Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 02/10/2025.

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 02/10/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Abdullahi Bello

  1. An kashe mutane biyu a zanga-zangar matasa a Morocco

    Zanga-zanga a Morocco

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    Bayanan hoto, Masu zanga-zangar sun kona motoci ciki har da ta 'yansanda a Morocco

    'Yansanda sun bude wuta domin tarwatsa masu zanga-zanga da ke kokarin farwa wani caji ofis a Lqliaa a kusan da birnin Agadir mai tashar ruwa a kasar Morocco, lamarin da ya hallaka mutum biyu.

    Wannan ne karon farko da aka samu rasa rai tun bayan fara zanga-zangar da matan Gen-Z suka fara, kan matakin gwamnati na gina filin wasan kwallon kafa domin gasar cin kofin duniya ta shekarar 2030, maimakon inganta rayuwar yan kasa da magance tabarbarewar tattalin arziki.

    Masu zanga-zangar na cewa kasar na da filayen wasa da dama, amma babu wadatattun asibitoci. Wani mai zanga-zanga ya shaidawa BBC asibitin birninsu Oujda da ke iyakar kasar da Algeria ya lalace, ya fi kama da kurkuku maimakon asibiti.

    Masu zanga-zangar na zargin jami'an tsaro da ma'aikatan jinya a asibitocin gwamnati da karbar na goro a hannun marasa lafiya kafin su samu ganin likita.

    Ana dai gudnar da zanga-zangar a kowanne dare, inda 'yansandan Morocco ke cewa tilas su ke bude wuta a sama domin tarwatsa masu zanga-zangar. Ko a jiya Laraba 'yansandan sun bude wuta a sama domin kare kai lokacin da aka kai musu hari, kamar yadda kafar yada labaran birnin Lqliaa ta rawaito.

  2. MSF ta yi allawadai da kisan jami'inta a Gaza

    Kungiyar agaji ta MSF, ta yi Allah-wadai da kisan ɗaya daga cikin ma’aikatanta a harin da Isra’ila ta kai Gaza. MSF ta ce wasu ma’aikatan lafiya huɗu sun jikkata a harin, ciki har da wani likitan ƙashi da kuma masu gashi.

    Harin ya auku ne a lokacin da suke jiran wata bas ɗon zuwa asibitin da suke aiki a Deirul Balah, dake tsakiyar Gaza. Kungiyar ta ce dukkansu suna sanye da rigunan Kungiyar agaji ta MSF.

    Jami'in da aka kashe mai suna Omar Hayek mai shekara arba’in da biyu da haihuwa, ya kasance jami'in kula da marasa lafiya ne.

    Shi ne mutum na goma sha huɗu daga cikin ma’aikatan MSF da aka kashe a Gaza tun daga ranar 7 ga watan Oktoba, shekara ta 2023.

  3. Kungiyoyin sa ido kan rashawa sun zargi Wike da boye kadarori

    .

    Asalin hoton, BBC PIDGIN

    Bayanan hoto, Wike

    Gamayyar ƙungiyoyin da ke sa ido kan shugabanci na gari da cin hanci da rashawa, sun yi kiran a gaggauta gudanar da bincike kan ministan babban birnin Tarayya Abuja Nyesom Wike, kan zarge-zargen boye kadarorinsa da kin bayyana su wanda hakan ya saba wa dokokin Najeriya.

    A cikin sanarwar hadin gwiwa da suka fitar, sun yi kira ga hukumomin binciken cin hanci da rashawa da suka hada da EFCC da ICPC da CCB da NJC da hukumar haraji ta FIRS su dauki matakin gaggawa kan Wike.

    Sanarwar ta ci gaba da cewa babu wani jami'in gwamnati komai mukaminsa da ya fi karfin hukuma, sun ce hakan na janyo ƙimar Najeriya na raguwa a idon duniya.

    Sun kara da cewa, akwai kwarararn rahotanni da ke alakanta ministan da maidakin shi Mai shari'a Eberechi Suzzette Nyesom-Wike ta kotun daukaka kara da tarin kadarorin da ba su bayyana kamar yadda doka ta tanada ga duk mai rike da madafun iko.

    Ciki har da manyan dogayen gine-gine masu daraja har 3 a jihar Florida ta Amurka da aka siya a shekarar 2021 zuwa 2023, ana kuma zargin sun sayawa 'ya'yansu ne.

    Harwayau, da wasu gidajen alfarma da manyan motoci da suka mallaka amma da sunan wasu 'yan uwansu a Abuja. Gamayyar kungiyoyin sun kuma yi wani zargin na karkatar da dala miliyan 300 na gyara muhalli a Ogoni da malalar mai ya lalata da suma aka karkatar ga kamfanoni masu zaman kan su.

  4. Ana zargin 'yan ta'adda da sace dansanda a jihar Kwara

  5. 'Yanbindiga sun sace Liman da kansiloli a jihar Zamfara

    'Yansandan Najeriya

    Asalin hoton, NPF.GOV.NG

    Bayanan hoto, 'Yansanda a bakin aiki

    Wasu 'Yanbindiga sun sace kansiloli biyu da limamin wani masallaci a garin Tsauni da ke birnin Gusau na jihar Zamfara a arewacin Najeriya.

    Kansilolin na wakiltar mazabun Gidan Goga da Tsibiri a karamar hukumar Maradun, an sace su da misalin karfe 8 na daren ranar Laraba a kusa da ofishin 'yan sanda da ke yankin jim kadan bayan kammala sallar Magariba.

    Shugaban karamar hukumar Maradun Honarabul Sanusi Gama Giwa, ya tabbatarwa da jaridar Daily Trust faruwar lamarin da ta ce dykkansu 'yan mazabar shi ne.

    Giwa ya ce mutanen na hutawa a wurin wani mai saida shayi, lokacin da 'yanbindigar suka far musu, tare da kwace wayoyin 'yansandan da ke wurin da awon gaba da mutum 6, amma daga bisani sun sako uku tare da gaba da Limam da kansilolin biyu..

    Rahotanni sun ce sun zo neman wani mutumin karamar hukumar Kaura amma da ba su gan shi ba sukai awon gaba da mutanen da ke wurin mai shayin.

  6. Ana neman mai yawon bude ido da ta bace a Afurka ta Kudu

    'Yan sanda a Afurka ta Kudu na ci gaba da neman wata mai yawon bude ido 'yar Birtaniya da ta bata tun ranar Lahadin karshen mako, lokacin da suka je hawan tsauni tare da mijinta.

    'Yansanda na amfani da jirage masu saukar ungulu a neman matar mai suna Elaine McSorley 'yar shekara 71, wadda aka yi wa ganin karshe a kusa da garin Mkuze a yankin KwaZulu Natal.

    Kamar yadda ma'aikatan Otal din da Elaine McSorley ta sauka suka bayyana, sun ce ma'auratan sun yi tattaki a harabar otal din a ranar Lahadi. Da misalin karfe 3 na rana mijinta mai shekara 81 ya dawo Otal din, bayan gajiya da tafiyar da ya yi, amma da ya ga har yamma ba ta dawo ba sai ya shaidawa ma'aikatan otal din. Daga nan aka aike wata tawaga ta fara neman ta. Sai dai 'yansanda sun ce tun daga ranar mijin Mrs McSorley ya tattara ya bar otal din kuma har yanzu ba a san inda ya ke ba.

    Mai magana da yawun ofishin harkokin wajen Birtaniya ya shaidawa BBC, su na bai wa iyalan matar taimakon da ya dace, su na kuma tattaunawa da hukumomin Afurka ta Kudun kan nemanta.

  7. Ghana ta fara shirin ƙaddamar da allurar rigakafin cutar HIV kafin 2026,

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ghana ta fara shirin kaddamar da allurar rigakafin cutar HIV kafin shekarar 2026, a wani mataki na rage yaɗuwar cutar a ƙasar.

    Hukumar AIDS ta Ghana ta bayyana cewa ƙasar ta samu sabbin masu ɗauke da cutar sama da 15,000 a shekarar 2024 kaɗai.

    Masana lafiya na ganin gabatar da rigakafin zai zama babban sauyi wajen rage yaɗuwar cutar, musamman a cikin waɗanda ke cikin haɗarin kamuwa da cutar.

    Shugaban Hukumar, Dr. Prosper Akanbong, ya ce tuni aka fara tattaunawa da kamfanonin magunguna da don tabbatar da shirin ya gudana yadda ya kamata.

    Ya ƙara da cewa rigakafin zai zama ginshiƙi a shirin rigakafin HIV na ƙasar, inda da farko za a shigo da magungunan daga ƙasashen waje, daga bisani kuma a ƙara ƙarfin masana’antar magunguna a cikin gida.

    Kididdiga daga Hukumar AIDS ta Ghana da UNAIDS sun nuna cewa a shekarar 2023 akwai kusan mutum 354,000 da ke rayuwa da cutar HIV a ƙasar, mafi yawansu mata da matasa, duk da ci gaban da aka samu wajen samar da magungunan ARV.

    A halin yanzu, ana amfani da ƙwayoyin rigakafi ta hanyar shan ƙwaya kullum ko allura duk bayan makonni takwas don rage yiwuwar kamuwa da cutar.

  8. Gwamna Fubara ya kori kwamishinoni da jami’an gwamnatin Rivers

    ...

    Asalin hoton, Rivers state Government House Media

    A wani gagarumin sauyi na baya-baya a jihar Ribas, gwamna Siminalayi Fubara ya kori dukkan kwamishinoni da sauran jami’an gwamnati da hukuncin kotun ƙoli ya shafa a baya.

    Wannan sanarwa ta fito ne yayin wani zama da aka yi a gidan gwamnati da ke Fatakwal a ranar Laraba.

    Hukuncin Kotun Koli ya soke naɗin kwamishinoni da sauran jami’an gwamnatin Fubara saboda rashin bin ƙa’ida daga bangaren tsohon jagoran majalisar dokokin jihar Ribas, Victor Oko-Jumbo.

    Kotun ta amince da tsagin majalisar mai wakilai 27 ƙarkashin jagorancin kakakin majalisar, Martins Amaewhule, a matsayin halatacce.

    Wannan korar ta shafi Babban Lauyan Ribas da kwamishinan Shari’a, inda ake ganin akwai wahalar su sake komawa kan kujerun su saboda yanayin siyasar jihar mai arzikin man fetur.

    Sanarwar gwamna Fubara ta jaddada cewa duk da korar, zai ci gaba da gudanar da ayyukan ci gaban jihar tare da kawo sabon salo.

    Ya godewa mambobin majalisar da suka bayar da gudunmawa a cikin shekaru biyu da suka gabata, sannan ya bukaci daukacin ‘yan Najeriya da su hada kai da shugaban kasa Bola Tinubu wajen gina kasa mai zaman lafiya da tsaro da wadata.

    Ana dai zargin cewa korar kwamishinonin da mukarrabansa ta ba da damar shigar da masu biyayya ga tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, cikin majalisar.

    Masu lura da siyasar jihar na ganin wannan sauyi a matsayin wani gagarumin ƙalubale ga gwamna Fubara, musamman ganin rikicin siyasar da aka daɗe ana yi tsakanin shi da Wike.

    Fubara ya dawo kan kujerar mulki a matsayin gwamna a ranar 18 ga watan Satumbar bana, bayan cikar wa’adin watannin shida da shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya kakaba dokar ta-ɓaci a jihar.

    Wannan sauyi da ya shafi kwamishinoni da sauran jami’an gwamnati yana daga cikin matakan da Gwamna Fubara ke dauka don tabbatar da ci gaban jihar.

  9. Babu inda na ce zan janye wa wani takarata - Atiku

    ...

    Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya musanta rahotannin da ke cewa zai janye wa wani takararsa a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa.

    Wannan na zuwa ne bayan wata hira da Atiku yayi da BBC Hausa a ranar Laraba, 1 ga watan Oktoban 2025, ranar da Najeriya ke bikin cika shekara 65 da samun ƴancin kai kenan.

    A cikin wata sanarwa da mai bai wa Atiku shawara da yaɗa labarai, Paul Ibe ya fitar, ya ce "An sami ruɗani daga wasu kafafen yaɗa labarai kan fassarar hirar da Atiku ya yi da BBC Hausa."

    "Ya ce bayan an yi nazari kan bidiyo da rubutaccen hirar, babu inda ya ce zai janye wa kowa takararsa.

    Sanarwar ta kara da cewa abin da Atiku ya bayyana a fili shi ne matasa da sauran masu sha’awar takara suna da damar shiga zaɓen fitar da gwani.

    Ya kuma ce "Idan matashi ya fito ya ci nasara a zaɓen fitar da gwani, shi zai goyi bayan wannan ɗan takaran ba tare da wata matsala ba.

    Sanarwar ta ƙara da cewa duk wani jita-jita da ke cewa Atiku zai janye daga takara don wani ba gaskiya ba ne, kuma bai yi daidai da abin da ya faɗa a hirar da ya yi da BBC Hausa ba.

  10. Ƴansanda sun kori mutanen da suka yi yunƙuri kafa ƙasa a Scotland

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƴan sanda a Scotland sun kori wasu mutum uku da ke yunƙurin kafa ƙasa a dajin Scottish Borders suna iƙirarin cewa su ƴan ƙabilar Afrika ne inda suke kira kansu da “Ƴan ƙasar Kubula”.

    An ce mutanen sun kafa sansan ne a filin gwamnati kusa da Jedburgh, duk da cewa an ba su takardar gargaɗi sau biyu da su fice daga wurin.

    Waɗanda aka kora sun haɗa da Kofi Offeh daga Ghana, Jean Gasho daga Zimbabwe, da kuma Kaura Taylor daga Texas, Amurka.

    Sun bayyana cewa suna neman dawo da filayen da aka ƙwace daga kakanninsu shekaru 400 da suka wuce.

    Lamarin ya jawo hankalin kafafen yada labarai, inda mutanen suka tara mabiya fiye da 100,000 a kafafen sada zumunta.

    Mazauna yankin sun bayyana farin ciki bayan korarsu, bayan wahalhalun da suka sha wajen ganin sun bar wurin.

  11. Me doka ta ce kan halascin takarar Jonathan bayan shan ranstuwa sau biyu?

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen 2027 a Najeriya, wata sabuwar muhawara ta ɓarke a ƙasar kan halascin takarar tsohon shugaban ƙasar Goodluck Jonathan.

    A ƙarƙashin dokokin Najeriya dai sau biyu ne kawai aka yarje wa mutum ya riƙe muƙamin shugaban ƙasar.

    Kan haka ne wasu ke ganin tsohon shugaban ƙasar ba shi da hurumin tsayawa takara saboda ya sha rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban ƙasa har sau biyu.

    To sai dai magoya bayansa na cewa abin da dokokin Najeriyar ke nufi shi ne a zaɓi mutum sau biyu, ba rantsuwa ba.

    Wannan batu dai ya haifar da zazzafar muhawara a ƙasar, musamman tsakanin ƴansiyasa da ma wasu masana shari'a.

  12. Kotu ta kori ƙarar da aka kai Tinubu kan sanya dokar ta-ɓaci a Rivers

    ...

    Asalin hoton, Facebook/Bola Tinubu

    Kotun Babban Birnin Tarayya, Abuja, karkashin jagorancin alƙali James Omotosho ta kori ƙarar da Belema Briggs da wasu huɗu suka shigar, wacce ta ƙalubalanci sanarwar Dokar Ta-ɓaci da Shugaba Bola Tinubu ya ayyana a Jihar Rivers.

    Ƙarar ta nemi kotu ta tantance halaccin ayyanawar dokar-ta-ɓacin da Shugaba Tinubu ya yi, amma alƙalin ya bayyana cewa masu ƙarar ba su da ikon shigar da ƙara, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

    Babu ɗaya daga cikin masu ƙarar da ya ce shi memba ne na kwamitin zartarwa na Jihar ko Majalisar Dokoki.

    Kotun ta kuma lura cewa babu ɗaya daga cikin masu ƙarar da ya samu amincewar babban lauyan jihar kafin shigar da ƙarar.

    Ya ƙara da cewa a ƙotun ƙloli ne kawai za a iya shigar da irin wannan ƙarar.

    Kotun ta kuma ce ƙarar ba ta da tushe inda ta lura cewa masu ƙarar basu nemi amincewar ‘yan jihar Rivers ba kafin su shigar da ƙarar.

    Shugaba Tinubu ya ayyana dokar-ta-ɓaci a Jihar Rivers ne a watan Maris bayan dakatar da gwamnan jihar, Siminalaye Fubara da mataimakinsa, da dukkan ‘yan majalisar jihar.

  13. Tanzania ta yi watsi da rahoton Human Rights Watch

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Tanzania ta yi watsi da wani rahoto da ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Human Rights Watch ta fitar kan halin dimokuradiyya a kasar, inda ta bayyana rahoton a matsayin iƙirarin da ba shi da tushe, wanda aka yi don ɓata sunan ƙasar a idon duniya.

    A makon da ya gabata ne ƙungiyar ta zargi gwamnati da ƙara matakan takura wa ‘yan adawa.

    Human Rights Watch ta bayyana cewa wannan dabi’a na tayar da “babban damuwa” yayin da ake shirin gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a karshen wannan watan.

    “Ya kamata hukumomin Tanzania su ɗauki matakai nan da nan don kare sahihancin zaɓen Oktoba, wanda yake cikin babban hatsari a halin yanzu,” in ji mai bincike a Afirka, Nomathamsanqa Masiko-Mpaka.

    A martanin da gwamnatin ƙasar mai ci ta yi yau da safe, ta ce “Gwamnati na son jaddada kudurinta na karewa da bunƙasa haƙƙin bil’adama kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin Jamhuriyar Tarayyar Tanzania da kuma yarjejeniyoyin kasa da kasa da na yankin da Tanzania ta rattaɓa hannu suka tanada,”

    Yayin da yaƙin neman zaɓe ke ƙara samun karfi, inda jam’iyyar gwamnati ke zagayawa ƙasar don tallata ‘yan takararta a manyan tarurruka, an hana manyan jam’iyyun adawa guda biyu shiga zabe.

    An kuma ware babbar jam’iyyar adawa, Chadema daga zaɓen, yayin da wanda ake ganin zai tsaya takarar shugaban ƙasa daga jam’iyyar ke cikin gidan yari yana fuskantar zargin cin amanar kasa.

  14. Elon Musk ya zama attajiri na farko da ya mallaki kusan dala biliyan 500

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Elon Musk ya zama attajiri na farko da ya mallaki dala biliyan 500, yayin da darajar kamfanin ƙera motocinsa na Tesla da sauran harkokinsa suka tashi a wannan shekarar.

    Kadarorin Musk sun kai dala biliyan 500.1 a ranar Laraba a New York, kafin ya ɗan sauka zuwa kimanin dala biliyan 499 a baya-bayan nan, kamar yadda Forbes ta ruwaito.

    Baya ga Tesla, darajar wasu kamfanoninsa kamar xAI da SpaceX ma sun ƙaru a ‘yan watannin nan.

    Wannan nasara ta ƙara tabbatar da matsayin Musk a matsayin mutum mafi arziki a duniya idan aka kwatanta da sauran manyan masu fasaha na duniya.

    A cewar Forbes, wanda ya biyo bayan Musk shi ne wanda me kamfanin fasaha na Oracle, Larry Ellison, da dukiyarsa ta kai dala biliyan 350.7.

    Dukiyar Musk mafi yawa ta samo asali ne daga kashi sama da 12 na hannun jarinsa a Tesla, wanda hannun jarinsa ya karu sosai a wannan shekarar.

  15. Ana fargabar gomman ɗalibai sun mutu bayan ruftawar makaranta a Indonesia

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomi a Indonesiya sun ce ƙasar na fargabar gomman ɗalibai sun mutu bayan ruftawar wata makaranta mai hawa biyu a garin Sidoarjo na ƙasar.

    Masu ceto sun ce ba a samu wani alamar mai rai ba a karkashin ginin makarantar Islamiyya inda har yanzu an kasa gano mutum 59.

    Ɗaruruwan ɗalibai, mafi yawan su samari ne, suna cikin makarantar lokacin da ta rufta ranar Litinin.

    Aƙalla ɗalibai biyar sun mutu, kusan 100 kuma suka jikkata, in ji hukumomin.

    Tun daga fara ayyukan ceto, mutum 13 ne aka samu cetowa daga ƙarƙashin ginin, amma daga bisani biyu daga cikinsu sun mutu a asibiti.

    Ana fuskantar ƙalubale wajen ceto saboda rashin daidaton ginin.

    A ranar Alhamis, hukumar kula da bala’o’i ta BNBP ta ce jirage marasa matuƙa da aka yi amfani da su bai nuna alamun akwai masu rai a ƙarkashin ginin ba in ji, shugaban BNBP a taron manema labarai.

  16. Uganda ta musanta tsare masu fafutuka biyu daga Kenya

    ...

    Asalin hoton, Bobi Wine/X

    Hukumomin Uganda sun musanta tsare wasu masu fafutuka biyu daga Kenya da aka yi zargin an yi garkuwa da su a jiya Laraba a babban birnin Kampala.

    Shugaban adawa na kasar, Bobi Wine ya bayyana a shafinsa na X cewa wasu jami'an tsaro ɗauke da makamai ne ne suka yi garkuwa da mutanen biyu da suka haɗa da Bob Nyagi da Nicholas Ayoo aka kuma kai su wani wurin da ba a sani ba.

    Sai dai kakakin ’yan sandan Uganda, Kituma Rusoke, ya shaida wa BBC cewa mutanen biyu ba sa hannun ’yan sanda.

    Lokacin da BBC ta tuntubi kakakin sojojin ƙasar, Felix Kulayigye, ya ce ba zai iya magana ba kan batun, domin yana da nasaba da zargin jami’an tsaro da ba sa sanye da kayan soja.

    Ya kuma kalubalanci Bobi Wine da ya tabbatar da zargin garkuwar da kuma hukumar tsaro wacce ta aikata hakan.

  17. Shettima ya koma Najeriya bayan kammala babban taron MDD

    Kashim Shettima

    Asalin hoton, Fadar shugaban Najeriya

    Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya koma Najeriya bayan kammala babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 da aka gudanar a birnin New York tare da wasu muhimman tattaunawa a ƙasar Jamus.

    A yayin zaman mako guda na hulɗar ƙasashen duniya, Shettima ya gabatar da jawabin ƙasa na Shugaba Bola Tinubu inda ya yi kira ga cikakkun sauye-sauye a Majalisar Ɗinkin Duniya.

    Haka kuma, ya jagoranci kare ikon Afirka kan albarkatun ma’adananta da aka ƙiyasta darajarsu a dala biliyan 700 tare da ƙarfafa hulɗa ta dabarun cigaba da Birtaniya da Gidauniyar Gates, da sauran manyan masu ruwa da tsaki a duniya.

    Daga bisani, Shettima ya gana da shugaban Majalisar Ɗinkin Duniya, António Guterres, wanda ya yaba da yunƙurin Najeriya na neman kujerar dindindin a kwamitin tsaro na Majalisar.

    A wani zama ta daban kuma, Shettima ya gabatar da damar zuba jari a fannin sauyin makamashin Najeriya da darajarsa ta kai dala biliyan 200 ga manyan masu zuba jari na duniya.

    Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma tabbatar wa al’ummar Najeriya mazauna ƙasashen waje cewa gwamnatin Tinubu za ta ci gaba da gana da su a harkokin gudanarwarta kafin ya wuce Jamus don kammala wasu muhimman hulɗoɗi.

  18. Adadin waɗanda suka mutu a hatsarin jirgi a Kogi ya kai 36

    ...

    Asalin hoton, National Emergency Management Agency, Nigeria, via REUTERS

    Hukumomi a jihar Kogi da ke arewa maso tsakiyar Najeriya sun tabbatar da cewa adadin waɗanda suka mutu a hatsarin jirgin ruwa da ya auku a jihar Kogi ya haura zuwa mutum 36

    A jiya ne dai hukumomin suka ce suna ci gaba da gudanar da aikin ceto bayan da kwale kwale ya kife a ƙaramar hukumar Ibaji da ke jihar.

    Kwale kwalen ya kife ne da wasu mutane da ke kan hanyarsu ta zuwa wata kasuwa a jihar Edo da ke makwaftaka da su.

    Hukumomin jihar sun ce an ceto mutum 40 daga cikin kwale-kwalen da ya nutse a bakin kogin da ke kusa da ƙauyukan Akpu da Odumomo.

    Yawancin fasinjojin sun haɗa da yara da mata da kuma wasu da suka je jana’iza a garin, inda suke kan hanyarsu ta dawowa Ilushi.

    Hukumomin sun ƙara da cewa aikin ceto yana ci gaba.

    Gwamna Ahmed Usman Ododo ya bayyana alhinin sa kan hatsarin, inda ya umurci hukumomi da su gaggauta aikin ceto.

  19. Shugaban Colombia zai kori jakadun Isra’ila daga ƙasar

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Colombia Gustavo Petro ya ce zai kori dukkanin jami'an diflomasiyar Isra'ila daga ƙasarsa a matsayin martani ga kama jiragen ruwa masu ɗauke da agaji zuwa Gaza.

    Ya kuma ya bayyana cewa an yi garkuwa da yan Colombia guda biyu.

    Petro babban mai caccakar yaƙin Isra'ila a Gaza, ya zargi Isra'ila da sake saɓa dokokin ƙasa da kasa inda ya buƙaci sakin su cikin gaggawa.

    Italiya ta kira kutsen jiragen ruwan da Isra'ila ta yi a matsayin fashin teku da kuma ta'addanci.

    An dai yi ƙokarin shigar da kayan agaji ne ta hanyar teku domin kaucewa shingen Isra'ila a yankin

  20. Sojojin Isra’ila sun kama jiragen ruwa da ke ƙoƙarin kai agaji Gaza

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Jiragen ruwa na sojin Isra'ila sun tare wasu jiragen ruwa na ƙasa da ƙasa da ke kokarin kai kayan agaji zuwa Gaza tare da kama masu fafutuka da ke cikin jirgin.

    Wani hoton bidiyo da ma'aikatar harakokin wajen Isra'ila ta wallafa ya nuna wata babbar mai mafufutika Greta Thunberg a zaune a kan saman daya daga cikin jiragen ruwan yayin da wani sojan ƙasar ke magana da ita.

    Ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila ta ce an dakatar da jiragen ruwan da dama kuma an tafi da wadanda ke ciki zuwa tashar jiragen ruwa ta Isra'ila.