Sallama
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen shafin a yau.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.
Mu kwana lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 19/09/2025.
Usman Minjibir da Umar Mikail
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen shafin a yau.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.
Mu kwana lafiya.
Kafafen yaɗa labaran Amurka sun bayar da rahoton cewa gwamnatin Trump na neman amincewar majalisar dokokin ƙasar don sayar wa Isra'ila kayan aikin soji na kusan dala biliyan shida.
An fahimci shirin ya ƙunshi jirage masu saukar ungulu 30 masu kai hari, da kuma motocin yaƙi fiye da 3,000.
Labarin shirin sayar da makaman na zuwa ne yayin da Isra'ila ta sanar da fara ƙaddamar da abin da ta kira ƙarfin da ba ta taɓa amfani da shi ba a ci gaba da hare-haren da take kai wa Birnin Gaza.
A ranar Juma'a rundunar sojin Isra'ila ta ce kusan Falasɗinawa 480,000 ne suka bar birnin tun ƙarshen watan Agusta.
Shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas zai yi jawabi a zauren Majalisar Dinkin Duniya ta bidiyo a mako mai zuwa bayan da Amurka ta hana shi bizar shiga birnin New York.
Mambobin Majalisar sun amince da kudirin da zai bai wa Mista Abbas damar yin jawabi a wurin taron shugabannin kasashen duniyar.
A watan da ya gabata, Amurka ta ce ta hana Mr Abbas da wasu jami'an Falasdinawa 80 takardar bizar saboda kokarin da suke yi na ganin wasu kasashe sun amince da kafa kasar Falasdinu.
Ƴargidan shugaban Kamaru, ta yi kira ga ƴan ƙasar kada su sake zaɓar mahaifinta a zaɓen shugaban ƙasar da ke tafe cikin watan Octoban.
Cikin wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na TikTok, Brenda Biya ta ce babu abin da mahaifinta ya tsinana wa mutanen Kamaru ciki har da danginta sai wahala.
A shekarar da ta gabata ne Brenda Biya ta fito ƙarara ta bayyana cewa ita ƴar maɗigo ce, wanda kuma hakan babban laifi ne a ƙasar da ke tsakiyar Afirka.
Ana sa ran Paul Biya - shugaban ƙasar da ya fi kowa daɗewa kan karagar mulki a duniya - zai lashe zaɓen shugaban ƙasar da za a yi cikin watan Octoba, a wa'adin mulki na 12, bayan da aka haramta wa babban mai hamayya da shi, Maurice Kamto.
Ƙungiyar tsaro ta Nato ta ce dakarunta sun tare jiragen yaƙin Rasha uku da suka keta sararin samaniyar Estonia.
Ma'aikatar harkokin wajen Estonia ta yi Allah wadai wadai da kutsen jiragen Rashar zuwa samaniyarta.
Ta ce jiragen yaƙin Rasha uku sun shiga sararain samaniyar ɗaya daga cikin mambobin Nato ''ba tare da izini ba, inda suka ci gaba da kasancewa a ƙasar har na tsawo minti 12'', a ranar Juma'a a samaniyar tekun ƙasar.
Kakakin ƙungiyar tsaro ta Nato, Allison Hart ta ce ƙawancen sojin ya ''mayar da martani cikin gaggawa tare da kakkaɓo jiragen'' .
Mist Hart ta bayyana lamarin a matsayin gangancin da Rasha ke ci gaba da yi, da kuma irin martanin da ƙungiyar Nato za ta yi''.
Kawo yanzu Rasha ba ta ce komai ba game da lamari.
Takun saka tsakanin nato da Moscow ya ƙara ƙamari tun bayan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine a 2022.
Shugaba Trump na Amurka ya yi ikirarin cewa shi da takwaransa na China Xi Jinping sun cimma yarjejeniyar da za ta ba a damar ci gaba da amfani da dandalin sada zumunta na TikTok a Amurka.
Sanarwar ta Mista Trump na zuwa ne bayan magana ta waya da suka yi da takwaransa na China, sai da har ya zuwa yanzu babu tabbacin hakan daga Shugaba Xi.
Kafofin yaɗa labaran China sun ruwaito cewa Shugaba Xi na cewa zai goyi bayan tuntuɓar juna da za a yi domin magance matsalar batun TikTok.
Batun bayanan tsaro ne suka sanya mjalisar dokokin Amurka kafewa sai an haramta dandalin matsawar ko kuma a sayar wa wani kamfanin Amurka ba.
Shugabanin Amurka da China sun amince da gawanar ga-da-ga da za su yi nan da wta uku a Koriya ta Arewa.
Gwamnan jihar Rivers Siminalayi Fubara ya buƙaci duka al'ummar jihar Rivers - ba tare da la'akari da bambancin siyasa ko addini ko ƙabilanci ba - domin ciyar da jihar gaba.
Yayin da yake jawabi a ga al'ummar jihar a birnin Fatakwal a ranar Juma'a, Fubara ya gode wa Shugaba Tinubu bisa ƙoƙarin da ya ce ya yi wajen sasanta rikicin siyasar jihar.
''A madadin gwamnati da al'ummar jihar Rivers muna miƙa saƙon godiyarmu ga mai girma shugaban ƙasa, bisa sanya baki da ya yi wajen sansanta rikicin siyasar jiharmu''.
A ranar Laraba ne Shugaba Tinubu ya sanar da kawo ƙarshen wa'adin dokar ta-ɓaci da ya sanya wa Rivers ta tsawon wata shida, sakamakon rikicin siyasar jihar da ya ƙi-ci-ƴa-ƙi-cinyewa.
Gwamnan ya ce a tsawon wata shidan da jihar ta ɗauka ƙarƙashin dokar, Tinubu ya yi ƙoƙarin sasanta duka ɓangarorin.
''Kuma dukanmu, kama daga Jagoranmu, Nyesom Wike da duka mambobin majalisar dokokin jiharmu da ni kaina gwamna mun amince da sasancin tare da yin watsi da saɓanin da muka samu a baya'', in ji shi.
Fubara ya ce a yanzu shi da duka sauran ƴansiyasar jihar sun sanya jihar da muradunta a gaba domin ciyar da Rivers gaba.
Jagororin mulkin sojin Sudan sun yi allah wadai da harin jirgi maras matuƙi da aka kai kan wani masallaci a birni El Fasher da ke yankin Darfur.
Sojojin sun ce harin ya kashe fiye da mutum 70 tare da ɗora alhakin harin kan mayaƙan RSF.
Jagororin mulkin sun ce kai wa mutanen hari - waɗnada ke tsaka da sallar asuba - babban laifi ne kuma abin kunya.
Rundunar RSF na yaƙi a Sudan domin ƙwace iko da birnin daga hannun sojojin ƙasar, yayain da yaƙin ƙasar ke ƙara tsananta.
Sai dai kawo yanzu ba ta ɗauki alhakin harin ba.
Akwai rahotonnin da ke cewa a yanzu haka ƙungiyar na iko da sansanin ƴangudun hijira da ke wajen birnin El Fasher.
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya kai wa iyalan tsohon shugaban ƙasar, marigayi Muhammadu Buhari a gidansa da ke Kaduna.
A lokacin ziyarar Tinubu na tare da shugban majalisar dattawan ƙasar, Sanata Godswill Akpabio da kakakin majalisar wakilan ƙasar, Hon Tajedeen Abbas da gwamnan Kaduna Sanata Uba Sani, da sauran manyan masu riƙe da muƙamai a ƙasar.
A yayin ziyayar Tinubu ya samu tarba daga iyalan marigayin ƙarƙashin jagorancin maiɗakinsa, Hajiya Aisha Buhari.
Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya shiga fadar gwamnatin jihar yau Juma'a, kwana ɗaya bayan shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ɗage dokar ta-ɓaci da ya ƙaƙaba a jihar.
Fubara ya shiga gdan gwamnati ne tare da rakiyar mai ɗakinsa, Valerie Fubara da mataimakiyarsa Ngozi Nma Odu.
A lokacin da ya isa gidan gwamnati, Fubara ya shaida wa dandazon mutanen da suka taru domin tarbarsa cewa "ƙaunar da kuka nuna min ta sa jikina ya yi sanyi."
Tun a ranar Laraba ne shugaban na Najeriya Bola Tinubu ya sanar da kawo ƙarshen dokar ta-ɓacin, inda ya ce "daga Alhamis 18 ga watan Satumba, Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Ngozi Nma Odu, da mambobin majalisar dokokin jihar ƙarƙashin jagoracin kakakin majalisar jihar, Martins Amaewhule, za su koma aikinsu''.
Hakan ya kawo ƙarshen dokar da ta shafe tsawon wata shida a jihar tun bayan da shugaban ya sanar da ita ranar 18 ga watan Maris ɗin 2025.
Sai dai rashin bayyanar Gwamna Fubara a gidan gwamnati jiya Alhamis ya haifar da raɗe-raɗi game da inda ya ke da kuma abin da ya hana shi komawa ofis.
Wasu da dama sun soki shugaban Najeriya Bola Tinubu kan dakatar da zaɓaɓɓen gwamnan jiha da kuma ƴan majalisa.
Sai dai shugaban ya ce ya yi hakan ne domin samun maslaha bayan turnuƙewar rikicin siyasa tsakanin Fubara da magabacinsa Nyesom Wike.
Shugaban Amurka, Donald Trump tare da takwaransa na China Xi Jinping sun yi magana ta waya karon farko cikin wata uku.
Shugaba Trump ya ce sun yi tattaunawa mai ma'ana, musamman kan batun TikTok tare da amincewa da yin ganawar ga-da-ga ciin wata mai zuwa a Koriya ta Kudu.
Kafofin yaɗa labaran China sun ce, Shugaba Xi ya shaida wa Mista Trump cewa ya kamata Amurka ta daina ƙaƙaba wa kayayyakin ƙasar ƙarin haraji.
An kuma bayar da rahoton cewa Shugaba Trump ya ce faretin soji da aka gudanar a China cikin watan da ya gabata ya ƙayatar.
A lokacin gudanar da faretin, Mista Trump ya zargi shugabannin China da Rasha da Koriya ta Arewa da haɗe wa Amurka kai.
Ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa ta Najeriya reshen Abuja ta janye yajin aikin da ta fara yi a farkon makon nan.
Shugaban ƙungiyar Association of Resident Doctors mai suna George Ebong ya faɗa wa jaridar Premium Times cewa shiga tsakanin da Majalisar Dattawan Najeriya ta yi ne ya sa ska jingine yajin aikin.
Ya ƙara da cewa tsagaitawa da yajin suka yi ba dakatarwa gaba ɗaya, yana mai cewa ba a biya ko ɗaya daga cikin buƙatun nasu ba.
"Mun dakatar da yajin aikin kuma za mu ci gaba da aiki daga ranar Litinin," a cewarsa.
"Duk da cewa ba a biya ko ɗaya daga cikin buƙatunmu ba, sun tabbatar mana cewa za su tattauna da minista, kuma majalisarmu ta yanke shawarar amincewa da 'yanmajalisar suka faɗa."
Ya ce majalisarsu za ta sake taruwa domin tantance alƙawuran da aka ɗauka, "kuma idan ba a yi komai ba za ta ɗauki mataki na gaba".
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya isa birnin Kaduna a yau JUma'a domin halartar ɗaurin auren Nasirudeen Yari, ɗa ga Sanata Abdulaziz Yari.
Fadar shugaban ƙasa ta ce Tinubu zai yi amfani da balaguron wajen kai wa iyalin marigayi Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a Kadunan.
Tuni shugaban ya yi sallar Juma'a a Masallacin Sultan Bello da ke ƙwaryar birnin.
Gwamnan jihar Rivers a kudancin Najeriya, Siminalayi Fubara, ya isa birnin babban birnin jihar domin komawa kan kujerarsa bayan ƙarewar wa'adin dakatarwar da gwamnatin tarayya ta yi masa.
Fubara ya isa filin jirgin sama na Fatakwal ne da misalin ƙarfe 12:19 a yau Juma'a, fiye da awa 24 kenan da ƙarewar wa'adin dokar ta-ɓacin da Shugaba Tinubu ya kafa, wadda ta dakatar da shi tare da majalisar dokokin jihar.
Dubban magaoya bayansa ne suka tarɓe shi, kuma rahotonni na cewa tuni ya kama hanyar isa fadar gwamnatin jihar domin ci gaba da aiki.
Yayin da majalisar ta koma bakin aiki tun a jiya Alhamis, Fubara bai koma duk da yayin da yadda magaoya suka yi wa fadar tsinke domin ganin isarsa.
Tun a watan Maris ne Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya sanar da saka dokar ta-ɓacin saboda iƙirarin da ya yi na "rashin doka da oda" sakamakon rikicin siyasa tsakanin Fubara da tsohon gwamna kuma ministan Abuja a yanzu, Nyesom Wike.
Rundunar 'yansandan Najeriya reshen jihar Legas ta ce ta kama mutum 18 sakamakon zanga-zangar da suka yi a kasuwar Tejuosho saboda yawan ɗaukewar lantarki.
A ranar Alhamis ne masu zanga-zangar suka fantsama a kasuwar domin nuna ɓacin ransu, amma sai macin nasu ya rikiɗe zuwa tashin hankali bayan 'yansanda sun harba musu hayaƙi mai sa hawaye.
Kakakin rundunar Babaseyi Oluseyi ya ce tuni suka fara bincike kan mutanen da suka kama zuwa yanzu.
"Dakaru sun kama 'yandaba 18 saboda tashin hankalin da suka haifar. Wasu daga cikinsu sun kai wa 'yansandan da ke gadin wani banki a kasuwar hari," in ji shi cikin sanarwar da ya fitar a yau Juma'a.
Gwamnatin Taliban ta haramta amfani da litattafan da mata suka rubuta wajen koyarwa a jami'o'in Afghanistan.
Sababbin dokokin sun haɗa da haramta koyar da darussan kare haƙƙi da kuma na cin zarafi ta hanyar lalata.
Akwai litattafai kusan 140 da mata suka rubuta da ke cikin 680 da gwamnatin ta ce tana da "damuwa" a kansu saboda "saɓa wa Shari'ar Musulunci da al'adun Afghanistan".
Haka nan, an faɗa wa jami'o'in cewa su daina koyar da wasu darussa 18, inda wani jami'in Taliban ɗin ya ce "sun ci karo da tanadin Shari'ar Musulunci da tsarin gwamnati".
Taliban ta kawo sauye-sauye da dama tun bayan komawa kan mulki a 2021, inda sauyin ya taƙaita wa mata 'yancin yin wasu abubuwa da dama.
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma jagoran adawa Atiku Abubakar ya ɗauki nauyin karatun ɗalibai uku da suka yi nasara a gasar Turancin Ingilishi ta TeenEagle Global Finals a Ingila.
Wata sanarwa da Gidauniyar Atiku ta fitar mai kwanan watan 5 ga watan Agusta ta ce nasarar da Nafisa Abdullahi, da Rukaiya Mohammed Fema, da Khadija Kashim Kalli suka yi "shaida ce cewa kwane yaro na iya cim ma burika".
"Saboda karrama wannan bajinta taku, Gidauniyar Atiku Abubakar za ta ɗauki nauyin kammala karatun sakandare da kuma na duk jami'ar da kuka zaɓa," a cewar sanarwar da sakataren gidauniyar, Farfesa Ahmadu Shehu ya fitar.
A farkon watan Agusta ne matasan 'yan asalin jihar Yobe suka doke takwarorinsu 20,000 daga sassan duniya a gasar bayan sun wakilci Najeriya daga makarantar Tulip International College.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Atiku ya ce a jiya Alhamis ne ɗaya daga cikinsu Nafisa Abdullahi ta kai masa ziyara a gidansa da ke Abuja, babban birnin Najeriya.
Hukumomi a jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutum 58 sakamakon annobar amai da gudawa a ƙananan hukumomi 14 cikin 20 na jihar.
Haka nan, akwai mutum 258 da aka tabbatar sun kamu da cutar ta kwalara, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito Mataimakin Gwamnan Bauchi Auwal Mohammed Jatau yana bayyanawa ranar Alhamis.
Babban jami'in gwamnatin ya bayyana hakan ne yayin rantsar da wasu kwamatoci biyu domin yaƙi da kwalara.
"Wannan annobar abu ne da za a iya magancewa a tsawon lokaci ta hanyar tsaftace ruwan sha, da tsaftar jiki," in ji shi.
Hukumar kula da harkokin ruwa ta Najeriya ta yi gargaɗi kan barazanar aukuwar ambaliya sakamakon tumbatsar madatsun ruwa a wasu jihohin ƙasar.
Hukumar Nigeria Hydrological Services Agency (NiHsa ) ta yi kira ga jama'ar da ke zaune a wuraren da abin ka iya shafa da su gaggauta tashi daga wuraren kafin aukuwar ambaliyar da ake hasashe.
"Da yawa kogunanmu sun cika, kuma su ne ke bai wa madatusn ruwanmu ruwan. Abin ya kai ga su ma madatsun ruwan sun cika har sun fara sakin ruwan," kamar yadda shugaban hukumar NiHsa Dr Umar Ibrahim ya shaida wa BBC.
Shugaban ya bayyana irin garuruwan da ke fuskantar barazanar ambaliyar, mafi yawansu a jihar Neja da Sokoto da Kebbi.
"Duk wani gari da ke kusa ko kuma kan hanyar Kogin Neja yana cikin barazana. Garuruwa kamar Bargu, Fatagi, Makwa - duka suna kan hanyar kogin da ke cikin jihar Neja.
"A ɓangaren Jaba kuma, akwai su Gungu, Gana, Bare, Goba, Baro - duk su ma suna cikin haɗari.
"Akwai kuma madatsar ruwa ta Goronyo ta buɗe. Garuruwan Sokoto, Goronyo, Wamako, Shinaka, Yarimawa - duka suna cikin haɗari."
Rahotanni daga birnin Paris na cewa Faransa ta dakatar da aikin yaƙi da ta'addanci na haɗin gwiwa da ƙasar Mali tare da korar jami'an diflomasiyyar kasar biyu,waɗanda aka ce jami'an tsaro ne.
Matakin ya biyo bayan kama wani jami'in tsaron Faransa da ke aiki a ofishin jakadancin ƙasar na babban birnin Mali Bamako a watan da ya gabata bisa zargin sa da neman tayar da fitina.
Malin ta kuma ayyana wasu jami'an diflomasiyyar Faransa biyar a matsayin wadanda ba a maraba da su, abin da ya sa suka fice daga kasar a karshen mako.
An kama jami'in diflomasiyyar na Faransa ne tare da wasu manyan hafsoshin sojin Mali.