Amurka ta sake yin fatali da daftarin tsagaita wuta kan Gaza a ƙuri'ar MDD
Amurka ta yi watsi da wani daftarin Kwamatin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya (MDD) wanda ya bukaci a tsagaita bude wuta nan take a Gaza.
Ita ce kasa ɗaya tilo da ta kaɗa ƙuri'ar kin amincewa da kudirin, wanda kuma ya bukaci a ƙara yawan kayan agajin da ake shigarwa zirin.
Jakadan Falasdinawa a MDD Riyad Mansour ya nuna rashin jin daɗinsa game da matakin.
"Babban abin takaici da ɓacin rai ne dakile wannan kudiri. Abin damuwa ne hana wannan kwamati gudanar da aikinsa na kare fararen hula, yayin da ake tsaka da aikata kisan ƙare-dangi," in ji shi.
Wannan karo na shida da Amurka ke hawa kujerar na-ƙi, kasancewarta ɗaya daga cikin ƙasashe biyar masu kujerar dindindin a kwamatin UNSC.