Labarin wasanni daga 22 zuwa 27 ga watan Fabrairu 2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Lahadi 22 zuwa 27 ga Fabrairu 2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Yanzu ake buga Premier League - Guardiola, Premier League

    Guardiola

    Asalin hoton, Getty Images

    Pep Guardiola ya ce yanzu ne aka fara buga Premier League ya kuma ce yana sa ran za a ga karin abubuwan da za suke ɗaukar hankali a kokarin lashe kofin bana, ya jaddada cewa Manchester City ba za ta mika wuya ba wajen ci gaba da kalubalantar Arsenal ba.

    Ƙungiyar da Guardiola ke jan ragama ta ci gaba da matsawa Arsenal lamba wajen maye gurbinta a kan teburin kakar bana.

    Ranar Asabar City ta doke Newcastle 2-1 a Etihad a wasan mako na 27, kenan saura maki biyu tsakani da Arsenal mai jan ragama, wadda za ta fafata da Tottenham a wasan mako na 28 ranar Lahadi.

  2. Sheffield Wednesday ta faɗi daga Championship, Champions League

    Wed

    Asalin hoton, Shutterstock

    Sheffield Wednesday, wadda aka cire mata maki 18 saboda karya dokar kashe kuɗi daidai samu, ta zama ta farko a tarihin English Football League da ta fadi daga gasar kasar tun a watan Fabrairu, bayan shan kashi 2-1 a hannun Sheffield United ranar Lahadi wanda ya tabbatar da saukarsu daga Championship.

    Tun watan Satumba ba ta ci wasa ba, kuma tana cikin jerin fafatawa 11 a jere ba tare da nasara ba a dukkanin gasa. Wednesday wadda tae ta karsen teburi ta 22, ana bin ta maki bakwai, kuma tana da tazarar maki 41 tsakani da West Bromwich Albion mai matsayi na 21,

    Da yake wasa 13 suka rage a kammala kakar bana, Wednesday ba za ta iya ci gaba da taka leda a baɗi ba, kenan za ta koma buga League One a baɗi.

    Ƙungiyar mai shekaru 158 a tarihi, yanzu ana neman mai sayenta.

  3. , Daga Jaridu

    De Bruyne

    Asalin hoton, Getty Images

    Real Madrid ce ke kan gaba wajen neman dan wasan baya na Jamus na Borussia Dortmund Nico Schlotterbeck, amma Barcelona ma tana sha'awar dan wasan mai shekaru 26. (AS Sport)

    Newcastle na sha'awar siyan dan wasan baya na Sifaniya Hugo Bueno mai shekaru 23 daga Wolves a wannan bazarar. (Football Insider)

    Liverpool na shirin mika tayin £83m ga dan wasan gefe na Ingila Anthony Gordon mai shekaru 24 na Newcastle idan dan wasan gaba na Masar Mohamed Salah, mai shekaru 33, ya bar kungiyar a wannan bazarar. (Fichajes)

    Everton na shirin gabatar da tayin £30m ga dan wasan gaba na Chelsea mai shekaru 23 Liam Delap a wannan bazarar. (Teamtalk)

  4. , Yadda teburin Premier League kafin a kammala wasannin mako na 27

    EPL Table

    Asalin hoton, BBC Sport

  5. , Wasannin da za a buga ranar Lahadi

    EPL

    Asalin hoton, BBC Sport

  6. , Sakamakon wasannin mako na 27a Premier League

    EPL Week 27

    Asalin hoton, BBC Sport

  7. An buga wasa biyar a Premier League ranar Asabar, Premier League

    Trophy

    Asalin hoton, Getty Images

    Ranar Asabar aka fara wasannin mako na 27 a gasar Premier League da aka yi karawa shida.

  8. Barkanmu da shiga sharhi da bayanan wasanni

    Jama'a barkanmu da shiga shirin sharhi da bayanan wasanni kai tsaye tare da ni Mohammed Abdu Mamman Skipper Tw.

    Za ku iya tafka muhawara a shirin ko bayar da gudunmuwa a BBCHausa Facebook.