Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Afcon 2025/29: Najeriya ta yi ta uku bayan cin Masar

Wasan neman mataki na uku tsakanin Masar da Najeriya a gasar cin kofin nahiyar Afirka da Morocco ke karɓar bakunci 2025/26

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Osimhen yana benci a wasan Masar, Masar 0-0 Najeriya

    Victor Osimhen yana zaman benci, wanda ya ci ƙwallo hudu a Afcon a bana - ko za a saka shi a wasan ko kuma ba zai buga ba.

  2. , Masar 0-0 Najeriya

    Saura minti 15 a tashi wasan daga nan a yi karin lokaci idan ba a samu wanda ya yi nasara a ba a je ga bugun fenariti.

    Wasan neman mataki na uku da na huɗu a Afcon tsakanin Masar da Najeriya.

  3. Masar ta sauya ɗan wasa, Masar 0-0 Najeriya

    Ibrahim Adel na Masar ya canji Mostafa Mohamed.

  4. , Masar 0-0 Najeriya

    Mustapha ya yi satar gida ya buga ƙwallon mai tsaron ragar Najeriya, Nwabali ya tare.

  5. , Masar 0-0 Najeriya

    Akor na Nageriya ya yi kokarin bugo ƙwallo amma ta taɓa ɗan wasan Masar ta yi je ƙwana an kuma kwaso ba wani haɗari.

  6. , Masar 0-0 Najeriya

    An ture ƙyaftin ɗin Najeriya, Simon zuwa kasa, amma ba a hura komai ba.

  7. , Masar 0-0 Najeriya

    An yi wa ƙyaftin, Simon na Najeriya keta daga gefen hagu, amma an busa bugun tazara zuwa gidan Masar.

  8. Najeriya ta yi canji ɗan wasa, Masar 0-0 Najeriya

    Alex Iwobi na Najeriya ya canji Bright Osayi-Samuel saboda raunin da ya ji.

  9. , Masar 0-0 Najeriya

    Marmoush na Masar ya ja rigar Chukwueze na Najeriya an kuma busa bugu zuwa gidan Masar.

  10. Masar ta yi canji biyu, Masar 0-0 Najeriya

    Mahmoud Saber ya maye gurbin Trézéguet.

    Omar Marmoush ya canji Zizo.

  11. , Masar 0-0 Najeriya

    Ademola Lookman ya samu ƙwallo a cikin gidan Masar amma ya kasa samun damar bugawa Akor ya yi kokarin taɓa ƙwallon amma ta fita ƙwana.

  12. , Masar 0-0 Najeriya

    Simon na Najeriya ya ja ƙwallo ta hagu ya bugo, amma an ce an yi satar gida.

  13. , Masar 0-0 Najeriya

    Salah ya samu ƙwallo ya rasa mai zai yi ya koma ta kafarsa ta hagu, amma ƴan wasan Najeriya biyu sun hau kansa sun amma Simon ya ƙwace wallon.

  14. , Masar 0-0 Najeriya

    Mustapha na Masar ya ja ƙwallo a guje ta bangaren hagu daga baya an yi masa katsalanta wallon ya je wajen mai tsaron ragar Najeriya, shi kuwa ya buga sama da karfi.

  15. , Masar 0-0 Najeriya

    Zizo na Masar yana ta juya ƙwallo a daf da layi ya kasa samun dama ya bugu, amma ta fita jifa da Najeriya za ta yi.

  16. , Masar 0-0 Najeriya

    Shima ƙyaftin ɗin Najeriya, Simon a wasan Masar ya nemi raga amma ƙwallon ba zafi mai tsare ragar Masar ya kama cikin sauki.

  17. , Masar 0-0 Najeriya

    Onyedika na Najeriya ya samu dama ya buga ƙwallon zuwa gidan Masar, amma mai tsaron raga ya kama ya kuma kwanta kasa.

  18. Yadda aka buga zagayen farko Masar da Najeriya

  19. , Masar 0-0 Najeriya

    Najeriya ta ci ƙwallo, amma an soke da cewar akwai satar gida.

  20. An koma zagaye na biyu