Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 03/01/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail da Haruna Kakangi

  1. Gwamnatin Venezuela za ta ba da lada ga duk wanda ya faɗi inda jagoran adawa yake

    Gwamnatin Venezuela ta sanar da cewa za ta bayar da tukwicin dala 100,000 ga duk wanda ya bayar da bayanan da za su kai ga kama jagoran 'yan'adawar ƙasar da ya yi gudun hijira.

    Edmundo Gonzales ya tsere daga ƙasar a watan Satumban bara kuma ya samu mafaka a Sifaniya bayan mahukuntan ƙasar sun bayar da umarnin kama shi.

    Sai dai ya yi alƙawarin komawa wa Caracas kafin a rantsar da Shugaba Nicolas Maduro a ranar Juma'a mai zuwa, inda ya zargi gwamnati da maguɗin zaɓe.

  2. Gwamnatin Tinubu ta kashe abin da ya zarta giɓin kasafin kuɗi na 2024

    Bola Tinubu

    Asalin hoton, State House

    Kuɗaɗen da gwamnatin Najeriya ta kashe a matsayin giɓi na kasafin kuɗi sun ƙaru da kashi 28 cikin 100 zuwa naira tiriliyan 12.1 cikin wata 10 na farkon shekarar 2024 idan aka kwatanta da na 2023.

    Wani rahoto da Babban Bankin Najeriya CBN ya fitar ne ya ƙunshi bayanan, inda aka gano cewa giɓin kasafin na 2024 naira tiriliyan 9.8 ne.

    Hakan na nufin gwamnatin Najeriya ta kashe kuɗin da ya zarta abin da ta ayyana a matsayin giɓin kasafin kuɗi na 2023 na naira tiriliyan 9.8 da kashi 31 cikin 100.

    Kuma ta kashe kuɗaɗen ne duk da yadda aka samu ƙaruwa wajen samun kuɗaɗen shiga a daidai lokacin da kashi 36 cikin 100.

    A kasafin kuɗi na 2025, gwamnatin Bola Tinubu ta ce za a samu giɓin naira tiriliyan 13.08 daga cikin jimillar tiriliyan 47.9 na kasafin, sannan kuma za ta biya bashi har na tiriliyan 15.81.

  3. Slovakia ta yi barazanar hukunta Ukraine saboda katse cinikin gas ɗin Rasha

    Firaministan Slovakia Robert Fico ya yui barazanar katse tallafi ga 'yan gudun hijirar Ukraine sama da 130,000 saboda rikicin da ya biyo bayan katse yarjejeniyar cinikin gas ɗin Rasha da Ukraine ɗin ta yi.

    A ranar 1 ga watan Janairu Ukraine ta kashe wani bututun gas da aka daɗe ana amfani da shi inda Rasha ke tura wa ƙasashen tsakiyar Turai makamashi.

    Slovakia ce babbar hanyar wucewar bututun kuma a yanzu za ta yi asarar miliyoyin yuro na kuɗin shiga.

    Hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da 'yan gudun hijira ta yi ƙiyasin cewa akwai 'yan Ukraine 13,530 a Slovakia daga cikin 6,813,900 da ke ƙasashen duniya.

    Fico wanda ya kai wa Shugaba Putin na Rasha ziyara a watan Disamba domin tattaunawa, ya kwatanta matakin na Ukraine da "ɓarna".

    Firaministan wanda ƙasarsa mamba ce a Tarayyar Turai ya ce zai ba da shawarar daina tura wa Ukraine wutar lantarki, da kuma rage tallafin kuɗi ga 'yan ƙasar da ke samun mafaka a ƙasarsa.

  4. 'Yansandan Abuja 140 ne suka mutu a 2024 - Kwamishina

    Olatunji Rilwan Disu

    Asalin hoton, FCT Police Command

    Kwamashinan 'yansanda na birnin Abuja a Najeriya ya ce aƙalla dakarunsa 140 ne suka mutu a bakin aiki cikin shekarar 2024 saboda tashin hankali daban-daban.

    Olatunji Rilwan Disu ya ce daga cikin dalilan da suka jawo mutuwar tasu har da arangamar da suka dinga yi da 'yan ƙungiyar IMN ta 'yan Shi'a a babban birnin.

    Da yake magana cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Alhamis, kwamashinan ya ce akwai kuma 'yansandan da suka kwanta barci amma ba su tashi ba.

    A cewarsa, tuni suka biya wasu daga cikin iyalan dakarun haƙƙoƙinsu, kamar yadda babban sufeton 'yansanda Kayode Egbetokun ya bayar da umarni.

    Daga cikin nasarorin da rundunar ta samu a 2024 akwai rahotonnin aikata laifi 1,426 da aka kai musu waɗanda suka kai ga kama masu laifi 1,077, a cewarsa.

  5. Apple zai biya tarar dala miliyan 95 kan manhajarsa ta Siri

    Apple

    Asalin hoton, Reuters

    Kamfanin Apple ya amince ya biya tarar dala miliyan 95 a ƙarar da aka shigar da shi kotun Amurka kan zargin manhajarsa ta Siri na sauraron tattaunawar sirri ta masu amfani da ita.

    Masu amfani da wayoyin Apple da kamfutarsu ta hannu wato Ipad da sauraron kamfutoci na zargin Siri da naɗar muryarsu a wasu lokutan, ko da ba su kunna ta ba.

    Sannan kuma suna zargin Apple da sace bayanan sirrinsu domin bai wa wasu kamfanonin.

    Sai dai Apple ya ce bai aikata wani laifi ba.

    Za dai a raba kudin ne tsakanin wadanda suka shigar da ƙarar.

  6. Assalamu Alaikum

    Barkanmu da hantsin Juma'atu babbar rana daga Sashen Hausa na BBC.

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye, wanda zai kawo rahotonni na abubuwan da ke faruwa daga sassan duniya, musamnna a Najeriya da Nijar da maƙwabtansu.

    Umar Mikail ne zai jagoranci kawo labaran bisa kulawar Haruna Ibrahim Kakangi.