MDD ta gargadi ƙasashen Afirka kan fuskantar haraji bayan ƙarewar AGOA

Asalin hoton, Getty Images
Taron Majalisar Dinkin Duniya kan kasuwanci da cigaba, UNCTAD, ta yi gargaɗi cewa ƙasashen Afirka na fuskantar barazanar ƙarin haraji da rage damar shiga kasuwannin Amurka, bayan ƙarewar yarjejeniyar bunƙasawa da bai wa ƙasashen afrka dama ta AGOA a yau Talata.
Shirin AGOA, wanda aka shafe tsawon shekaru 25 ana amfani da shi, ya bai wa ƙasashen Afirka kusan 30 damar fitar da kayayyaki zuwa Amurka ba tare da biyan haraji ba.
Sai dai yanzu, yayin da Amurka ke nazarin yiwuwar tsawaita yarjejeniyar, dubban ‘yan Afirka na fuskantar barazanar rasa ayyukansu, musamman ma a masana’antar kayan ɗinki da tufafi.
Shirin AGOA dai an fara shi a majalisar dokokin Amurka ne a shekarar 2000, domin ƙarfafa ciniki da jari tsakanin Amurka da ƙasashen Afirka.
An sabunta shi a shekarar 2015, inda aka ƙara masa shekaru goma.
Yanzu kuwa, kamfanoni da dama a nahiyar sun shiga halin rashin tabbas kan makomar tattalin arzikinsu.



