Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya - Laraba 23 ga watan Afrilu, 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail da Habiba Adamu da Ibrahim Yusuf Mohammed da Ahmad Bawage

  1. Gwamnatin jihar Neja ta haramta yawo da gashin dada

    ,,,

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnan jihar Neja da ke tsakiyar Najeriya, Umar Bago, ya umarci jami'an tsaro da su kama ƴandaba da duk waɗanda ke da hannu wajen tayar da zaune tsaye a Minna, babban birnin jihar.

    Bago ya bayar da umarnin ne bayan samun tashe-tashen hankula a birnin na Minna.

    Umarnin nasa ya hada da kama mutanen da ke yawo da gashin dada.

    Tuni dai gwamnatin jihar ta sanya dokar takaita zirga-zirgar mutane da baburan haya, domin magance rikicin ƴandaba da birnin ke fama da shi.

    Lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane goma, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

  2. Akwai ƴanƙasar waje da ke kai hari a Benue - Alia

    ,,,

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnan jihar Benue da ke tsakiyar Najeriya, Hyacinth Alia ya yi zargi cewa maharan da suka kai hari jihar ba ƴan Najeriya ba ne.

    Gwamnan ya faɗi hakan ne a wani shirin gidan talbijin na Channels, inda ya ce maharan na magana ne da wata irin Hausa da Fulatanci wanda ba irinsu ake yi a ƙasar ba.

    "Waɗannan mutanen sun zo ne a shirye da makamansu da bindigogi ƙirar AK-47 da 49. Kuma ba su yi kama da ƴan Najeriya ba, ba sa magana kamar yadda muke yi, Hausarsu ba irin ta mu ba ce. "

    Inda ya ƙara da cewa daga bayanan sirrin da suka samu daga mazauna yankunan da aka kai hare-hare, ya nuna cewa maharan ƴanƙsar waje ne.

    Hakan na zuwa ne bayan wata ziyarar nuna alhini da mai baiwa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya kai jihar.

    Inda ya bai wa al'umomin jihar tabbataci kan matakan da ya ce gwamnatin na ɗauka domin magance matsalar tsaro a ƙasar.

    Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da ake zargin wasu ƙungiyoyin ƴanbindiga na ƙasashen waje na kai hari wasu sassan ƙasar.

    Kamar ƙungiyar Lakurawa da ke kai hare-hare a jihohin Sokoto da Zamfara da ke arewa-maso-yammacin ƙasar.

  3. Za a fara bankwana da gawar Fafaroma Francis

    ,,,

    Gawar Fafaroma Francis ta isa Cocin St Peter’s Basilica, inda za a ajiye ta domin yi mata bankwana.

    Za a fara da gudanar da addu'o'i tukuna, kafin a bar masu makoki su fara wucewa ta gaban akwatin gawar domin girmamawa da sallama da babban limamin mabiya darikar ta Katolika na duniya.

    Gawar za ta kasance a cocin na St Peter’s Basilica na tsahon kwanaki uku, kafin ayi jana'iza a binne shi a ranar Asabar.

    A harabar cocin tuni mutane suka taru domin samun yin bankwana da gawar.

    Haka zalika an fara shirye-shirye da karbar baƙuncin dubban mabiya da wakilan akalla kasashe 100 da za su halarci jana'izar.

    An dai tsaurara matakan tsaro a ciki da wajen birnin Roma.

  4. Assalamu Alaikum

    Ma'abota BBC Hausa barkanmu da hantsin Laraba - ta bawa ranar samu.

    Ku biyo mu domin sanin halin da duniya ke ciki, musamman a Najeriya da Nijar da maƙwabtansu a yau.