Alkalan da za su ja ragamar wasan Masar da Najeriya, Afcon Morocco 2025/26
Alkalin wasa:Jalal Jayed
Mai kula da VAR:Lahlou Benbraham
Mataimaki a fili na ɗaya:Zakaria Brinsi
Mataimaki a fili na biyu:Mostafa Akarkad
Mai jiran ko-ta-kwana:Peter Waweru
Maiatmain VAR:Haythem Guirat
Tarihin wasan neman mataki na uku a gasar Afcon, Afcon Morocco 2025/26
Asalin hoton, Getty Images
Najeriya da Masar za su fafata a wasan neman matsayi na uku a Afcon karo na 32.
A cikin wasa 31 da aka buga a baya a neman matsayi na uku an ci ƙwallo 87.
A cikin wasa 13 daga 31, dukkan tawagogin biyu sun ci kwallo.
Wasa biyar baya a gurbin neman mataki na uku da fenariti aka kare — 1988, 1998, 2000, 2015 da 2023.
Wasan neman mataki na uku da aka fi cin ƙwallaye shi ne na 1998, lokacin da Burkina Faso da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DR Congo) suka tashi 4–4, inda DR Congo ta yi nasara a bugun fenariti bayan Burkina Faso ta fara da cin ƙwallo 3–0 da kuma 4–1.
Wasannin da suka kara a Afcon da sakamakonsu, Afcon Morocco 2025/26
Asalin hoton, Getty Images
1963 – Cikin rukuni: Masar 6–3 Najeriya
1976 – Zagaye na biyu: Najeriya 3–2 Masar
1980 – Cikin rukuni: Najeriya 1–0 Masar
1984 – Daf da karshe: Najeriya 2–2 Masar (Najeriya ta yi nasara a fenariti)
1988 – Cikin rukuni: Najeriya 0–0 Masar
1990 – Cikin rukuni: Najeriya 1–0 Masar
1994 – Cikin rukuni: Najeriya 0–0 Masar
2010 – Cikin rukuni: Masar 3–1 Najeriya
2021 – Cikin rukuni: Najeriya 1–0 Masar
Super Eagles da za su fuskanci Masar, Afcon Morocco 2025/26
Asalin hoton, Getty Images
Ƴan Masar da za su kara da Najeriya a Afcon, Afcon Morocco 2025/26
Asalin hoton, BBC Sport
Najeriya na fatan zama ta uku a Afcon karo na tara, Afcon Morocco 2025/26
Asalin hoton, Getty Images
Najeriya za ta so zama ta uku a gasar cin kofin Afirka karo na tara jimilla a lokacin da za ta fuskanci Masar ranar Asabar a Morocco.
Wannan ne karo na 10 da tawagogin biyu za su hadu a gasar cin kofin Afirka.
Gaba ɗaya
Najeriya: Wasanni 20, Ta yi nasara 8 da canjaras 6, Ta sha kashi 6, Ta ci kwallaye 29, Aka zura mata 24.
Masar: Wasanni 20, Ta yi nasara 6 da canjaras 6, Ta sha kashi 8, Ta ci kwallaye 24, Aka zura mata 29.
AFCON kawai
Najeriya: Wasanni 9, Ta yi nasara 5 da canjaras 2, Ta sha kashi 2, Ta ci kwallaye 12, Aka zura mata 13.
Masar: Wasanni 9, Ta yi nasara 2 da canjaras 2, Ta sha kashi 5, Ta ci kwallaye 13, Aka zura mata 12.
An kafa tarihin cin ƙwallo 120 tun kan gama Afcon ta bana
Asalin hoton, Getty Images
Gasar Cin Kofin Afirka ta Morocco 2025 an sake kafa tarihin bayan zama gasar da aka fi zura ƙwallaye a tarihinta, inda aka riga aka ci 120 kafin wasan neman mataki na uku da na karshe da za a buga ranar Lahadi.
Wannan adadi ya zarce tsohon tarihin kwallaye 119 da aka kafa a gasar da ta gabata a Côte d’Ivoire, kuma yana nuna karuwar kai hare-hare a raga, sannan an samu inganci wasa da ƙwarewa daga tawagogi da kuma ƴan wasan Afirka.
Kafin hakan, an ci kwallaye 102 a gasar shekarar 2019 da aka gudanar a Masar, lokacin da aka faɗaɗa gasar daga ƙungiyoyi 16 zuwa 24.
Barkanmu da shiga sharhi da bayanan wasanni
Jama'a barkanmu da shiga shirin sharhi da bayanan wasanni kai tsaye tare da ni Mohammed Abdu Mamman Skipper Tw.
Za ku iya tafka muhawara a shirin ko bayar da gudunmuwa a BBCHausa Facebook.