Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 03/01/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail da Haruna Kakangi

  1. Rufewa

    Masu bibiyar shafinmu na BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

    Amma kafin nan muke cewa mu kwana lafiya.

  2. Babban burin sojojin Najeriya shi ne tabbatar da tsaron ƙasa - CG Musa

    Tsaro

    Asalin hoton, Defence HQ/X

    Babban hafsan tsaron Najeriya Janar Christopher Musa, ya jaddada ƙudirin rundunar sojin ƙasar na tabbatar da tsaro ta hanyar kawar da miyagu da ke haddasa tabarbarewar tsaro a faɗin kasar.

    Janar Musa ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan ziyarar da ya kai sananin sojojin ƙasar da ke Samaru a ƙaramar hukumar Zangon Kataf ta jihar Kaduna, kamar yadda rahotonni suka ambato.

    CG Musa ya kai ziyarar ne domin ƙaddamar da kayan aiki da rundunar sojin ƙasar ta samar a sansanin domin tunkarar ƙalubalen tsaro a Kudancin Kaduna da kewaye.

    Babban Hafsan Tsaron ya kuma yaba wa sojojin bisa ƙwarewa da sadaukarwar da suka yi wajen kare ƙasar tare da ba da tabbacin cewa jin daɗinsu shi ne abu mafi muhimmanci da shalkwatar tsaron ƙasar ta sanya a gaba.

    Ya kuma buƙaci sojoji da su yi tsayin daka wajen gudanar da ayyukansu na kare ƙasa da kuma mutunta hakkin ɗan'adam wajen gudanar da ayyukansu.

    Janar Musa ya jaddada muhimmancin haɗin kai da sauran hukumomin tsaro da fararen hula wajen cimma burin tabbatar da tsaron kasa

  3. Hamas ta ce za a koma tattaunawar tsagaita wutar yaƙin Gaza a Doha

    Ƙungiyar Hamas ta ce za a koma tattaunawar dakatar da buɗe wuta kai-tsaye tsakaninsu da Isra'ila a ranar Juma'a a birnin Doha na Qatar.

    Hamas ta ce tattaunawar za ta mai da hankali wajen kawo ƙarshen yaƙin da janyewar sojin Isra'ila daga Gaza.

    Amurka dai ta buƙaci Hamas ta amince da rattaɓa hannu kan yarjejeniyar sakin sauran Isra'ilawan da Hamas ta yi garkuwa da su ranar 7 ga watan Oktoba lokacin da ta fara ƙaddamar da hari a Isra'ilar.

    Har yanzu akwai mutum 96 da ba a sako ba, amma Isra'ila ta ce ta yi amanna an kashe da dama cikin mutanen da aka yi garkuwar da su.

    Ba dai wannan ne karon farko da ake zaman tattaunawar tsagaita wuta tsakanin Hamas da Isra'ila ba cikin watanni 15 da suka kwashe suna yaƙi da juna, sai dai a lokuta da dama zaman baya ɗorewa.

  4. An sake zaɓar Mike Johnson a matsayin kakakin majalisar wakilan Amurka

    Mike Johnson

    Asalin hoton, Getty Images

    Kakakin Majalisar wakilan Amurka, Mike Johnson na jam'iyyar Republican ya sake samun nasarar ɗarewa kujerar mai matuƙar tasiri a siyasar ƙasar, bayan da majalisar ta zaɓe shi a yau Juma'a.

    Zaɓaɓɓen shugaban Amurka, Donald Trump ne ya nuna goyon bayansa ga Mr Johnson a matsayin wanda yake so ya zama kakakin majalisar.

    A ƙuri'ar farko da aka kaɗa Jonson bai samu nasara ba, bayan da wasu 'yan majalisa uku daga jam'iyyarsa sun ƙi zaɓarsa.

    Bayan zuwa zagaye a biyu na ƙuri'ar ne biyu daga cikinsu suka sauya matsaya inda suka kaɗa masa ƙuri'arsu.

  5. 'A yanzu duk mai fasfo ɗin Afirka zai iya shiga Ghana ba tare da bisa ba'

    Nana Akufo-Addo

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaba Nana Akufo-Addo na Ghana ya sanar da cewa daga yanzu duk wanda ya ke da fasfo ɗin Afirka ba ya buƙatar bisa shiga ƙasar.

    Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ya rage ƙasa da kwanaki uku ya miƙa mulki ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasar John Dramani Mahama a ranar Litinin mai zuwa.

    Tsarin dai na cikin shirin Afirka na kasuwanci maras shinge, kuma gabannin wannan ƙasasshe sama da 20 na Afirka suna buƙatar visa kafin shiga ƙasar ta Ghana.

    A shekarar 2019 Ghana ta ƙaddamar da shirin da ta yi wa laƙabi da 'The Year Of Return'.

    Hakan ya ja hankalin Amurkawa tsatson Afirka inda suka dinga zuwa domin zuba jari.

    A yanzu dai Ghana da Rwanda, da Seychelles da Gambia da Benin ne ke amfani da tsarin na kasuwanci maras shinge a nahiyar Afirka.

  6. An nemi shugaban riƙo na Koriya ta Kudu ya sa baki kan kama Yoon Suk Yeol

    Yoon Suk Yeol

    Asalin hoton, Getty Images

    Masu bincike kan yaki da cin hanci da rashawa a Koriya ta Kudu sun yi kira ga shugaban riƙo na ƙasar ya sanya baki, a ƙoƙarin kama shugaba Yoon Suk Yeol kan dokar soji da ya sanya da ba ta yi nasara ba.

    An dai tsige Mr Yoon daga shugabancin ƙasar amma har yanzu yana zaune a fadar shugaban ƙasa inda jami'an tsaro suka hana yunkurin kama shi.

    Dandazon waɗanda ke son a kama tsohon shugaban dai sun yi ta ihu a lokacin da jami'an tsaron suka hana shiga gidan;

    Masu binciken dai na son mukaddashin shugaban Koriya ta Kudu Choi Sang-mok ya bai wa jami'an tsaro umarnin miƙa Mr Yoon.

    Wannan danbarwa ta jefa Koriya ta Kudu cikin rikita-rikitar siyasa da jefa dimocradiyyar ƙasar cikin halin rashin tabbas.

  7. Ba zan ci gaba da zama a Liverpool ba - Salah

    Salah

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗan wasan Liverpool, Mohamed Salah ya ce babu wata alama da ke nuna tsawaita kwanginsa da ƙungiyar tasa, kuma da ''kamar wuya'' hakan ta kasance.

    Ɗan ƙasar Masar ɗin ya shiga wata shidan ƙarshe na kwantiraginsa, kuma a yanzu zai iya tattaunawa da ƙungiyoyin da ba na Ingila ba, kan makomarsa idan kwantiraginsa ta ƙare a wannan kaka.

    Mai 32 ya koma Liverpool daga Roma a 2017, kuma a wannan kaka ya zura ƙwallo 20 a duka wasannin da ya buga wa ƙungiyar a bana, lamarin da ya taimaka wa ƙungiyar ɗarewa teburin Premier da na Gasar Zakarun Turai.

    A yanzu ɗan wasan ne kan gaba a yawan zura ƙwallo a gasar Premier, inda ya ci 17, uku fiye da Erling Haaland na Man City.

    Da aka tambaye shi, ko yana tunanin wannan ce kakarsa ta ƙarshe a Anfield? sai ya amsa da cewa ''ya zuwa yanzu dai haka ne, saura wata shida''.

    "Babu alamun ci gaba da zamana a nan, da alama ba za mu daidaita ba, amma dai mu ɗan jira mu gani''.

    A baya-bayan nan Salah na yawan magana da kafafen yaɗa labarai game da makomarsa a Liverpool.

    A watan Satumbar shekarar da ta gabata ma, lokacin da Liverpool ta doke Manchester United, ɗan wasan ya ce ya buga wasan ne tamkar wasansa na ƙarshe a Old Trafford, sannan ya maimaita kalaman nasa a lokacin da suka doke Manchester City a watan da ya gabata.

    Shi ma kaftin ɗin ƙungiyar, Virgil van Dijk da Trent Alexander-Arnold kwantiraginsu za ta ƙare a ƙarshen wannan kaka.

    An dai yi ta alaƙanta Alexander-Arnold da komawa real Madrid.

  8. Gwamnatin Syria ta hana ƴan Lebanon shiga ƙasarta

    al-Sharaa

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Syria ta sanya sabuwar dokar hana 'yan Lebanon shiga ƙasar bayan tashin hankalin da ya faru a iyakar ƙasasshen biyu.

    Sojojin Lebanon sun ce wasu gungun Syria ɗauke da makamai sun buɗe musu wuta bayan sun yi amfani da buldoza a ƙoƙarin hana su buɗe iyakar ƙasar da ba ta hukuma ba.

    Tun bayan afkuwar lamarin a daren jiya Alhamis, ta ɗauki matakin hana 'yan Lebanon da ba su da shaidar zama a ƙasar shiga cikinta.

    A baya dai fasfon tafiye-tafiye da lokacinsa bai ƙare ba kawai 'yan Lebanon suke buƙatar nunawa idan za su shiga Syria, ta ƙasa.

  9. Fintiri ya naɗa sarakunan sabbin masarautun da ya ƙirkira

    Umaru Fintiri

    Asalin hoton, Umaru Fintiri/X

    Gwamnan jihar, Umaru Fintiri ya amince da naɗin sarakunan sabbin masarautu bakwai da aka ƙirƙira a jihar.

    Cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan, Humwashi Wonisikou ya fitar ranar Juma'a, ya ce naɗin sabbin sarakunan ya fara aiki ne nan take.

    Gwamna Fintiri ya ce an zaɓo sarakunan ne bisa cancanta da ficen da suke da shi a tsakanin al'umominsu.

    Haka kuma gwamnan ya umarce su da zama masu gaskiya da amana bisa ayyukan da aka ɗora musu.

    Sakarakunan da aka naɗa sun haɗa da:

    • Sani Ahmadu Ribadu a matsayin sarkin Fufore.
    • Alheri Nyako a matsayin Tol na Huba.
    • Farfesa Bulus Luka Gadiga a matsayin Mbemge na Michika
    • Ali Danburam a matayin Phil na Madagali.
    • Aggrey Ali a matsayin Kumu na Gombi.
    • Ahmadu Saibaru a matsayin sarkin Maiha.
    • John Dio a matsayin Gubo na Yungur.
  10. Mutum biyu sun cinna wa kansu wuta a Indiya

    iNDIA

    Asalin hoton, Getty Images

    Mutum biyu sun cinna wa kansu wuta a jihar Madhya Pradesh ta Indiya a lokacin gudanar da wata zanga-zanga kan zubar da ɗaruruwan tan na shara mai illa ga lafiya.

    Wani kamfani da ke haɗa magungunan kashe ƙwari ne mai suna Union Carbide ya zubar da sharar.

    Ma'aikatar ita ce wurin da aka samu tsiyayar sinadarai masu haɗari shekaru 40 da suka gabata wanda ya kashe dubban mutane.

    Hotuna da ake gani a shafukan sada zumunta na nuna mutanen biyu a garin Pithampur, inda a ka kai sharar, su na watsa wa kansu wani abu mai ruwa-ruwa kafin wuta ta kama su.

    Hukumomi sun ce tuni aka kai su asibiti.

    Alummomin da ke yankin sun nuna damuwar su kan illolin da kona sharar ke da shi ga lafiyarsu da kuma muhallinsu. jami'ai sunyi iƙirarin cewa za a yi shi lafiya.

  11. Shugaba Ferdinand Marcos na Philipines ya tsige mataimakiyarsa

    Philipphines

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaba Ferdinand Marcos na Philipines ya tsige mataimakiyarsa, Sara Duterte daga kwamitin tsaron ƙasar bayan fusatar da ta yi da furta cewa ta shirya yadda za ta hallaka shi.

    Wani babban jami'in gwamnati ya ce a yanzu, Misis Sara ba ta da iko ko tsoma baki kan harkokin kwamitin.

    A shekarar 2022 ne dai aka zaɓi 'yan siyasar biyu, amma dangantaka tsakaninsu ta yi tsami a bara, kan ikirarin da Mis Sara ta yi na ƙoƙarin kashe shugaba Marcos, da ta ce tuni har ta fara tuntubar wanda zai ma ta wannan aikin.

    Amma ta ce an yi wa kalamanta mummunar fahimta da juya mata zance.

  12. Somalia ta amince dakarun Habasha su shiga ƙasarta

    Ethiopia/Somalia

    Asalin hoton, Ethiopia Foreign Ministry

    Somalia ta ce a shirye take ta amince dakarun ƙasar Habasha shiga ƙasarta a wata sabuwar yarjejeniyar zaman lafiya ƙarƙashin ƙungiyar Tarayyar Afirka domin taimakawa ƙasa yaƙi da masu ikirarin jihadi na ƙungiyar, Al Shabab.

    Wannan ya biyo bayan ganawar da aka yi a jiya Alhamis tsakanin shugaba Hassan Sheikh Mahmood na Somalia da ministan tsaron Habasha a birnin Mogadishu.

    Dangantaka tsakanin ƙasashen biyu ta inganta a ɗan tsakanin nan, kan shirin Habasha na gida tashar ruwa a yankin Somaliland da ake taƙaddama a kai.

    Gwamnatin Mogadishu na ganin matakin keta hurumin ƙasarta ne.

  13. Jawabin Peter Obi cike yake da ɓata suna - APC

    Peter Obi

    Asalin hoton, X/Peter Obi

    Jami'iyar APC mai mulki a Najeriya ta kwatanta jawabin sabuwar shekara na tsohon ɗantakarar jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, a matsayin saƙon ɓata-suna.

    Cikin saƙon nasa ga ƴan Najeriya, Peter Obi ya soki Shugaba Bola Tinubu tare da nuna damuwa kan abin da ya kira ''cin hanci da rashin tafiyar da gwamnati yadda ya kamata da talauci da wahalhalu da kuma tarin bashin da ƙasar ke karɓowa''.

    Tsohon gwamnan jihar Anambra ya ce cin hanci da rashawa da kuma naɗa ƴan ƙabila guda a muƙamai sun yi katutu a cikin gwamnatin Tinubu.

    Ya kuma buƙaci tsare-tsare masu kyau daga gwamnatin domin kawo sauƙi ga ƴan Najeriya.

    A cikin wata takarda na martani da suka fitar, kakakin jamiyyar APC Felix Morka, ya ce matsayar Obi ta yi hannun riga da duk alamomin da ke nuna tattalin arziƙin ƙasar na farfaɗowa a dukkanin ɓangarori.

    Morka ya zargi Obi da wasu ƴan ƙungiyar adawa ta PDP da ƙoƙarin tunzura al'umma kan gwamnatin Tinubu.

    Sun kuma zargi Peter Obi da nuna kansa a matsayin ''mai yawan hasashen abubuwa marasa kyau, kuma wanda ya san komai'' bayan kuma ya gaza yin abubuwan a-zo-a-gani a lokacin da yake gwamnan jihar Anambra har na tsawon shekara takwas''.

  14. Kalli saƙon sabuwar shekara daga ma'aikatan BBC Hausa

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku kalli kalli bidiyo

    Shekara kwana, in ji Bahaushe!

    Ku kalli saƙon sabuwar shekara daga ma'aikatan BBC da ke Abuja, waɗanda ke aiki ba dare ba rana domin tattarowa, da tantancewa, da kuma tsarawa domin kuma kawo muku sahihan rahotannin da suka shafi rayuwarku.

  15. Ana zargin Lakurawa da kashe 'yansanda biyu a jihar Kebbi

    Wani ɗansandan Najeriya

    Asalin hoton, Reuters

    Wasu mahara da ake zargin mayaƙan ƙungiyar Lakurawa ne sun kai hari a garin Natisini a karamar hukumar Argungu da ke jihar Kebbi a arewa maso yammacin Najeriya.

    Bayanan da BBC ta tattara sun nuna cewa maharan ɗauke da makamai sun kashe akalla mutum uku, biyu daga cikinsu jami’an tsaro na ‘yansanda, a harin na ranar Alhamis da dare.

    Kazalika, sun sace shanu da dama, wanda ya jawo mutanen garin da dama suka tsere zuwa wasu wurare na daban.

    Wasu mazauna garin sun shaida wa BBC cewa da misalin ƙarfe 10:00 na dare suka fara harbe-harbe.

    Shugaban ƙaramar hukumar Argungu, Aliyu Sani Gulma, ya faɗa wa manema labarai ta wayar tarho cewa shanun da maharan suka sace sun kai aƙalla 200.

    Mai magana da yawun rundunar 'yansandan Kebbi, ASP Nasiru Abubakar, ya tabbatar wa BBC faruwar lamarin amma bai yi ƙarin bayani ba saboda yana kan hanyar zuwa wurin da abin ya faru a lokacin.

  16. Ministocin harkokin wajen Faransa da Jamus za su tattauna da sabuwar gwamnatin Syria

    Faransa da Jamus

    Asalin hoton, EPA

    Ministocin harkokin wajen Faransa da Jamus na ziyarar aiki a Syria domin ganawa da mahukuntan sabuwar gwamnatin 'yantawaye ƙarƙashin jagorancin Mohammed al-Sharaa, wanda aka fi sani da al-Jaolani.

    Bayan isarsu, Ministar Harkokin Wajen Jamus Annalena Baerbock, da takwaranta Nna Faransa Jean-Noel Barrot sun kai ziyara ƙasurgumin gidan yarin nan na Saydnaya.

    A gefe guda kuma, ƙasar Czech Republic ta sake buɗe ofishin jakadancinta a birnin Damascus na Syrian, wanda Amurka da sauran ƙasashen Turai ke amfani da shi tsawon shekaru.

    Kamar Amurka, ita ma ƙungiyar Tarayyar Turai ta saka wa Syria takunkumai lokacin mulkin Bashar al-Assad, kuma ana sa ran ɗage su na cikin abubuwan da za su tattauna.

  17. Ku San Malamanku tare da Sheikh Ali Isa Fezzan

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo

    An haifi Sheikh Ali Isa Fezzan a unguwar Fezzan da ke birnin Maiduguri kimamin shekara 52 da ta gabata.

    Ya fara karatu a makarantun allo kamar yadda aka saba a al'adance wajen karatun addinin Musulunci.

    Daga mahafinsa ya kai shi makarantar Ma'at da ke birnin Maiduguri domin samun karatun ilimi.

    Bayan nan ya zarce makarantar Higher Islamic da ke birnin Maiduguri a matsayin sakandire.

  18. Fursuna ya yi garkuwa da mutum biyar a gidan yarin Faransa

    Ɗansandan Faransa

    Asalin hoton, Reuters

    Rundunar 'yansanda a Faransa ta ce wani fursuna ya yi garkuwa da ma'aikata biyar a gidan yarin Arles da ke kudancin ƙasar.

    Mutumin riƙe da wuƙa, na tsare ne da ma'aikata lafiya huɗu da kuma gandiroba ɗaya.

    Rahotonni sun ce fursunan na zaman ɗaurin fyaɗe amma kuma yana da larurar ƙwaƙwalwa.

  19. Hankalin Alexander-Arnold na kan Liverpool 100 bisa 100 - Slot

    Trent Alexander-Arnold

    Asalin hoton, EPA

    Kocin Liverpool Arne Slot ya haƙiƙance cewa "hankalin Trent Alexander-Arnold yana kanm" baki ɗaya yayin da ake ta raɗe-raɗi game da makomar ɗanwasan.

    Kwantaragin ɗanwasan bayan na Ingila mai shiekara 26 zai ƙare a ƙarshen kakar wasa ta bana.

    Majiyoyi sun shaida wa BBC cewa Real Madrid ta fara tunkarar ɗanwasan amma dai ba ta miƙa wani tayi ba tukunna game da sayensa a watan nan na Janairu.

    Kafofin yaɗa labarai a Sifaniya sun ruwaito cewa Real na da niyyar sayensa a watan nan, amma Slot ya ce yana da ƙwarin gwiwar ba za a janye hankalinsa ba, har ma ya tabbatar cewa yana cikin tawagarsa da za su kara da Manchester City a ƙarshen makon nan.

    "Ina ganin yadda yake mayar da hankali a filin atasaye a kullum. Hankalinsa yana tare da mu kuma zai buga wasa ranar Lahadi," in ji kociyan yayin taron manema labarai.

  20. Jirgin sama ya kashe mutum biyu a Amurka bayan ya rikito

    Mutum biyu sun mutu wasu 19 kuma sun ji raunika ranar Alhamis lokacin da wani ƙaramin jirgin sama ya rikito kan rufin wata ma'aikatar ƙera kujeru a kudancin birnin California na Amurka.

    A cewar rundunar 'yansandan Fullerton, mutanen da suka mutu fasinjojin jirgin ne, yayin da waɗanda suka jikkata kuma ke cikin ginin a lokacin da lamarin ya faru.

    Ma'aikatan ceto sun kai mutum 11 asibiti, yayin da aka bai wa sauran mutum takwas kulawa a wurin.

    Jirgin ya rikito ne ƙasa da minti biyu kacal da tashinsa daga filin jirgi sama na Fullerton a lardin Orange, a cewar FlightAware wani shafin bin sawun jirage.