Wakilan Hamas na buƙatar tabbaci daga Trump kan kawo ƙarhen yaƙin Gaza

Asalin hoton, EPA
Yayin da aka shiga kwana na biyu a tattaunawar da ba ta keke da keke ba tsakanin wakilan Isra'ila da Hamas, babban wakilin kungiyar Khalil al-Hayya ya ce Hamas na bukatar tabbaci daga shugaba Trump kan duk wata tattauna ko yarjejeniyar da za a cimma za ta tabbatar da an kawo karshen yakin da ake yi Gaza baki daya.
Sai dai wakiliyar BBC ta ce Isra'ila na son maida hankali ne kan matakin farko na yarjejeniyar wato sako wadanda akai garkuwa da su, da bayanin inda za a sake su da wadanda za su jagoranci hakan.
Yayin da wakilan bangarorin biyu ke can Masar tattauna kawo karshen yakin, can a zirin Gaza tankokin yaki da makaman rokar Isra'ila na ci gaba da barin wuta kan Falasdinawa.























