i na farko da na biyu na shekarar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayyana.

    Amma a rubu'i na uku, sai aka samu ƙaruwar shiga da kayayyakin daga ƙasar.

    Ƙididdigar ta NBS ta nuna cewa Malta ce ƙasa ta biyar a cikin ƙasashen da aka fi shigo da kayayyakinsu Najeriya.

  11. Majalisar jiha ta cire Lamidon Adamawa a matsayin shugaban majalisar sarakuna

    Majalisar dokokin jihar Adamawa da ke arewa maso gabshin Najeriya ta amince da ƙudurin kafa wasu masarautu uku masu daraja ta ɗaya a jihar.

    Dokar, wadda yanzu take jiran sa hannun gwamnan jihar, Ahmadu Finitiri, na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan gwamnan ya sa hannu kan wata dokar ta ƙirƙirar gundumomi 84 a 4 ga Disamba.

    A wata wasiƙa da gwamna da aika majalisar, ya buƙace su da su amince da ƙudurin naɗawa da cire sarakuna na jihar, wadda za ta ba gwamnan damar ƙirƙirar sababbin masarautu, naɗa sarakuna da cire su, kamar yadda muka kalato daga jaridar Premium Times.

    Ƙudurin ya tsallake karatu na farko da na biyu a majalisar a ranar Litinin, sannan a ranar Talata ƴanmajalisar suka amince da shi, inda yanzu ake jiran sa hannun gwamna domin ya zama doka.

    Sabuwar dokar, ta cire wa Lamiɗon Adamawa, Mustapha Barkindo, muƙaminsa na shugaban majalisar sarakunan Adamawa na dindindin, inda yanzu zai riƙa zagawa da matsayin tsakanin sarakunan jihar masu daraja ta ɗaya.

    Sannan a dokar ta farko da gwamnan ya sa hannu, an rage ƙasar Lamidon Adamawa daga ƙananan hukumomi takwas zuwa uku.

    A baya, ƙananan hukumomin Hong, Song, Gombi, Fufore, Girei, Yola ta arewa, Yola da kudu, da Mayo-Belwa suna ƙarƙashin masarautar Adamawa ne, amma yanzu Girei, Jimeta da Yola ne kawai suke ƙarƙashin masarautar.

  12. An kashe ministan Taliban a harin ƙunar bakin wake

    An kashe ministan kula da ƴangudun hijirra na Afghanistan, Khalil Haqqani, a wani harin ƙunar bakin wake.

    Shi ne babban jami'in gwamnatin Taliban da ka kashe tun bayan da ƙungiyar ta ƙwace mulkin ƙasar shekara uku da suka gabata.

    Wata majiya daga ma'aikatar harkokin cikin gida ta ce an kashe shi ne tare da wasu mutum shida.

    Ƙanin Khalil Haqqani ne shugaban ƙungiyar Haqqani wadda ake tsoro matuƙa a ƙasar.

    Ɗanuwansa, Sirajuddin, wanda shi ne ministan harkokin cikin gida na gwamnatin Taliban, shi ne na farko a cikin waɗanda Amurka take nema ruwa a jallo.

    Har yanzu babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin harin.

  13. Ƴantawayen HTS sun ƙwace garin Deir Ezzor mai albarkatun mai a Siriya

    Ƴantawayen da suka hambarar da gwamnatin Bashar al-Assad a Siriya sun ce sun ƙwace iko da birnin Deir Ezzor mai albarkatun mai da ke gabashin ƙasar.

    Mai magana da yawun yantawayen na ƙungiyar HTS ya ce mayaƙan Kurdawa da ke samun goyon bayan Amurka sun janye daga yankin.

    Wani babban jam'in Ƙurdawan da ke iko da arewaci da kuma gabashin Siriya, Sahih Muslim, ya shaida wa BBC cewa ba su da matsala da sabuwar gwamnatin Muslinci ta Siriyar.

    Sai dai ya ce akwai hannun Turkiyya a cikin rikicin da ke faruwa a yankin, saboda tana ƙoƙarin kafa sabuwar Daular Usmaniyya.

  14. Babban layin lantarki na Najeriya ya sake lalacewa

    Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, ofishin dake kula da babban layin wutar lantarki a Najeriya, ya ce layin ya sake daukewa da misalin karfe 2 da minti tara na rana agogon kasar a ranar Laraba.

    Cikin sakon, ofishin ya ce tuni aka fara kokarin dawo da layin bakin aiki.

    Daukewar babban layin wutar lantarkin da ake yawan samu a kasar, na janyo babbar asara musamman ga 'yan kasuwa wadanda ke neman kudi ta hanyar amfani da lantarki.

    Ofishin, ya nemi afuwar al'ummar Najeriya, yana mai cewa tuni aka dukufa don dawo da wutar.

    An samu daukewar babban layin wutar lantarkin sau 12 ke nan tun daga farkon shekarar 2024 kawo yanzu.

    Babban layin wutar lantarki na Najeriya - power grid a Turance - gungun layuka ne da suka haɗa tashoshin samar da lantarki da ke bai wa dukkan sassan Najeriya wuta.

    A taƙaice, wata ma'dana ce da ke ɗauke da dukkan lantarkin da ake sha a Najeriya. Haka nan, ba wani wuri ba ne guda ɗaya, tarin layuka ne a wurare daban-daban.

    An tsara shi ne don ya yi aiki ta wasu taƙaitattun hanyoyi musamman dangane da yawan wutar da ake da ita, da tsaron lafiyarsa.

  15. An kashe ministan Taliban a harin kunar bakin wake

    An kashe ministan kula da harkokin ƴan gudun hijira na Afghanistan, Khalil Haqqani, a yayin wani harin ƙunar baƙin wake.

    Shine ne dai babban jami'in gwamnatin Taliban na farko da aka kashe tun bayan da ƙungiyar ta karbi mulki shekaru uku da suka wuce.

    Ma'aikatar harkokin cikin gida ta ƙasar ta ce an kashe shi ne tare da wasu mutum shida a lokacin da yake ƙoƙarin fita daga ofishinsa.

    Har yanzu babu wanda ya dauki alhakin kai harin.

  16. An samu raguwar kamuwa da cutar Malaria a duniya

    Wani sabon rahoto da Hukumar Lafiya ta Duniya ta fitar ya nuna cewa an samu raguwar masu kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro wato maleriya a duniya, da kimanin mutum biliyan biyu inda aka samu raguwar masu mutuwa daga cutar tun daga shekarar 2000 kawo yanzu.

    Sai dai rahoton ya ce har yanzu akwai miliyoyin mutane da ke fama da wannan cuta a duniya musamman a nahiyar Afirka, inda adadin masu kamuwa da cutar ya kai kashi 95 cikin dari, sakamakon rashin ingantaccen tsarin kiwon lafiya da kuma hanyoyin samar da kariya daga cutar.

    Duk da wannan nasarar da aka samu a cikin wadannan Shekarau, Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayana cewa har yanzu cutar zazzabin cizon sauron na ci gaba da shafar mutane da dama a Afirka, musamman mata masu juna biyu da yara kanana wadanda su ne sahun gaba daga cikin masu fuskantar barazana daga wannan cuta.

    Daga watan Nuwambar shekarar 2024, an samu kimanin kasashe arba’in da hudu da kuma wani yanki guda daya da suka zama na farko a duniya da hukumar lafiya ta duniya ta ce ta kawar da cutar maleriya dungurungum a cikinsu.

    Kazalika, akwai kasashe da dama da ke daf da cimma wannan matsayi. Inda kimanin kasashen ashirn da biyar a yanzu daga cikin kasashe tamanin da uku da al’ummarsu suka fi fama da zazzabin cizon sauro, suka bayyana raguwar matsalar.

    Daraktan hukumar Lafiyar, Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce duk da an samu gagarumin ci gaba a wannan bangare na yaki da cutar maleriya a wasu sassan duniya, amma a kasashen Afirka har yanzu akwai fatan da ake da shi na neman mafita daga wannan barazana.

    Tun a shekarar 2015 WHO, ta ce an samu cimma kashi 16 cikin 100 na muradun da ake da sun a samun raguwar mace-mace a dalilin cutar ta Maleriya.

    Sai dai wata kididdiga da hukumar ta fitar a 2023 ta nuna cewa a duk cikin mutum dubu daya ana samun kashi hamsin da biyu da ke mutuwa sakamakon cutar, abin da ke nuna karuwar masu rasa rayukansu fiye da sau biyu, wanda kuma ya yi hannun riga da muradin nan na shirin kawar da cutar maleriya nan da shekarar 2030.

    A farkon wannan shekarar ministocin lafiya da ga kasashen Afirka sha daya da suka hada da Burkina Faso da Kamaru da Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo da Ghana da Mali da Mozambique da Nijar da Najeriya da kuma Sudan, sun yi wani taro inda suka saka hannu kan wata yarjejeniyar da ke fafutukar yaki da maleriya da kuma manufar inganta tsarin kiwon lafiyar kasashen.

  17. An cinna wa kabarin mahaifin Bashar al-Assad wuta a Syria

    Hotunan da ke fitowa daga lardin Latakia na yammacin Syria sun nuna yadda mayaƙan ƴantawaye suke tsaye a gefen kabarin tsohon shugaban ƙasar, Hafez al-Assad wanda aka cinna wa wuta.

    Za a iya ganin wani ɓangare na kabarin da kuma wani akwatin gawa na ci da wuta, wanda ke nuna cewa an fito da akwatin ne daga cikin kabarin.

    A shekarar 2000 ne mahaifin Bashar al-Assad ya rasu, inda aka binne shi a wani wuri na musamman a ƙauyensu,, Qardaha.

    Bari mu kawo muku wasu hotunan da aka dauka gaban kabarin mahaifin hambararren shugaban Syria Bashar a--Assad.

    Hotunan da kamfanin dillanci na AFP, sun nuna mayakan 'yan tawayen a galabaice inda wasu daga cikinsu ke kallon kabarin wasu kuma sun daga tutar kasar.

    A cewar kungiyar kare hakkin dan ta Syria da ke Birtaniya wato Syrian Observatory for Hman Rights, 'yan tawayen sun cinnawa kabarin wuta wanda ke a Latakia wato asalin garin al'ummar Alawite.

    Ga wasu hotnan da aka dauka a yayin kona kabarin kabarin:

    Yadda ainihin wajen da aka binne Hafez al-Assad ya ke kafin mutuwarsa a 2000.

  18. An ci tarar wani mutum fiye da fan 800 bayan ya jefar da sigari a kan titi

    An umarci wani mutum da ya biya tarar fiye da fan 800 bayan ya yasar da sigari a kan titi.

    Carl Smith, daga New Addington a Croydon dake kudancin Ingila, ya bayyana gaban kotun majistreda ke Bromley a ranar 3 ga watan Disambar 2024, bayan ya gaza biyan tarar da aka shata masa saboda yasar da sigarin da ya yi amfani da ita a harabar wata kasuwa tun a ranar 23 ga watan Mayun 2024.

    An same shi da laifin karya dokar sashe na 87 na dokar kare muhalli ta 1990, inda aka umarce shi da ya biya tarar fan 833.

    Wannan shari'a ta mutumin ita ce ta 12 da kotun da ke Bromley ta yanke hukunci akan irin wannan laifi.

    Shari'a makamanciyar wannan ta baya-bayannan ita ce wadda aka yi wa wata mata da wani mutum da suka yasar da sigarin da suka sha a farkon shekarar 2024, inda aka umarcesu su biya tarar fan 731 kowannensu.

    Alkalin kotun mai shari'a Angela Page, ta ce suna daukar wannan mataki ne saboda matsalar yasar da sigarin da aka sha akan titi ta zama ruwan dare game da duniya, shi ya sa duk wanda aka samu da yasar da irin wannan ake cin shi tara.

    Ta ci gaba da cewa tana mai bawa mutane shawara da su daina zubar da shara a ko ina, ya kamata kowa ya samu wajen da zai rika zubar da shararsa.

  19. An kama fiye da mutum 100 sanadiyyar rikicin bayan zaɓen shugaban Ghana

    'Yan sanda a Ghana sun kama mutum fiye da 100 yawancinsu magoya bayan zababben shugaban kasar John Mahama saboda nuna rashin da'a.

    Ana zargin magoya bayan sabon zababben shugaban wadanda ke neman guraben aiki da kai wa cibiyoyin gwamnati hari tare da sata da kuma tayar da tarzoma lamarin da har ya raunata 'yan sanda da sojoji.

    Kazalika magoya bayan sabon shugaban kasar sun kai hari wasu ofisoshin hukumar zabe biyu saboda jan kafar da aka yi kafin sanar da sakamakon zabe.n shugaban kasa dana 'yan majalisun dokokin da aka yi a ranar Asabar din da ta wuce.

    John Mahama, ya yi alawadai da abin da ya faru inda ya yi kira ga shugaba Nana Akufo-Addo da hukumomin tsaro da su dukin matakin da suka dace wajen shawo kan wannan matsala da ta kunno kai.

    Shi kuwan mataimakin shugaban na Ghana, wato dan takarar shugaban kasar jam'iyya mai mulkin da ya sha kayi, Bawumiya, kira ya yi ga zababben shugaban kasar da ya ja kunnen magoya bayansa.

  20. 'Yan gudun hijirar Syria sun fara komawa gida

    'Yan kasar Syria da dama ne suka fara komawa gida kasarsu daga Turkiyya da kuma Lebanon tun bayan faduwar gwamnatin Assad.

    Hotunan komawar ta su da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda Siriyawan ke tafiya dauke da kayansu yayin da wasu kuma ke daukar 'ya'yansu kanana a kusa da iyakarsu da Syrian.

    Siriyawan na tafiya ne ta iyakar Cilvegözü da ke Turkiyya.

    Akwai wasu Siriyawan da ke bi ta iyakar gabashin Lebanon inda suke tsallakawa don komawa kasarsu.

    Yawancinsu dai na cike da fatan cewa zasu koma kasarsu don ci gaba da rayuwa kamar yadda suka saba a baya.