Ƴan Najeriya na ganin amfanin basukan da Tinubu ke ciyowa - APC

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta kare batun yawan karbe-karben basukan da gwamnatinta ke yi tun hawan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda ta tsaya kai da fata cewa karbar basukan wata dabara ce ta samar da kudaden gudanar da wasu muhimman ayyukan, ba wai wani ganganci ba ne kamar yadda wasu 'yan kasar ke ta korafi.

Masu korafin sun hada da masu sharhi kan al'amuran yau da kullum da masana tattalin arziki da kuma wasu jam'iyyun hamayya irin su Labour.

Masu sukar ciyo bashin musamman na waje na nuni da hadurran da suka ce na tattare da shi ga makoma da kuma al'ummar kasar.

Jam'iyyar Labour ta kwatanta yawan ciyo bashin da gwamnatin Tinubun ke yi daga waje da cewa abin takaici ne, kamar yadda sakatarenta Umar Ibrahim Faruk ya bayyana wa BBC:

''Mu a matsayinmu na jam'iyyar Labour Party mun kalli abin da takaici saboda haka muna nuna ma gwamnatin nan cewan abin da take yi bai daidai ba ne, ta duba da kyau kuma a dakatar da maganr karbar bashin nan haka,'' in ji shi.

Sakataren ya kara da cewa ya kamata, gwamnati ta tabbatar da toshe duk wasu kafofi na satar wadannan kudade.

Bugu da kari gwamnatin ta duba irin kudaden da take kashewa a kan wasu abubuwa da ba su wajaba ba, kamar tafiye-tafiye da kayan alatu ya ce ya kamata a rage ko ma a daina idan ba wadanda suka zama na dole ba ne.

Jami'in na jam'iyyar hamayya ta Labour ya ce, abin da ya kamata gwamnati ta yi bayan tsuke bakin aljihunta shi ne ta mayar da hankali wajen amfani da kudaden wajen inganta rayuwar talakawa ta fannin kula da lafiya da makarantu da tsaro da sauran muhimman bangarori da al'umma za su amfana: ''Amma ba a je a dauki kudi a rika shagali da su ba,'' ya ce.

Sai dai a martanin jam'iyyar APC mai mulkin Najeriyar ta ce lamarin ba yadda 'yan hammayya da sauran masu suka kan bashin suke gani yake ba, kamar yadda darektanta na yada labarai, Bala Ibrahim ya sheda wa BBC.

Ya ce, '' wannan shugaban kadsa Bola Ahmed Tinubu shi ne shugaba na farko dansiyasa, dankasuwa wanda ya san darajar kudi ya san darajar riba, ya san faduwa, ya kuma san yadda za a sarrafa kudi idan aka ciyo ba shi.''

'' A ba ka bashi ma nuni ne da cewa an yarda da karfin tattalin arzikinka. Don haka wannan ce-ce-ku-ce da ake game da basukan da Najeriya ke ci ba wani abu ba ne illa rashin fahimtar abubuwa,'' in ji darektan.

Dangane da korafin da masu sukar ke yi cewa ba su ga abin da ake yi da kudin da ake ciyo ba shin ba, sai Bala Ibrahim ya ce : ''Cin bashi ba wai lalle ka ciyo ba shi ka ginarijiya ko ka ciyo bashi ka gina gada ko asibiti ba, 'a'a ana iya cin bashi domin a kara karfafa karfin cinikayya tsakanin kasa da kasa.''

Ya kara da cewa: ''Yanzu idan ka dubi ingancin wutar lantarkin da ake samu a Najeriya ba a dai kai gabar da ake so ba amma lalle al'amura sun inganta ta yadda ana samun wutar fiye da yadda a baya ake samu. Wannan na daya daga cikin irin abubuwan da ake yi da irin wadannan kudade da aka ciyo bashi.

Yayin da ire-iren wadannan bayanai ke fitowa daga bangaren jam'iyyar APC da gwamnatinta, 'yan Najeriya na nan cike da fatan kwalliyar karbo basukan ta biya kudin sabulu.