Ƙungiyar M23 ta ce ta ƙwace birnin Uvira daga hannu sojojin DR Congo
Asalin hoton, Getty Images
'Yan tawayen ƙungiyar M23 a gabashin DR Congo sun ce a yanzu su ke da cikakken iko da birnin Uvira - wanda ya kasance gari na ƙarshe da ke hannun gwamnati a lardin Kivu ta Kudu.
A wata sanarwa da suka fitar 'yan tawayen da Rwanda ke mara wa baya sun yi kira ga sauran sojojin Kongo da su miƙa wuya.
Jami'an yankin sun tabbatar da kasancewar mayaƙan ƙungiyar a hedikwatar gwamnan lardin da kuma babban ɗakin taro na birnin.
'Yar tazara kaɗan ce ta 'yan kilomita daga Birnin na Uvira zuwa makwabciyar ƙasar, Burundi, inda dubban farar hula suka tsere zuwa can.
A yanzu dai ƙungiyar 'yan tawayen ta M23 ta rufe iyakar.
'Yan tawayen sun ƙwace birnin ne ƙasa da mako ɗaya bayan da Amurka ta jagoranci ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Kongo da Rwanda.
Ministan harkokin waje na Burundi, ya bayyana kama birnin a matsayin kunya ta Shugaba Trump.
'Ba za mu taɓa yafe wa waɗanda suka kashe ƴan Shi'a ba a Zaria'
Shekara goma kenan tun bayan kisan da jami’an sojin Najeriya suka yi wa mabiya mazhabar Shi’a a garin Zaria na jihar Kaduna.
A wancan lokaci an yi amanna ɗaruruwan mutane ne suka mutu, da dama kuma suka jikkata, bayan zargin rundunar soji cewa mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky sun tare musu hanya.
Lamarin ya haddasa suka daga kungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam na duniya, waɗanda suka zargi sojoji da amfani da ƙarfi fiye da kima.
Shugaban dandalin tattauna al’amura naƙkungiyar mabiya Shi’a ta IMN a Najeriya, Farfesa Abdullahi Danladi, ya ce duk da wucewar shekaru goma tun bayan faruwar wannan mummunan lamari, har yanzu ba za su taɓa yafe wa waɗanda suka aikata wannan mummunan aikin ba.
A tattaunawarsa da BBC, Farfesan ya ce raɗadin abin da ya faru na ci gaba da sosa zuƙatan al’ummar Shi’a, musamman ganin cewa babu wani bangare na gwamnati da ya ɗauki matakin hukunta masu laifi.
Ya ce, “Shekara 10 kenan da kashe mutanenmu, kuma har yanzu babu wanda aka kama. Gwamnati ta yi shiru, kwamitin da aka kafa don bincike ma bai fito da wani sakamako ba, balle a hukunta masu laifi.”
Farfesa Danladi ya ce abin da ya faru ya wuce abin da za a yi gum a kai, domin an kashe mutane ba tare da an ga adalci ba.
“Ba yadda za a ce an taru an kashe mutane, amma babu wanda ya fuskanci hukunci. Dole ne a dauki mataki domin hukunta wadanda suka aikata wannan ta’asa,” in ji shi.
Ya kara da cewa akwai bayanai da ke nuni da cewa ana kokarin dakile wannan batu daga fitowa fili.
A cewarsa, “Akwai bayanan da ke nuna cewa ana kokarin rufe maganar. Amma irin wannan shari’a tana iya daukar lokaci ko tsawon shekaru, amma wata rana gaskiya za ta bayyana, ko da kuwa ba mu da rai. Tarihi ba zai manta da wannan mummunan aiki ba.”
Farfesan ya ce tunawa da lamarin bayan shekaru goma na kara tabbatar da matsayin su na rashin yafiya da neman adalci".
“Idan irin wannan lokaci ya zo — musamman yanzu da yake shekara 10 dole ne zuciya ta sosa. Za mu taru mu fadakar da juna, mu kuma jaddada cewa ba za mu taɓa yafe wa ba, kuma muna jiran ranar da za a mana adalci a wannan duniya,” in ji shi.
Na fice daga PDP ne don kare kaina – Adeleke
Asalin hoton, Adeleke/Twitter
Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya kare matakin da ya ɗauka na ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar AP, yana mai cewa ya sauya sheƙa ne domin kare kansa da kuma tabbatar da zaman lafiyar jihar.
Adeleke, yayin da yake magana a gidan talabijin na Channels a ranar Laraba, ya ce bai yi watsi da PDP ba, wacce har yanzu yake girmamawa, sai dai ya zaɓi fifita ɗorewar ci gaban da ake samu a Osun.
Ya ce:“Ba gaskiya ba ne cewa na yi watsi da PDP. Ina son PDP, amma dole ne in kare kaina.
Dole ne in tabbatar na kare jihata saboda kyawawan ayyukan da muke yi domin mu ci gaba.”
Adeleke ya shiga jam’iyyar AP ne a ranar Talata bayan ya fice daga PDP, jam’iyyar da ta kai shi mulki a zaɓen gwamnan jihar na 2022.
A ranar Laraba ne ya samu tikitin takarar gwamna a karkashin sabon jam’iyyarsa ta AP.
Yanzu haka zai kara da ‘yan takara daga APC, PDP, da kuma jam'iyyar hɗaka ta ADP a wani zabe da ake sa ran zai kasance mai matukar tasiri ga makomar siyasar sa.
Dangane da damuwar cewa takara a karkashin jam’iyya mara karfi na iya rage masa kuri’u a zaben 2026, Adeleke ya nuna kwarin gwiwa, yana mai cewa ayyukan da ya gudanar a mulkinsa za su samar masa wa’adin mulki na biyu.
Najeriya ta ƙulla yarjejeniyar tsaro da Saudiyya, wane alfanu za ta samu?
Asalin hoton, others
Masana harkokin alaƙa tsakanin ƙasashe sun bayyana yarjejeniyar ƙawancen tsaro da Najeriya ta ƙulla da Saudiyya a matsayin mai muhimmanci, kodayake suna cewa ba zai yiwu Najeriya ta dogara da ita ba wajen shawo kan matsalolin tsaron da take fama da su.
A ranar Laraba ne ƙasashen biyu suka saka hannu kan yarjejeniyar domin ƙarfafa haɗin gwiwa a fannin tsaro da ayyukan soja tsakaninsu.
Wata sanarwa daga Ma'aikatar Yaɗa Labarai ta Najeriya ta ce Ƙaramin Ministan Tsaro Bello Matawalle ne ya wakilci Najeriya, yayin da Mataimakin Ministan Tsaro Dr. Khaled H. Al-Biyari ya wakilci Saudiyya.
Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Alhamis daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu ci gaba daga inda muka tsaya a jiya na Talatan kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa a cikin Najeriya da sauran sassan duniya.
Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo da tafka muhawara.