Yaƙi na yawaita a yankunan da magoya bayan Assad ke da yawa a Syria
Ƙasashen duniya na ƙara bayya damuwarsu kan rikice-rikicen da suke ƙaruwa a Syria a yankunan da magoya bayan tsohon Shugaban Ƙasar Syria, Bashar al-Assad suke da yawa.
Rahotanni sun ce an kashe sama da mutum 1,000 a cikin ƴan kwanakin nan - kuma mafi yawansu fararen hula ƴan ɗarikar alawy.
Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya yi kira ga gwamnati ta bincika ƴanta'addan da ya bayyana da masu ikirarin jihadi da suke kashe mutane.
Shi ma babban jami'in kare haƙƙin ɗan'adam na Majalisar Ɗinkin Duniya, Volker Turk da gwamnatin Jamus duk sun yi irin wannan kira.