Me ya sa Amurka da Isra'ila suka kai wa Iran hari, kuma yaushe yaƙin zai ƙare?

Asalin hoton, Getty Images
Rikici ya ɓarke a Gabas ta Tsakiya bayan kashe jagoran addinin Iran Ayatollah Ali Khamenei, a wasu hare-haren da Amurka da Isra'ila suka ƙaddamar.
Bayan harin, shugaban Amurka Donald Trump ya buƙaci al'ummar Iran su tuntsurar da gwamnati.
A matsayin martani, Iran ta harba makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa a wurare da dama na yankin, kamar ƙasashen Isra'ila da Bahrain da Kuwait da Qatar da Hadaddiyar Daular Larabawa da Jordan da Saudiyya da tsibirin Cyprus, har ma da jiragen dakon man fetur da ke ratsawa ta mashigar Hormuz.
Haka nan ma ƙungiyar Hezbollah mai samun goyon bayan Iran da ke a Lebanon ta shiga faɗan, inda ta harba rokoki zuwa cikin Isra'ila daga sansanoninta da ke cikin Lebanon.
Isra'ila ta mayar da martani ta hanyar kai hari kan cibiyoyin Hezbollah a Lebanon.

