Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Afcon 2025/29: Najeriya ta yi ta uku bayan cin Masar

Wasan neman mataki na uku tsakanin Masar da Najeriya a gasar cin kofin nahiyar Afirka da Morocco ke karɓar bakunci 2025/26

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Alkalan da za su ja ragamar wasan Masar da Najeriya, Afcon Morocco 2025/26

    Alkalin wasa:Jalal Jayed

    Mai kula da VAR:Lahlou Benbraham

    Mataimaki a fili na ɗaya:Zakaria Brinsi

    Mataimaki a fili na biyu:Mostafa Akarkad

    Mai jiran ko-ta-kwana:Peter Waweru

    Maiatmain VAR:Haythem Guirat

  2. Tarihin wasan neman mataki na uku a gasar Afcon, Afcon Morocco 2025/26

    Najeriya da Masar za su fafata a wasan neman matsayi na uku a Afcon karo na 32.

    A cikin wasa 31 da aka buga a baya a neman matsayi na uku an ci ƙwallo 87.

    A cikin wasa 13 daga 31, dukkan tawagogin biyu sun ci kwallo.

    Wasa biyar baya a gurbin neman mataki na uku da fenariti aka kare — 1988, 1998, 2000, 2015 da 2023.

    Wasan neman mataki na uku da aka fi cin ƙwallaye shi ne na 1998, lokacin da Burkina Faso da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DR Congo) suka tashi 4–4, inda DR Congo ta yi nasara a bugun fenariti bayan Burkina Faso ta fara da cin ƙwallo 3–0 da kuma 4–1.

  3. Wasannin da suka kara a Afcon da sakamakonsu, Afcon Morocco 2025/26

    • 1963 – Cikin rukuni: Masar 6–3 Najeriya
    • 1976 – Zagaye na biyu: Najeriya 3–2 Masar
    • 1980 – Cikin rukuni: Najeriya 1–0 Masar
    • 1984 – Daf da karshe: Najeriya 2–2 Masar (Najeriya ta yi nasara a fenariti)
    • 1988 – Cikin rukuni: Najeriya 0–0 Masar
    • 1990 – Cikin rukuni: Najeriya 1–0 Masar
    • 1994 – Cikin rukuni: Najeriya 0–0 Masar
    • 2010 – Cikin rukuni: Masar 3–1 Najeriya
    • 2021 – Cikin rukuni: Najeriya 1–0 Masar
  4. Super Eagles da za su fuskanci Masar, Afcon Morocco 2025/26

  5. Ƴan Masar da za su kara da Najeriya a Afcon, Afcon Morocco 2025/26

  6. Najeriya na fatan zama ta uku a Afcon karo na tara, Afcon Morocco 2025/26

    Najeriya za ta so zama ta uku a gasar cin kofin Afirka karo na tara jimilla a lokacin da za ta fuskanci Masar ranar Asabar a Morocco.

    Wannan ne karo na 10 da tawagogin biyu za su hadu a gasar cin kofin Afirka.

    Gaba ɗaya

    • Najeriya: Wasanni 20, Ta yi nasara 8 da canjaras 6, Ta sha kashi 6, Ta ci kwallaye 29, Aka zura mata 24.
    • Masar: Wasanni 20, Ta yi nasara 6 da canjaras 6, Ta sha kashi 8, Ta ci kwallaye 24, Aka zura mata 29.

    AFCON kawai

    • Najeriya: Wasanni 9, Ta yi nasara 5 da canjaras 2, Ta sha kashi 2, Ta ci kwallaye 12, Aka zura mata 13.
    • Masar: Wasanni 9, Ta yi nasara 2 da canjaras 2, Ta sha kashi 5, Ta ci kwallaye 13, Aka zura mata 12.
  7. An kafa tarihin cin ƙwallo 120 tun kan gama Afcon ta bana

    Gasar Cin Kofin Afirka ta Morocco 2025 an sake kafa tarihin bayan zama gasar da aka fi zura ƙwallaye a tarihinta, inda aka riga aka ci 120 kafin wasan neman mataki na uku da na karshe da za a buga ranar Lahadi.

    Wannan adadi ya zarce tsohon tarihin kwallaye 119 da aka kafa a gasar da ta gabata a Côte d’Ivoire, kuma yana nuna karuwar kai hare-hare a raga, sannan an samu inganci wasa da ƙwarewa daga tawagogi da kuma ƴan wasan Afirka.

    Kafin hakan, an ci kwallaye 102 a gasar shekarar 2019 da aka gudanar a Masar, lokacin da aka faɗaɗa gasar daga ƙungiyoyi 16 zuwa 24.

  8. Barkanmu da shiga sharhi da bayanan wasanni

    Jama'a barkanmu da shiga shirin sharhi da bayanan wasanni kai tsaye tare da ni Mohammed Abdu Mamman Skipper Tw.

    Za ku iya tafka muhawara a shirin ko bayar da gudunmuwa a BBCHausa Facebook.