Rufewa
Masu bibiyar mu a nan muke sallama da ku, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu ci gaba da kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rabiatu Kabir Runka ke maku fatan alheri.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 20/12/2024
Haruna Kakangi, Badamasi Mukhtar da Isiyaku Muhammed, Rabiatu Runka
Masu bibiyar mu a nan muke sallama da ku, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu ci gaba da kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rabiatu Kabir Runka ke maku fatan alheri.
Wani bincike da BBC ta gudanar, ya gano gwamnatin sojin Myanmar na iko ne da kashi daya cikin 3 na daukacin kasar, shekaru 4 da hambarar da mulkin shugaba Aung San Suu Kyi.
Kungiyoyin 'yan tawaye da yawanci ba sa ga maciji da juna saboda banbancin kabila na rike da sama da kashi 40 cikin 100 na Myanmar.
BBC ta karkare wannan kididdiga ne bayan samun sahihan bayanai daga kungiyoyin kauyukan kasar.
Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya ta musamman kan Myanmar ta ce har yanzu gwamnatin sojin na rike da ikon wasu daga cikin biranen kasar, sai dai ana zaune cikin hatsari.
BBC ta kuma gano yawancin sojin kasar na yi wa 'yan tawayen da ke goyon bayan mulkin dimukradiyya aiki amma a boye.

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Malaysia ta bada izinin sake fara bincike kan jirgin kasar MH370 a daya daga cikin danbarwar batan jirgi mai cike da ban mamaki a duniya.
Hukumomin Malaysia sun gayyato wani kamfani mai zaman kan shi na OCEN INFINITY domin gudanar da sabon binciken, tashin farko za su fara ne da neman jirgin.
Jirgin dai na dauke da fasinjoji 239, da ya taso daga birnin Kula Lumpur zuwa Beijing shekaru 10 da suka gabata. An yi amanna jirgin ya yi hatsari a cikin tekun India dubban kilomita daga inda ya taso.
Sai dai har yanzu ba a gano tarkacen jirgin ba, a shekarar 2017 akai watsi da binciken sanin ainahin abin da ya faru da jirgin.

Asalin hoton, AFP
Jami'an diflmoasiyyar Amurka sun yi ganawar farko da sabbin shugabannin riƙo na gwamnatin ƴan tawayen a birnin Damascus.
Mataimakiyar sakataren harkokin cikin gida na Amurka Barbara Leaf , ta gana da mambobin Hayat Tahrir Al-Sham da suka hambarar da mulkin shugaba Bashar al-Assad makonni biyu da suka gabata, sun tattauna kan batun tallafin da Amurka za ta yi wa Syria.
Wakilin BBC a birnin Damascus ya ce mambobin HTS na son Amurka da kawayenta su cire su daga jerin 'yan ta'adda, hakan zai share wata hanya da samun damar janyewa kjasar takunkuman da aka kakaba musu.
Wakilin na mu ya kara da cewa ganawar alama ce da ke nuna da gaske Amurka ta ke na aiki kafada da kafada da HTS domin sake gida sabuwar Syria.

Asalin hoton, Reuters
Kotu ta ɗaure yayan tsohon ɗanwasan Manchester Tunited, Paul Pogba, shekara uku a gidan yari bayan samun sa da laifin yunƙurin yi wa ɗan'uwan nasa ƙwace.
Mathias Pogba wanda kotun ta kuma ci shi tarar yuro 20,000 (£16,500), zai yi zaman gidan yarin na shekara ɗaya ne kawai amma zai saka maɗauri a ƙasa mai aiki da lantarki.
Kotun ta kuma samu wasu mutum biyar da laifin ƙwace da sauran laifuka, inda ta yanke musu hukuncin shekara huɗu zuwa takwas a ranar Alhamis.
Paul Pogba mai shekara 31 ya ce "abokansa sun yaudare shi" ta hanyar tsira shi da bindiga a 2022 kuma suka nemi ya ba su yuro miliyan 13. Ya ce ya ba su yuro 100,000

Asalin hoton, Getty Images
Ma'aikatar tsaron Chadi ta ce ƙasar Faransa ta soma janye dakarunta daga ƙasar a yau Juma'a, bayan kawo ƙarshen yarjejeniyar soji tsakanin ƙasashen biyu.
Sojoji 120 ne suka tashi daga babban birnin ƙasar, N'Djamena zuwa Faransa.
Ma'aikatar tsaron Chadin ta bayyana hakan ne a shafinta na Facebook.
Kasar Chadi dai ta kasance wata babbar hanyar da Faransa ke amfani da ita wajen ci gaba da kasancewarta a nahiyar Afirka, musamman a yankin sahel, tun bayan janyewar dakarunta daga Mali da Burkina Faso da kuma Jamhuriyar Nijar.
A ranar 28 ga watan Nuwamba ne ƙasar ta sanar da kawo ƙarshen yarjejeniyar tsaro ta 1960.
Faransa da ke da dakaru 1,000 a Chadi, ba ta ce komai ba kan lamarin.
A shekarun baya-bayan nan shugabannnin mulkin sojin Mali, da Nijar da Burkina Faso na nuna alamun ƙulla sabon ƙawance da Rasha.
An gurfanar da Wanda ake zargi da harbe shugaban wani kamfanin inshorar lafiya a Amurka a gaban kotu a birnin New York,
Luigi Mangione, ya isa Manhattan ne a jirgi mai saukar ungulu, inda 'yan sanda dauke da makamai suka rako shi Bayan tuhume-tuhumen da jihohin New York da Pennsylvania suka gabatar, yanzu yana fuskantar tuhumar gwamnatin tarayya na kisan kai.
Zai ci gaba da zama a gidan yari har zuwa lokacin da zai sake bayyana a gaban kotu a watan Janairu An dai harbe Brian Thompson ne a wajen wani otal a birnin New York a farkon wannan watan.

Asalin hoton, Getty Images
Ma'aikatar lafiya ta Rwanda ta ayyana kawo karshen cutar Marburg da ta yi mummunar barna a kasar.
An samu sama da mutum 60 da suka kamu da cutar, wadda ta barke a watan Satumba, wasu 15 kuma suka mutu.
Hukumomi a Rwanda sun ce sun dauki matakan da ya dace domin kakkabe cutar a asibitoci tare da yi wa marar lafiya gwaji da zarar sun fara nuna alamun cutar.
Cutar Marburg na farawa da zazzabi mai zafin gaske, da kasala a wasu lokutan kuma mutane kan fara zubda jini da tsayawar aikin wasu daga cikin sassan jiki.

Asalin hoton, Getty Images
Sama da mutum 40 ne a sassan yammaci da tsakiyar Afirka suke fama da yunwa a daidai lokacin da aka fara kakar abinci.
A wata sanarwa da shirin samar da abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya ya fitar a ranar Juma'a, ya ce za a samu ƙaruwar mutanen zuwa miliyan 52.7 zuwa tsakiyar shekarar 2025, ciki har da mutum miliyan 3.4 da za su faɗa cikin matuƙar yunwa.
Adadin waɗanda suke fama da matuƙar yunwa wato mataki na huɗu ya ƙaru da kashi 70, kamar yadda sanarwar ta nuna.
Ƙasashen da aka fi fama da yunwar sun haɗa da Najeriya da Kamaru da Chad, waɗanda su kaɗai ne suka da sama da rabin adadin.
Lamarin ya nuna buƙatar da ke akwai na aikin gaggawa domin samar da abinci domin magance matsalar a yankin Sahel.

Asalin hoton, Namadi/Facebook
An ƙaddamar da aikin samar da ruwa na Greater Dutse Water Supply a birnin Dutse na jihar Jigawa, wanda ya kusa shekara 20 ana hanƙoro domin samar da ruwan sha ga mutanen yankin.
Gwamnan jihar, Umar Namadi ne tare da ministan albarkatun ruwa da tsabtace muhalli, Farfesa Joseph Terlumun Utsev suka jagoranci ƙaddamar da aikin a garin Sintilmawa da ke ƙaramar hukumar Ringim.
An kasafta kashe naira biliyan 59.9 na aikin, wanda za a yi haɗaka tsakanin gwanmatin tarayya da jiha domin ɗaukar nauyi.
Da yake jawabi a waje ƙaddamar da shirin, gwamna Namadi ya yi godiya ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu bisa cika alƙawarin da ya ɗauka na fara aikin.
A nasa ɓangaren, Farfesa Joseph Terlumun Utsev, yabawa ya yi game da fara aikin, inda ya ce idan aka kammala, za a samu ragowar kamuwa da cututtuka.

Asalin hoton, DOGARA TWITTER
Tsohon shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara, ya ce koma-baya da ake samu a yankin Arewa laifi ne na jagororin siyasar yankin.
Ya kuma yi kira ga ƴan Najeriya da su goya wa Tinubu baya kan yunƙurinsa na inganta tattalin arzikin ƙasar ta hanyar ƙudurorin haraji.
Dogara ya bayyana hakan ne a wani taron jagororin kiristoci ƴan arewacin Najeriya, inda ya ce jagororin yankin ba su yi amfani da damar da suka ba na kusan shekara 40, wanda hakan a cewarsa ya jefa yankin talauci da rashin aikin yi.
"Ba Tinubu ko yankin kudu ba ne matsalarmu. Wasu na ƙorafin cewa Yarbawa suna samun muƙamai da yawa, amma kar mu manta, mun yi mulkin sama da shekara 40. Me za mu nuna? har yanzu arewa na nan yadda take," in ji shi, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Asalin hoton, NG Police
Kakakin rundunar ƴansandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi, ya ce zagin mutane a kafofin sadarwa laifi a ƙarƙashin dokokin Najeriya, wanda kuma duk wanda ya aikata zai iya fuskantar hukunci.
Adejobi ne ya wallafa shakan a shafinsa na X, inda ya ce: "zagin mutane a kafofin sadarwa ba furta albarkacin baki ba ne.
"Cin zarafi ta kafafen sadarwa na, wadda kuma daban yake da ɓata suna. Kuma laifi ne babba, wanda mai aikatawa zai iya fuskantar hukunci. A bi a hankali."
Asusun ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, wato UNICEF, ya ce Najeriya na ɗaya daga cikin ƙasashen duniya waɗanda yaran da ke ƙasar ba sa zuwa makaranta.
Al'amarin da galibi yawan rikice-rikice da rashin tsaro suka haifar a sassa da dama na ƙasar.
A sakamakon haka, wata mata ta sami karsashin kafa gidauniyar ilimi a wani ƙauye na jihar Filato, bayan da iyalai da dama suka kasa biyan kudaden makarantar yaransu.
Da gidauniyar ce take wayar da kai tare da taimakon yara suna zuwa makaranta.

Asalin hoton, Dada Olusegun/X
Shugaban ƙasa Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima za su kashe naira biliyan 9.36 a tafiye-tafiyen cikin gida da na ƙasashen waje da maƙulashe a baɗi.
Kamar yadda yake ƙunshe a cikin kasafin kuɗin wanda Tinubu ya gabatar a gaban majalisa, shugaban zai kashe naira biliyan 7.44 a tafiye-tafiye da sauran maƙulashe, shi kuma Shettima zai kashe naira biliyan 1.9.
Tafiye-tafiyen shugaban ƙasa zuwa ƙasashen waje za su laƙume naira biliyan 6.14, sannan tafiye-tafiyensa na cikin gida za su laƙume naira miliyan 873.9.
Shi kuma mataimakin shugaban ƙasa zai kashe naira biliyan 1.31 a tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje, da kuma naira miliyan 417.5 a tafiye-tafiyen cikin gida.
A shekarar 2024, Tinubu da Shettima da uwargidan shugaban ƙasa sun kashe kusan naira biliyan 5.24 a tafiye-tafiya a tsakanin Janairu zuwa Maris, kamar yadda Daily Trust ta kalato daga wani rahoton tafiye-tafiye ta manhajar GovSpend, wadda ke ƙididdige kashe kuɗaɗen gwamnati.

Asalin hoton, AFP
Jami'an diflomasiyyar Amurka suna birnin Damascus inda suke shirin ganawa da wakilan ƙungiyar Hayat Tahrir al-Sham, wadda ke riƙe da madafun iko a ƙasar.
Sai dai har yanzu Washington na cigaba da kallon ƙungiyar a matsayin ta ƴan ta'adda.
Ziyarar ta biyo bayan tawagar Majalisar Ɗinkin Duniya da na wasu ƙasashe ciki har da Birtaniya da Faransa, da kuma Jamus da suka ziyarci ƙasar cikin kwanakin nan.

Asalin hoton, BBC Yoruba
A ranar Alhamis ne aka wayi gari da labarin turmutsutsu a jihar Oyo, wanda ƴansanda suka tabbatar da mutuwar yara 35, sannan wasu suka jikkata.
An shirya taron ne - kamar yadda aka saba yi duk shekara - domin nishaɗin yara, sannan a raba musu kyaututtuka da kuɗaɗe da abinci, kamar yadda iyayen wasu daga cikin yaran suka bayyana.
Sai dai a bana, wannan shi ne karo na huɗu da aka samu irin hakan, inda turmutsutsun mutane a taruka suka jawo asarar rayuka.
A watan Maris, wasu mata ɗalibai biyu sun rasu a jihar Nasarawa da ke maƙwabtaka da babban birnin tarayya Abuja a wurin raba shinfaka da gwamnatin jihar ta shirya. Bayan mutuwar, aƙalla mutum 23 kuma sun jikkata.
Bayan kwana uku kuma, a jihar Bauchi da ke arewa maso gabas, aƙalla mutum bakwai suka rasu lokacin da wani ɗankasuwa yake raba kuɗi.
Tun kafin wannan kuma, a watan Fabrairu, mutum biyar sun rasu a Legas lokacin da hukumar kwastam ta yi gwanjon shinkafar da ta ƙwace a farashi mai rahusa.
Zuwa taruka irin waɗannan ba sa rasa nasaba da yanayin tsadar rayuwa da ake fama da ita a Najeriya, inda iyalai suke zuwa domin samun sauƙi.

Asalin hoton, Tinubu X
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya ya ba da umarnin a gaggauta gudanar da bincike domin musabbabin turmutsutsun da ya auku a jihar Oyo, wanda ya yi sanadiyar mutuwar yara da 35 da jikkata wasu a wurin taron al'ada na ya yara.
Tinubu ya bayyana wannan buƙatar ce a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya fitar.
Shugaba Tinubu ya bayyana matuƙar kaɗuwarsa, sannan ya miƙa ta'aziyyarsa ga gwamanti da iyalan waɗanda abin ya shafa, da al'ummar jihar baki ɗaya.
"Kula da yaranmu nauyi ne da bai kamata a yi wasa da shi ba," in ji shi, sannan ya ƙara da kira ga masu shirya taruka da su riƙa kula hanyoyin gudanar da tarukansu cikin tsanaki.
A ranar Alhamis, ƴansanda sun ce sun kama mutum bakwai da suka da alaƙa da shirya taron da ya janyo turmutsutsun, ciki har da wadda ta shirya taron, tsohuwar matar Ooni na Ife Naomi Silekunola.
Wasu iyayen da suka zanta da ƴanjarida sun ce sun raka yaransu taron ne domin an yi alƙawarin za a raba kuɗi naira 5,000 ga duk wanda ya je, sannan za a raba abinci kyauta.

Asalin hoton, Godswill Akpabio
Majalisar Dattijan Nijeriya ta umarci Babban Bankin Ƙasar ya sake nazari kan manufofinsa na kuɗi saboda waɗanda ya yi amfani da su a shekara mai bankwana, ba su yi tasiri ba.
Kwamitin kula da bankuna da cibiyoyin kuɗi da na inshora na Majalisar ya kuma nemi jin bahasi a kan matsalar ƙarancin takardun kuɗi da ake fama da ita yanzu, da kuma ƙaruwar tsofaffin kuɗi a hannun mutane.
Matakin na zuwa ne bayan gayyatar da kwamitin ya yi wa Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Olayemi Cardoso don yi musu ƙarin bayani kan nasarorin da bankin ya samu game da manufofinsa na kuɗi a 2024.

Asalin hoton, EPA
Wani bincike da wata cibiyar bincike da ke birnin New York ta yi, ya zargi ƙungiyar Houthi ta Yamen da amfani da azabtarwa da danniya wajen ci gaba da iko da akasarin yankunan ƙasar.
Cibiyar da ake kira Counter Extremism Project ta ce ƙungiyar da ke samun goyon bayan Iran na kai hari kan ƴan adawa da mabiya wasu addinai wurin yaɗa da aƙidarta.
Wakilin BBC ya ce ƙungiyar Houthi wanda ta karɓe mulki shekara 10 da suka gabata na da tarin makamai masu linzami da jirage mara matuƙa da ta ke amfani da su warin kai hare-hare.
A cikin wata goma sha uku da suka gabata da ƙungiyar ta kai hari kan jiragen ruwa a tekun Bahar Maliya tare da harba makamai masu linzami kan Isra'ila.
Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Juma'atu babbar rana, daga nan sashin Hausa na BBC, inda za mu kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Za ku iya leƙawa shafukanmu na sadarwa domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo.
Ku kasance tare da mu.