Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 12/09/2025.

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 12/09/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Usman Minjibir da Aisha Babangida

  1. Hilda Baci na shirin kafa tarihin dafa shinkafa mafi yawa a duniya cikin tukunya ɗaya

    Fitacciyar mai girkin nan ƴar Najeriya - da ta taɓa kafa tarihin shafe tsawon lokaci tana girki a duniya - ta fara yunƙurin kafa wani sabon tarihin ta hanyar dafa shinkafar da ba a taɓa dafa mai yawa irinta ba.

    Hilda Baci ta ɗora wata ƙatuwar tunkunyar da ba a taɓa girki a irinta ba, domin girka dafa-dukar shinkafa.

    Ɗaruruwan mutane ne suka hallara a wurin da take girkin a birnin Legas da ke kudancin ƙasar domin shaida wannan gagarumin girki.

    Matashiyar ta ɗauki mutane masu yawa aiki domin taimaka maka kafa wannan babban tarihi.

    Baci ta bayyana kayayakin da ta tanada domin wannan gagarumin aiki da suka ƙunshi:

    • Shinkafa kilogiram 4,000 kwatankwacin buhu 80 mai nauyin kilogiram 50, (wato buhuna masu kwano 17, guda 80)
    • Timatirei mai nauyin 1200, katan 500 na timatirin gwangwani
    • Magi da kayan ɗanɗano masu tarin yawa
    • Albasa kilogiram 600
    • Ruwa kilogiram 6,000
    • Nama kilogiram 168
    • Mai kilogiram 700

    A shekarar 2023 kundin adana abubuwan tarihi na Guiness ya karrama Hilda Baci da lambar yabo ta wadda ta fi kowace daɗewa tana girki a duniya.

  2. Shugaban Qatar zai gana da Trump a Amurka

    Nan gaba ake sa ran shugaba Donald Trump, zai karɓi baƙuncin shugaban Qatar Sheikh Tamin bin Hammad Al-Thani a liyafar cin abincin dare, kwana uku da Isra'ila ta kai hari birnin Doha.

    Wakilin Trump na musamman, Steve Witkoff, shi ma zai halarci liyafar.

    Tun da fari Shugaba Trump ya ce harin da aka kai birnin Doha ga ƙusoshin Hamas bai cika burin Amurka da Isra'ila ba.

    To amma duk da hakan ya aike sakataren harkokin waje Marco Rubio zuwa Isra'ila, domin jaddada goyon bayan Amurka ga Isra'ila.

    A ɓangare guda kuma ƙasashen Jamus da Birtaniya fa Faransa sun yi kiran Isra'ila ta gaggauta janyewa daga birnin Gaza.

  3. Nato ta ƙaddamar da shirin ƙarfafa tsaronta

    Ƙungiyar tsaro ta NATO ta ƙaddamar da wani aiki da za ta ƙara tsaron ƙasashe mambobinta da ke gabashin duniya, a wani martani kan kutsen jirage marasa matuƙa da ta yi a sararin samaniyar Poland da safiyar ranar Laraba.

    Shugaban Nato, Mark Rutte ya kira abin da Rasha ta yi da ''rashin hankalin'' da ba za a amince da shi ba.

    Ƙarkashin shirin, Denmark za ta bayar da gudummawar jiragen yaƙi samfurin F-16 da Frigate, sai kuma Faransa ta bayar da jirgi samfurin Rafale, yayin da Jamus za ta ba da jiragen yaƙi huɗu samfurin Eurofighters.

    Sauran ƙasashen ƙawancen NATO su ma za su bayar da tasu gudammawar domin magance barazanar tsaron Rasha.

  4. An rantsar da sabuwar firaministar Nepal bayan zanga-zanga

    An rantsar da tsohuwar mai shari'ar kotun kolin Nepal a matsayin sabuwar firaministan rikon ƙwarya, bayan zanga-zangar ƙin jinin gwamnati ta tilasta wa firaminista KP Sharma Oli sauka daga muƙamin.

    Sushila Karki ta zamo mace ta farko da za ta jagoranci ƙasar.

    Abu na farko da ta fara yi shi ne umartar shugaban ƙasa ya rushe gwamnatinsa, wanda shi ne ɗaya daga cikin buƙatar masu zanga-zangar.

    An kuma sanar da za a gudanar da zaɓen 'yan majalisar wakilai ranar 5 ga watan Maris na 2026.

    Zanga-zanga ta ɓarke a Nepal bayan matakin gwamnati na rufe dukkan kafafen sada zumunta, daga bisani an sake dawo da shafukan amma duk da hakan masu zanga-zangar da suka kira kan su da 'Gen Z' ba su saurara ba.

    Sama mutum 50 ne suka mutu ɗaruruwa suka jikkata a lokacin zanga-zangar.

  5. Gwaji ya tabbatar da matuƙan jirgi biyu na ta'ammali da barasa

    Hukumar binciken tsaron lafiyar ƴannajeriya ta ce wani gwajin miyagun ƙwayoyi da ta yi kan wasu matuƙan jirgi biyu na kamfanin Air Peace ya nuna cewa suna shan ƙwaya da barasa.

    hukumar ta ce ta gudanar da bicniekn ne bayan da jirgin da suke tuƙawa ya kauce hanya a babban filin jirgin saman Fatakwal ranar 13 ga watan Yulin da ya gabata.

    “Sakamakon farko na binciekn da aka gudanar a kansu ya nuna cewa suna ta'ammali da ƙwayoyi masu yawa, ciki har da barasa, haka ma gwaji ya samu wani ma'aikicin jirgin da ta'ammali da tabar wiwi''.

    Hukumar ta ce an sake nazarin wannan sakamakon gwajin, inda aka tabbatar da shi.

    “Kuma gwajin na biyu ya tabbatar da cewa matuƙan jirgin biyu na ta'ammali da barasa,'' in ji rahoton.

  6. Japan ta zama kan gaba a yawan mutanen da suka zarta shekara 100

    Gwamnatin ƙasar Japan ta ce adadin mutanen da suka kai shekara 100 zuwa sama ya kai matsayin da ba a taɓa gani ba a tarihin ƙasar.

    Ma'aikatar lafiyar ƙasar ta ce zuwa Satumban 2025 adadin mutanen da suka kai shekara 100 zuwa sama ƙasar sun kai 99,763, yayin da mata ke kan gaba a adadin.

    Japan ce ta fi kowace ƙasa hasashen tsawon rai a duniya, inda ake yi mata kirari da ƙasar tsofaffi.

    Mazauna ƙasar na samun ingantaccen abinci mai rai da lafiya, sannan mata ba su fiya haihuwa da yawa ba.

    Ministan lafiyar ƙasar, Takamaro Fukoka ya ce mata 87,784 ne suka kai shekara 100 zuwa sama a Japan yayin da yawan maza masu waɗannan shekaru ya kai 11,979.

    Matar da ta fi kowa tsufa a Japan ita ce Shigeko Kagawa, mai shekara 114, da ke zaune a yankin Yamatokoriyama, a birnin Nara.

    Yayin da Kiyotaka Mizuno mai 111 daga birnin Iwata da ke gaɓar ruwa ya zama namiji mafi tsufa a ƙasar.

  7. Matakin Tinubu na shigo da abinci ya taimaka wajen karya farashinsa - Minista

    Ministan noman Najeriya, Sanator Abubakar Kyari ya ce matakan da gwamnatin Tinubu ta ɗauka kan wadatuwar abinci a ƙasar sun taimaka wajen karyar da farashin kayan abinci a faɗin ƙasar.

    Yayin wata hira da gidan talbijin na ARISE TV a ƙasar ranar Juma'a, Sanata Kyari ya ce bayar da damar shigo da abinci da gwamnatin ƙasar ta yi ya taimaka wajen cimma nasarar.

    “Akwai dabaru da yawa da za ka yi amfani da su idan kana son magance matsalar ƙaranci abinci a ƙasar,'' in ji Kyari.

    A shekarar da ta gabata ne shugaba Tinubu ya bayar da damar shigar da abinci cikin ƙasar na ɗan lokaci da nufin magance matsalar ƙarancin abincin da kuma tsadarsa.

    A baya-bayan nan an ga yadda farashin kayan abinci ke karyewa a Najeriya, wani abu da talakawan ƙasar ke farin ciki da shi.

    Sai dai a gefe guda manoma na kukan yadda taki ya yi tsada, duk da karyewar farashin abincin, wani abu da suke fargabar janyo musu asara a harkar noma, idan gwamnati ba ta magance shi ba.

  8. An kama mutumin da ake zargi da kashe ɗan ga-ni kashe-nin Trump

    Hukumomi a Amurka sun tabbatar da kama mutumin da ake zargi da harbe matashin nan mai ra'ayin mazan jiya a ƙasar, Charlie Kirk.

    Gwamnan jihar Utah, Spencer Cox ya ce mutumin ɗan shekara 22, mai suna Tyler Robinson - ya fadi wa wani abokinsa cewa shi ne ya yi laifin, inda shi kuma abokin ya sanar da ƴansanda.

    An harbi Mista Kirk ne a wuya sa'ilin da yake yin bayani ga dandazon mutane a wata jami'a, ranar Laraba, kuma tuni ya mutu.

    Masu bincike na nazari kan shaidun da suka samu, waɗanda suka haɗa da kwanson harsashe da kuma wasu kalaman ƙiyayya.

  9. Amurka ta ce za ta mayar wa Brazil martani kan Bolsanaro

    Amurka ta yi gargaɗin cewa za ta mayar da martani kan hukuncin da kotun kolin Brazil ta yanke wa tsohon shugaban ƙasar Jai Bolsonaro, bayan samun sa da laifin shirya yin juyin mulki bayan ya yi rashin nasara a zaɓen 2022.

    An yanke wa Bolsonaro hukuncin zaman gidan yari na shakara 27.

    Mista Trump ya ce hukuncin da aka yanke wa abokin sa ya bashi mamaki kuma mummunan abu ne ga ƙasar.

    Washington ta bayyana shari'ar a matsayin bita da kullin siyasa.

    Lauyoyin Bolsonaro za su yi ƙoƙarin daukaka ƙara, duk da hakan zai yi wuya, ganin cewa alkali ɗaya ne kawai ya wanke shi daga laifin ba alkalai biyu da ake buƙata ba.

  10. Matatar Dangote za ta fara rarraba mai kai-tsaye bayan rage farashinsa

    Matatar man fetur ta Dangote ta sanar cewa za ta fara rarraba man kai-tsaye zuwa tashoshi a duk faɗin Najeriya daga ranar Litinin, 15 ga Satumba.

    Kazalika, kamfanin ya rage farashin man fetur ga masu gidajen mai zuwa N820 kan lita ɗaya, inda gidajen man jihohin Legas da sauran jihohin yammacin Najeriya za su sayar da shi kan N841.

    Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kamfanin na fitar a shafinsa na X.

    Sai kuma Abuja da Rivers da Delta da Edo da Kwara za su sayar kan N851. Ta ce daga baya shirin zai karaɗe sauran jihohin ƙasar.

    Kamfanin ya ce an yi wannan tsarin ne domin rage farashin rarraba man da kuma sauƙaƙa farashin a tashoshi, da kuma rage matsin tattalin arziki.

    Haka nan, ana sa ran tsarin zai amfani ƙananan masana’antu sama da miliyan 42 ta hanyar rage farashin makamashi da inganta ribarsu, in ji matatar.

  11. Sabuwar taƙaddama ta ɓarke tsakanin Dangote da NUPENG

    Sabuwar takaddama ta sake ɓarkewa tsakanin Dangote da ƙungiyar ƙwadago ta ma'aikatan dakon man fetur da iskar gas a Najeriya, NUPENG bayan kusan sa'o'i 48 da hukmar tsaron farin kaya ta DSS ta shiga tsakani wajen sulhunta su kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

    Shugabannin ƙungiyar sun dakatar da ɗibar mai a tashar matatar Dangote ranar Alhamis, bayan kamfanin ya bayar da umarni ga direbobi su cire dukkan sitikar ƙungiyar da aka liƙa a kan motocinsu a ranar Laraba.

    Daily Trust ta ruwaito cewa DSS ta shiga tsakani ranar Talata, bayan taron sulhu na farko da aka yi ranar Litinin ya ƙare ba tare da cimma matsaya ba kan batun ƙungiyoyi.

    Amma kuma bayan taron sirri da aka gudanar a hedkwatar DSS a Abuja, shugabannin NUPENG sun umarci membobinsu da su janye yajin aikin da suke yi baki ɗaya.

  12. Ukraine ta kai hari da jiragen yaƙi marasa matuƙa 221 kan Rasha

    Ukraine ta kaddamar da hari da jiragen yaki marasa matuki 221 kan Rasha, inda aka ce an harbo fiye da rabinsu a yankin Bryansk da Smolensk, inda ake zargin harin ya nufi wuraren kamfanin man Lukoil ne.

    A yankin Leningrad, an harbo jirage 28 kuma gobara ta tashi a tashar man fetur ta Primorsk amma an kashe ta ba tare da rasa rai ko zubewar mai ba.

    A Ukraine kuma, mutum biyu sun mutu a Sumy bayan bam ɗin Rasha ya bugi wani ƙauye a kusa da iyaka.

    Hare-haren sun shafi aƙalla yankuna tara na Rasha, ciki har da Moscow, inda aka harbo jirage tara.

    A Bryansk kuma, mutum bakwai sun jikkata bayan jirgi marar matuki ya bugi wata bas.

    Rahotanni sun nuna cewa wannan na ɗaya daga cikin manyan hare-haren sama da Ukraine ta kai cikin watanni hudu, lamarin da ya tilasta a dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a filin jirgin Pulkovo na St Petersburg.

    Hare-haren kan iyaka sun zama ruwan dare, inda a watan Yuli aka rufe dukkan filayen jirgin saman Moscow saboda kai hari.

  13. Likitoci sun fara yajin aiki a faɗin Najeriya

    Ƙungiyar likitoci masu neman ƙwararewa ta sanar da fara yajin aikin gargadi na kwana biyar daga yau, bisa ga matsayar da aka cimma a majalisar zartarwar ƙungiyar.

    Ƙungiyar ta bukaci dukkan mambobinta a cibiyoyi daban-daban su bi wannan umarni ba tare da kaucewa ba.

    A cewar kungiyar, matakin yajin aikin ya zama dole ne domin matsa lamba ga gwamnati kan buƙatunsu na inganta walwala da kyautata yanayin aiki, tare da tabbatar da ingantacciyar tsarin kiwon lafiya ga ‘yan Najeriya.

    Sun ce makasudin yajin ba wai cutar da al’umma ba ne, sai dai domin tabbatar da nagartar harkar lafiya a kasa.

    Ƙungiyar ta jaddada muhimmancin hadin kai tsakanin mambobinta a wannan lokaci, inda ta ce nasarar wannan mataki zai dogara ne akan yadda kowa zai tsaya tsayin daka wajen aiwatar da yajin aikin.

    Kungiyar ta ce za ta ci gaba da lura da yadda lamarin zai kaya a wannan mako, sannan a ƙarshe za ta tantance matakan gaba dangane da yadda gwamnati za ta amsa buƙatunsu.

    Ta kara da cewa ba za ta yi Ƙasa a gwiwa ba wajen kare muradun likitoci da kuma tabbatar da kyakkyawan tsarin kiwon lafiya ga al’ummar Najeriya.

  14. FBI za ta bayar da tukwicin dala 100,000 kan kisan Charlie Kirk

    Hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka (FBI) ta bayyana cewa za ta biya dala 100,00 kimanin naira miliyan 150 kenan ga wanda ya taimaka wajen bayar da sahihan bayanai da zai kai ga gano da kuma cafke wanda ya kashe Charlie Kirk a ranar 10 ga Satumba, 2025, a Jami’ar Utah Valley dake garin Orem, jihar Utah.

    Kisan matashin, wanda babban magoyin bayan Shugaba Donald Trump ne ya girgiza al’ummar Utah da ma Amurka baki ɗaya tare da janyo kalamai na alhini da suka.

    Har yanzu ba a bayyana wanda ya aikata wannan kisan kai ba, amma jami’an hukumar sun bayyana hoton mutumin da ake zargi da kisan.

  15. Kotu ta gayyaci Mark da wasu kan rikicin jagorancin ADC

    Babbar kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci shugabannin rikon kwarya na jam’iyyar haɗaka ta ADC ƙarƙashin Sanata David Mark da su bayyana a gaban kotu ranar 15 ga Satumba.

    Kotun na son su bayyana dalilin da zai sa ba za a hana INEC amincewa da shugabancinsu ba.

    Wannan umarni ya biyo bayan ƙarar da tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar, Nafiu Gombe, ya shigar yana iƙirarin shi ne shugaban jam’iyyar na gaskiya.

    Alƙali Emeka Nwite ne ya bayar da wannan umarni ranar 4 ga Satumba

    Ya nemi kotu ta hana INEC amincewa da David Mark a matsayin shugaban jam’iyyar da kuma Rauf Aregbesola a matsayin sakatare har sai an yanke hukunci.

    Waɗanda ake ƙara sun haɗa da jam'iyyar ADC da David Mark da Rauf Aregbesola da INEC da tsohon shugaban ADC Ralph Nwosu.

    Alƙali Emeka Nwite ya ce a sanar da su sannan su bayyana a kotu domin kare kansu.

  16. Jonathan ya gana da Obi gabanin zaɓen 2027

    Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour (LP) a zaɓen 2023, Peter Obi, sun gana a jiya a birnin Abuja yayin da tattaunawa ke ƙaruwa kan yiwuwar haɗin gwiwar jam’iyyun adawa domin fuskantar zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

    Waɗannan manyan ’yan siyasa daga Kudancin Najeriya sun kasance a kan gaba cikin tattaunawa a kwanakin baya inda ake kallonsu a matsayin masu ƙalubalantar shugaba Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC.

    Duk da cewa har yanzu Obi yana cikin jam’iyyar Labour, yana ta haɗuwa da jiga-jigan jam'iyyar haɗaka ta ADC.

    Jonathan, wanda har yanzu memba ne na jam’iyyar PDP bai sake taka muhimmiyar rawa a cikin jam’iyyar ba tun bayan da ya sha kaye a zaɓen 2015.

    Babu cikakken bayani da aka fitar dangane da ganawar da suka yi ranar Alhamis, amma Obi ya wallafa hotuna a shafin X, inda ya bayyana cewa sun tattauna kan halin da ƙasar ke ciki.

    Obi ya rubuta cewa; “A yau a Abuja, na gana da babban ɗan uwa na, ɗan siyasa, kuma jagora, tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan @GEJonathan. Mun yi wata muhimmiyar ganawa inda muka tattauna kan halin da ƙasarmu ke ciki.”

  17. Kotu ta yanke wa tsohon shugaban ƙasar Brazil hukuncin ɗaurin shekara 27

    Kotun kolin Brazil ta yankewa tsohon shugaban ƙasar Jair Bolsonaro hukuncin daurin sama da shekaru ashirin da bakwai a gidan yari, bayan samunsa da laifin yunkurin juyin mulki bayan shan kaye da ya yi a zaɓen 2022.

    An yanke masa hukuncin ne tare da wasu mutum bakwai da aka tuhume su tare, ciki har da tsofaffin ministoci da hafsoshin soja.

    Tsohon shugaban mai ra'ayin mazan jiya wanda ake tsare da shi a gida ya musanta zargin da ake masa.

    Akwai yiwuwar ya ɗaukaka ƙara, ko kuma ya nemi a mayar da daurin na talala saboda shekarunsa, da kuma yanayin lafiyarsa.

    Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya ce Washington za ta mayar da martani kan abun da ya bayyana a matsayin bita da kullin siyasa. Ma'aikatar harkokin wajen Brazil ta bayyana barazanar a matsayin ihu bayan harin.

  18. 'Shugabannin Isra'ila masu tsattsauran ra'ayi su ne ke neman tayar da rikici a duniya'

    Qatar ta yi lale marhabun da matakin kwamitin sulhu na Majalisar na yin Allah wadai da harin da Isra'ila ta kai wa shugabannin Hamas a birnin Doha.

    Firaiministan Qatar, Mohammed bin Abdulrahman Al-Thani, ya halarci taron gaggawan a New York.

    Ya bayyana shugabannin Isra'ila a matsayin masu tsattsauran ra'ayi da ke kishirwar jefa duniya cikin rikici.

    To amma ya ce hakan ba zai hana su ci gaba da jagorantar yunkurin cimma yarjejeniya don wanzar da zaman lafiya a Gaza ba.

    Nan gaba a yau Juma'a ne dai firaministan zai je Washington domin tattaunawa a fadar White House, inda shima shugaba Trump ya nuna fushinsa da kai harin.

    An gudanar da jana'izar wadanda aka kashe a jiya Alhamis, amma Hamas ta ce shugabanninta sun tsira.

  19. Assalamu Alaikum

    Barkanmu da sake saduwa a shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa a hantsin Juma'a

    Shafin na yau zai fi mayar da hankali ne kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwabtanta, da kuma sauran sassa na duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo.

    Ku kasance da mu.