Me zai faru idan mutane suka mallaki bindigogi domin kare kansu?

Wani mutum riƙe da makamai

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Jama'a da masu sharhi na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu dangane da kiran da wasu al'ummomin jihar Sokoto suka yi na a ba su damar mallakar bindigogi domin kare kansu daga hare-haren ƴanbindiga.

Jihar Sokoto da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya na daga cikin jihohin ƙasar da ke fama da matsalar tsaro, inda ƴanbindiga ke cin karensu babu babbaka.

A baya-bayan nan ne dai wasu al'umomi a yankin ƙaramar hukumar Kebbe a jihar suka buƙaci gwamanti ta ba su ikon mallakar makamai domin kare kansu.

Jama'ar yankin sun ce sun gaji da yadda ƴanbindigar ke ci gaba da kai masu hari, da kashe masu mutane da kuma garkuwa da wasu, lamarin da ya janyo masu mummunar asara.

Sun ce daga cikin garuruwa 17 da ƙaramar hukumar Kebbe ke da su, a yanzu ƴanbindiga sun kori mutane daga garuruwa aƙalla 11, saboda yawaitar hare-hare.

Sai dai masana tsaro sun yi gargaɗi game da illar fararen hula su mallaki makami domin kare kai, ko da yake sun ce tura ce ta kai mutanen bango.

Me kiran ke nufi?

Masana tsaro na kallon wannan kira a matsayin gazawa ga hukumomin tsaron Najeriya

Dokta Audu Bulama Bukarti, ƙwararren lauya a Birtaniya kuma mai bincike kan harkokin tsaro a ƙasashen Afirka ya ce kira na nun irin halin damuwa da firgici da ma yanke kauna da al'umomin yankin suka yi.

''A baya idan aka kai irin wannan hari, mutane kan fito su yi kira ga gwamnati da jami'an tsaro cewa suna neman ɗauki, amma da alama yanzu sun fara yanke ƙauna da kiran kare su'', in ji Bukarti.

Shi ma Dokta Kabiru Adamu shugaban kamfanin Beacon Security mai nazarin tsaro a yankin Sahel ya ce hakan na nuna cewa mutane sun fara gajiya da halin da suke ciki.

''Mutane na ganin an kai fagen da dole sai sun fito sun bayyana wa duniya halin da suke ciki'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa hakan ya kara fito da taɓarɓarewar tsaro a yankin.

Ikon bayar da lasisin mallakar makamai a Najeriya

wasu bindigogi na zamani  masu yawa a kan teburi

Asalin hoton, Getty Images

Dokta Bukarti ya ce a tsarin dokokin Najeriya an raba makamai zuwa gida biyu dangane da damar mallakarsu.

''Akwai manyan makamai da ake kira ''Military grade weapons'' da jami'an tsaron ƙasar ne kawai za su iya riƙewa'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa irie-iren waɗannan makamai sun haɗa da nau'in AK, da G3 da mashinga da makaman atilare.

''Ire-iren waɗannan makamai babu mai bayar da lasisin ikon riƙe su sai shugaban ƙasa, kuma a tarihin Najeriya babu shugaban ƙasar da ya taɓa bayar da lasisin riƙe su'', in ji shi.

Sannan kuma Dokta Bukarki akwai ƙananan makamai da doka ta amince wa babban sufeton ƴansandan ƙasar ya bayar da lasisin mallakarsu, wanda shi kuma a wasu lokuta yakan bai wa kwamishinonin ƴansanda damar bayar da lasisin mallakar a madadinsa..

''Ire-iren waɗannan makamai sun haɗa da bindigar harba ruga, bindigar farauta, da ƙaramar bindigar ƙirar gida ta hannu'', in ji shi.

Mallakar bindiga za ta taimaka wa tsaro?

wasu bindigogi

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Dokta Bukarti ya ce bai wa mutane damar mallakar makami ba zai zama mafita, kasancewar bindigogin da doka ta amince fararen hula su riƙe ba za su taɓa kare su daga hare-haren yanbindigar da ke rike da manyan makamai ba.

''Su dama ƙananan makamai doka ta bayar da damar a ba su ikon mallaka, su kuma waɗanda suke kai musu hari manyan makamai suke riƙe da su, don haka wannan ba mafita ba ne'', in ji gogaggen lauyan.

Haka shi ma Dokta Kabiru Adamu ya ce mallakar makami ba ya taimaka wa yaƙi da matsalar tsaro.

Masanin tsaron ya ce hasalima ƙara ta'azzara matsalar tsaron yake yi.

''Yanzu idan da duba ƙasar Amurka mai dokokin da suka tanadi mallakar makami, idan ka duba laifulan da ake samu sakamakon mallakar makami, babu ƙasar da ake samun hakan a duniya'', in ji masanin tsaron.

Ya ci gaba da cewa babu wata shaida da bincike ya tabbatar da cewa bai wa yanƙasa makamai na taimaka wa yaƙi da matsalar tsaron kowace ƙasa.

Barista Bukarti ya ce ''idan ka duba yawan mutanen da suke mutuwa sakamakon laifukan da suka shafi mallakar bindiga a Amurka, sun zarta adadin mutanen da suke mutuwa sanadiyyar ta'addanci a Najeriya'', in ji shi.

Illolin bai wa fararen hula damar mallakar makamai

wani mutum riƙe da bindiga

Asalin hoton, Getty Images

Masana tsaron sun yi gargaɗin cewa barin ƴanƙasa su mallaki makamai na da illoli masu yawa da za su cutar da zaman lafiyar ƙasar.

Bukarti ya ce bai wa mutane damar mallakar makamai ya ma fi illa fiye da wadda ake ciki yanzu ta hare-haren ƴanbindiga.

  • Ƙaruwar aikata miyagun laifuka

Kabiru Adamu ya ce barin yankasa su mallaki makamai zai ƙara haifar da wasu miyagun laifukan.

''Duk lokacin da ake ce kowa zai iya mallakar makami to fa maganar tsaro sai dai Allah ya kiyaye, amma babu batun ƙarewar matsalar'', in ji shi.

Shi ma Bukarti ya ce riƙe makaman zai sa a riƙa aikata wasu laifukan ma da a baya ba a aikata su.

''A Amurka fa idan mutum ya samu saɓani da budurwarsa sai kawai ya ɗauko bindiga ya je wurin da mutane ke taruwa ya buɗe musu wuta'', in ji shi.

  • Gasar mallakar makami

Dokta Kabiru adamu ya ce wta matsalar da hakan zai haifar ita ce gasar mallakar makamai tsakanin mutane.

''Kowa zai yi ƙoƙarin mallakar maƙamin da ya fi na wani, kuma a wannan yanayin da ake ciki akwai manyan makamai da dama, da mallakar su zai zama wata barazana, saboda hakan ba alheri ba ne'', in ji shi.

Dokta Bukarti ya ce idan kowa ya mallaki bindiga, to fa tsakanin maƙwabci da maƙabci ma idan rigima ta kaure to za a yi ɗauko bindiga.

  • Ƙaruwar rikicin ƙabilanci

Kabiru Adamu ya ce bai wa fararen hula mallakar makami zai ƙara haifar da matsalar matsalar rikicin ƙabilanci a ƙasar.

''A yanzu idan ka duba akwai wata ƙabila ɗaya da ake yawan zargi da tashe-tashen hankulan yankin arewa maso yamma, to idan ka bai wa mutane damar mallakar makami za su riƙa kai wa wannan ƙabila hare-hare, sannan ita ma ƙabilar mutanenta ba zama za su yi ba, za su ta shi su mallaka domin kare kansu'', in ji shi.

  • Rigima da jami'an tsaro

Dokta Bukarti ya ce idan mutane suka mallaki bindigogi a yau, to za su koma faɗa ne da jami'an tsaro.

''Domin jami'an tsaron ne za su riƙa zuwa suna kamo su da cewa su ne masu aikata laifukan,'' in ji shi.

Wane mataki ya kamata gwamnati ta ɗauka?

Yana da kyau gwamnati ta ƙara ƙarfafa ayyukanta wajen kare ƴankasa daga hare-haren masu riƙe da makamai, a cewar Dokta Kabiru Adamu.

Ya ƙara da cewa idan gwamnati ta yi abin da ya kamata wajen sauke nauyin da ke kanta to hakan zai mutane da daina tunanin mallakar makami domin kare kansu.

Dokta Bukarti kuwa cewa ya yi yana da kyau gwamnatin tarayya ta bai wa gwamnoni ko sarakuna damar ɗaukar mutanen da za su riƙa bai wa garuruwansu kariya.

''A yi wani tsari ta yadda za a ɗauki bayanan duk wanda aka bai wa bindiga da irin bindiga da alburushin da aka ba shi ta yadda lokaci zuwa lokaci za a riƙa bibiya'', in ji shi.