Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 19/09/2025.

Taƙaitattu

  • Latsa nan ku shiga tasharmu ta WhatsApp
  • Rundunar sojin Najeriya ta musanta yunƙurin juyin mulki
  • Sojin Najeriya sun kuɓutar da mutum 21 daga hannun 'yanbindiga a jihar Kwara
  • Shugaba Tinubu ya koma Najeriya bayan taron Italiya
  • 'An kashe Falasɗinawa 11 a Gaza'
  • Ba zan yi takarar shugaban ƙasa da Tinubu ba - Wike
  • An gano hanyar gwajin cutar kansa a matakin farko

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir da Umar Mikail

  1. Amurka ta sake yin fatali da daftarin tsagaita wuta kan Gaza a ƙuri'ar MDD

    Wakiliyar Amurka a UNSC

    Asalin hoton, Reuters

    Amurka ta yi watsi da wani daftarin Kwamatin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya (MDD) wanda ya bukaci a tsagaita bude wuta nan take a Gaza.

    Ita ce kasa ɗaya tilo da ta kaɗa ƙuri'ar kin amincewa da kudirin, wanda kuma ya bukaci a ƙara yawan kayan agajin da ake shigarwa zirin.

    Jakadan Falasdinawa a MDD Riyad Mansour ya nuna rashin jin daɗinsa game da matakin.

    "Babban abin takaici da ɓacin rai ne dakile wannan kudiri. Abin damuwa ne hana wannan kwamati gudanar da aikinsa na kare fararen hula, yayin da ake tsaka da aikata kisan ƙare-dangi," in ji shi.

    Wannan karo na shida da Amurka ke hawa kujerar na-ƙi, kasancewarta ɗaya daga cikin ƙasashe biyar masu kujerar dindindin a kwamatin UNSC.

  2. Assalamu Alaikum

    Maraba da shigowa shafin labarai kai-tsaye na yau Juma'atu - babbar rana.

    Za mu mayar da hankali kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da kuma makwaɓatansu.