Alcaraz ya kai daf da karshe a karon farko a Australian Open, Australian Open
Asalin hoton, Getty Images
A gasar
tennis ta Australian Open da ake gudanarwa a Melbourne, Carlos Alcaraz ya kai
wasan daf da karshe a karon farko a kofin da ya kasa dauka.
Wanda yake
matsayi na daya a duniya ya doke Alex de Minaur da cin 7-5, 6-2, 6-1. kenan dan
kasar Sifaniya zai kece raini a wasan gaba da Alexander Zverev, wanda ya fitar
da Learner Tien.
A gobe ake
sa ci gaba da wasan kwata fainals tsakanin Novak Djokovic mai kofin 10 da
Lorenzo Musetti.
A bangaren
mata kuma, Elina Svitolina ta doke Coco Gauff da cin 6-1, 6-3 cikin minti 59,
karon farko da ta kai daf da karshe a wasannin –
Za kuma ta
fuskanci Aryna Sabalenka, wadda ta caskara Iva Jovic da cin 6-3, 6-0.
, Damben boksin
Fafatawar neman kambun duniya ajin bantamweight tsakanin Francesca
Hennessy da Ellie Bouttell za ta ja hankali ranar Asabar a Copper Box Arena a
Landan.
Damben da za
a yi tsakanin yan Burtaniya ya zama babban wasa, saboda karawar neman kambu
ajin light-welterweight tsakanin Adam Azim da Gustavo Lemos ta zama kwantai,
sakamakon raunika da dukkan ‘yan damben suka samu.
West Ham na shirin ɗaukar Traore daga Fulham, Premier League
Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar
West Ham na dab da kammala sayen dan wasan Fulham, Adama Traore, ana jiran sakamako auna koshin lafiyarsa da aka yi.
Dan wasan
mai shekaru 30 zai sake taka leda karkashin Nuno Espirito Santo, wanda ya taba
horar da shi a Wolverhampton.
Traore,
wanda ya buga wa Sifaniya wasa takwas, ya yi karawa biyu a Fulham a Premier
League a kakar nan – bai buga karawar da kungiyar ta ci Brighton 2-1 ranar
Asabar.
, Bournemouth
Asalin hoton, Getty Images
Kungiyar Bournemouth ta kammala sayen dan wasan gaba Rayan daga Vasco da Gama kan kudin farko na fam miliyan 24.7, bisa kwantiragin shekaru biyar da rabi, wanda kuma ya kunshi kari na fam miliyan 5.6 idan an cika wasu sharudda.
Bournemouth ta doke wasu kungiyoyi da dama daga Turai, da kuma kungiyoyi daga Saudiyya da Rasha, domin samun sa hannun dan wasan Brazil mai shekaru 19.
Wannan shi ne saye na biyu mafi tsada a tarihin Bournemouth, tare da fam miliyan 32 da suka biya a 2024 domin dauko dan kasar Brazil kuma dan wasan gaba Evanilson daga Porto.
Rayan ya koma gabar tekun kudancin Ingila ne a matsayin maye gurbin dan wasan gaba Antoine Semenyo, wanda ya koma Manchester City kan kusan fam miliyan 65 a farkon wannan wata.
Matashin dan wasan na taka leda ne a matsayin dan wasan gaba na tsakiya mai amfani da kafar hagu, amma yana iya buga wasa a bangarori biyu na gaba. Dan wasan tawagar Brazil ta ‘yan kasa da shekaru 20 ya ci kwallaye 14 a wasanni 34 na gasar firimiya ta Brazil a kakar da ta gabata.
Haka kuma, kungiyar Bournemouth ta kammala yarjejeniyar aro da golan kasar Girka, Christos Mandas, daga kungiyar Lazio ta gasar Serie A ta Italiya.
Golan mai shekaru 24, wanda ya zama dan wasan Girka na farko a tarihin kulob din, ya zo ne a matsayin aro har zuwa karshen kakar wasa, tare da zabin saye gaba daya.
Bournemouth na biyan kudin aro na euro miliyan 1.5 (fam miliyan 1.3), sannan za su biya karin fam 860,000 idan suka yanke shawarar kada su saye shi gaba daya.
Idan suka zabi sayen sa a dindindin, farashinsa zai kai fam miliyan 16.
, Daga Jaridu
Asalin hoton, Getty Images
Ɗanwasan gaba na Faransa Randal Kolo Muani, mai shekara 27 na Paris St-Germain da ke murza leda a matsayin aro a Tottenham wani zaɓi ne da Juventus take dibawa. (Fabrizio Romano)
Ɗanwasan tsakiya na Manchester United Bruno Fernandes zai jira sai ƙarshen kaka kafin tabbatar da makomarsa inda kwangilar ɗanwasan za ta kawo ƙarshe a 2027 duk da yana da zaɓin ƙarin shekara guda. (Mirror).
Atletico Madrid na tattaunawa da Atalanta domin karɓo ɗanwasan tsakiya na Brazil Ederson. (AS - in Spanish)
Kano Pillars za ta kara da Katsina United ranar Laraba, Premier League ta Najeriya mako na 23
Asalin hoton, npfl
Za a buga wasa 10 ranar Laraba a ci gaba da gasar Premier League ta Najeriya.
Kano Pillars da Katsina United
Warri Wolves da Remo Stars
Rivers United da El-Kanemi Warriors
Nasarawa United da Enyimba
Bayelsa United da Niger Tornadoes
Kun Khalifat da Kwara United
Bendel Insurance da Barau FC
Plateau United da Rangers International
Abia Warriors da Wikki Tourists
Ikorodu City da Shooting Stars Sports Club
Dorgu zai yi jinyar mako a Manchester United, Manchester United
Asalin hoton, Getty Images
Watakila ɗan wasan Manchester United, Patrick Dorgu zai yi jinyar makonni bayan raunin da ya ji a karawar da suka doke Arsenal 3-2 a Emirates a Premier League ranar Lahadi.
Mai shekaru 21, wanda ya zura ƙwallon ta biyu a wasan ya fita daga fili yana jan kafa a karshen fafatawar, inda kocin rikon kwarya Michael Carrick ke fatan cewa raunin ba wani mai girma bane.
Sai dai alamu sun nuna raunin ya fi haka tsanani, kodayake majiyoyi sun ce har yanzu ana ci gaba da duba lafiyarsa, kuma ba a bayyana tsawon lokacin da zai yi jinyar ba.
Dorgu, wanda ke kan ganiya a kakar nan, ya koma United daga Lecce watan 12 da suka gabata. A karkashin Carrick, yana nuna ƙwarewarsa sosai, haka kuma ya zura ƙwallo ma a nasarar da United ta samu a baya a kan Manchester City.
Manchester United na da wasa takwas a Premier League nan gaba kafin hutun wasannin kasa da kasa a watan Maris, inda ake sa ran Dorgu zai wakilci Denmark a karawar neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya.
Aston Villa za ta kara karɓar aron Douglas Luiz, Aston Villa
Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar Aston Villa ta cimma yarjejeniya domin sake ɗaukar aron tsohon dan wasanta, Douglas Luiz.
Mai shekaru 27 yana buga wasannin aro a halin yanzu a Nottingham Forest daga Juventus, amma ana sa ran zai bar filin City Ground kafin wa’adin rufe kasuwar saye da sayar da ƴan yawa ya cika ranar Litinin, sannan ya koma Villa.
Chelsea ma ta nuna sha’awar ɗaukar ɗan wasan na Brazil, amma majiyoyi sun shaida wa BBC cewa zuciyarsa tafi son komawa Aston Villa, wadda ya bugawa wasa 204 daga 2019 zuwa 2024.
Yarjejeniyar ta kunshi har da zabin sayen ɗan wasan idan ya taka rawar gani.
Aston Villa ta sayar da Luiz ga Juventus kan fam miliyan 42.5 a watan Yunin 2024.
Ya fara wasa uku kacal a gasar Serie A kafin ya koma Nottingham Forest a matsayin aro a watan Agustan 2025.
, Daga Jaridu
Asalin hoton, Getty Images
Everton ta yi watsi da tayin Lazio kan ɗanwasan tsakiya na Ingila Tim Iroegbunam. (Corriere dello Sport - in Italian)
Wolves ta yi watsi da tayin fam miliyan 6.9 daga Roma kan ɗanwasanta na baya David Moller Wolfe. (Sky Sports)
Tsohon kocin Southampton da Rangers Russell Martin na cikin waɗanda ake tunanin Leicester City za ta ɗauko bayan bayan korar Marti Cifuentes. (Football Insider)
Za a buga wasan karshe a kofin duniya a 2030 a Sifaniya, Fifa World Cup 2030
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban hukumar ƙwallon kafar Sifaniya ya bayyana cewa za a gudanar da wasan karshe a gasar cin kofin duniya a 2030 a Sifaniya.
Za a yi haɗakar karɓar baƙuncin gasar tsakanin Sifaniya da Portugal da Morocco, yayin da wasa uku na farkon buɗe labulen gasar za a buga su a Uruguay da Argentina da kuma Paraguay domin tunawa da cika shekaru 100 da fara wasannin babbar gasar tamaula ta duniya.
Morocco ta nuna sha’awar karɓar bakuncin wasan karshe a 2030, amma shugaban hukumar kwallon kafa ta Spain, Rafael Louzan, ya ce: “Sifaniya ta daɗe tana nuna ƙwarewa wajen shirya manyan gasa ta duniya.”
Filin wasa na Santiago Bernabeu na Real Madrid da kuma Nou Camp na Barcelona ana kallonsu a matsayin manyan wuraren da za su iya karbar bakuncin wasan, sai dai Louzan bai bayar da karin bayani ba.
BBC ta tuntubi hukumar ƙwallon kafa ta duniya FIFA, wadda ke da ikon yanke hukunci na karshe kan inda za a buga wasan, da kuma hukumomin ƙwallon kafa na Portugal da Morocco domin jin ta bakinsu.
Morocco na son a buga wasan karshe a birnin Casablanca, a sabon filin wasa mai suna Grand Stade Hassan II, wanda ake sa ran kammala shi a shekarar 2028 kuma zai iya ɗaukar mutane 115,000.
Bayern za ta tsawaita yarjejeniyar Kane a ƙungiyar, Bayern Munich
Asalin hoton, Getty Images
Daraktan wasannin Bayern Munich, Max Eberl, ya ce suna tattaunawa da Harry Kane kan batun tsawaita kwantiraginsa.
Ƙyaftin ɗin tawagar Ingila mai shekaru 32 ya koma Bayern ne a watan Agustan 2023 daga Tottenham, kan yarjejeniyar kaka huɗu kan (£86.4m).
Tun daga lokacin, Kane ya ci ƙwallo 119 tare da bayar da bayar da 30 aka zura a raga a wasa 126 da ya buga wa Bayern, sannan ya lashe babban kofin tamaula na Jamus a tarihinsa na tamaula, sakamakon ɗaukar Bundesliga a kakar 2024–25.
A wannan kakar ta bana, ya ci ƙwallo 34 a wasa 30 da ya buga wa ƙungiyar da Vincent Kompany ke jan ragama, ciki har da ƙwallo 21 a wasa 19 a Bundesliga, yayin da yake kokarin karya tarihin tsohon ɗan wasan Bayern, Robert Lewandowski, na cin ƙwalo 41 a kakar Bundesliga guda ɗaya.
Kane ya kuma taimaka wa Bayern tana matsayi na biyu a teburin gasar Champions League, bayan da saura wasa ɗaya da ya rage mata a cikin rukuni.
Barkanmu da shiga sharhi da bayanan wasanni
Jama'a barkanmu da shiga shirin sharhi da bayanan wasanni kai tsaye tare da ni Mohammed Abdu Mamman Skipper Tw.
Za ku iya tafka muhawara a shirin ko bayar da gudunmuwa a BBCHausa Facebook.