Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 03/02/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 3 ga watan Fabrairun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Isiyaku Muhammed, Aisha Babangida da Ahmad Bawage

  1. Congo ta zargi maharan M23 da kai mata harin jirage maraa matuƙa a filin jirgin Kisangani

    M23

    Asalin hoton, AFP

    Lardin Tshopo na Dimokuraɗiyyar Jamhuriyar Congo ya sanar da cewa jami'an tsaron ƙasar sun samu nasarar daƙile yuƙurin harin jirage marasa matuƙa a babban filin jirgin saman Bangoka da ke birnin Kisangani a ranar 1 ga watan Fabrailun da ta gabata, kamar yadda tashar rediyo ta Radio Top Congo FM ta ruwaito.

    Kakakin gwamnatin lardin ne ya sanar hakan, inda ya zargi mayaƙan M23 da ke samun goyon bayan Rwanda da ƙaddamar da harin, sannan ya ƙara da cewa maharan sun yi amfani da jirage marasa matuƙa.

    "Wannan zalunci ne da rashin hankali da Rwanda da ƙawayenta suke yi domin tayar da zaune tsaye a ƙasarmu. Muna godiya da yabo bisa ƙoƙari da jajircewar jami'an tsaronmu wajen daƙilewa tare da kakkaɓo jirage marasa matuƙa guda 8," in ji shi.

    Sai dai babu tabbaci ko harin ya yi sanadiyar mutuwar mutane ko yanayin asara da aka yi.

    Kisangani na yammacin biranen Nord da Sud Kivu, waɗanda M23 suka fi ƙarfi, kuma a baya mayaƙan sun yi barazanar kutsawa Kinsaha ta hanyar Kisangani.

  2. Ƴansandan Australia sun jinjina wa ɗan shekara 13 da ya yi ninƙayar kilomita huɗu domin ceto ƴanuwansa

    Ninƙaya

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar ƴansandan Australia ta jinjina wa wani yaro na ɗan shekara 13 bisa jarumtar da ya nuna na yin ninƙaya a ruwa na tsawon kilomita huɗu domin neman ɗauki bayan mahaifiyarsa da kuma ƴanuwansa biyu ruwa ya tafi da su.

    Yaron da sauran iyalansa nasa sun fita unguwa inda suka je wani yanki da ke yammacin ƙasar, inda ruwa ya tafi da su a can saboda iskar mai ƙarfin da aka yi.

    Wakiliyar BBC ta ruwaito daga kafar yaɗa labarai ta ABC cewa yaron ya yi ninƙaya ta tsawon sa'oi 2 sanye da rigar kariya daga nitsewar ruwa inda kuma daga bisani ya cire ta ya sake yin wata sa'a biyun yana ninƙayar a cikin ruwa .

    Ƴansanda sun ce ya nuna jarumta wajen ceto iyalansa.

  3. China ta fara samun tagomashi a zuba jari ɓangaren kwal

    China

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani sabon rahoto ya ce zuba jarin da China ta yi a bangaren kwal a shekarar da ta gabata ya samu tagomashi sosai duk da bukatar kasar na son komawa amfani da makamashin da baya gurbata muhalli.

    A kididdigar da aka yi ta nuna cewa a 2025, kasar ta samu riba sosai a bangaren kwal. Wakilin BBC ya ce adadin kwal din da China ta yi amfani da shi domin samar da hasken lantarki a bara ya gaza a cikin shekaru, to amma duk da haka ta kara zuba jari a bangaren kwal din.

    Bukatar komawa shuka bishiyo a China ta taso ne bayan raguwar da kasar ke samu a bangaren samar da hasken lantarki. break

  4. Za mu fara tattaunawa da Amurka kan shirinmu na nukiliya - Iran

    Iran

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya ce ya umarci ministan harkokin wajen ƙasar da ya fara tattaunawa da hukumomin ƙasar Amurka kan shirin ƙasar na nukiliya.

    Pezeshkian ya ce yana so ne a shiga tattaunawar domin lalubo hanyoyoyin da za a samar da maslaha ta ba cuta, ba cutarwa.

    Shugaban Amurka Donald Trump dai ya daɗe yana barazanar sake ƙaddamar da hare-hare a Iran, inda ya ce za su fi waɗanda ya yi a baya zafi matuƙar ba su yi watsi da shirinsu na nukiliya.

    Haka kuma ya zargi hukumomin ƙasar da jami'an tsaronta da amfani a ƙarfi wajen murƙushe masu zanga-zanga a ƙasar, lamarin da ƙasar ta musanta.

    Ana sa ran ministan harkokin wajen Iran Abbas Arapchi zai gana da wakilin Trump na musamman a yankin Gabas ta Tsakiya Steve Wikoff.

  5. Farawa

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Talata daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.