Nicky ya naɗa mahaifinsa mataimakinsa a Quuens of the South, Queens of the South
Nicky Clark ya naɗa mahaifinsa mataimakinsa a lokacin da tsohon ɗan wasan Rangers da Dundee United zai fara aikin kociyan, Queens of the South.
Ɗan wasan mai shekara 34 ya koma Palmerston Park a zagaye na biyu a kakar wasan da ta gabata, inda ya zura ƙwallaye bakwai a wasa 13 da ya buga.
Zai ci gaba da taka leda a kakar wasa mai zuwa, yayin da ƙungiyar Queen of the South ta Scottish League One ke da kwarin gwiwar cewa suna da tsarin da zai ba shi damar hada aikin wasa da kuma horarwa a lokaci guda.
Sandy, mai shekara 69, ya dawo a matsayin mataimakin koci na Queens karo na uku, bayan da ya taɓa aiki sau biyu a karkashin Allan Johnston a baya.
A matsayinsa na tsohon ɗan wasan gaba a Rangers da Heart of Midlothian, ya bar aikin koci a ƙungiyar Albion Rovers ta Lowland League domin komawa aiki tare da dansa.
A karo na karshe da suka yi aiki tare a Palmerston shi ne a kakar 2012–13, lokacin da suka lashe Second Division da Challenge Cup, inda Nicky Clark ya zura ƙwallaye 41 a wasanni 46.

Asalin hoton, Getty Images











