Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 09/03/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 09/03/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza da Isiyaku Muhammed

  1. Yaƙi na yawaita a yankunan da magoya bayan Assad ke da yawa a Syria

    Ƙasashen duniya na ƙara bayya damuwarsu kan rikice-rikicen da suke ƙaruwa a Syria a yankunan da magoya bayan tsohon Shugaban Ƙasar Syria, Bashar al-Assad suke da yawa.

    Rahotanni sun ce an kashe sama da mutum 1,000 a cikin ƴan kwanakin nan - kuma mafi yawansu fararen hula ƴan ɗarikar alawy.

    Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya yi kira ga gwamnati ta bincika ƴanta'addan da ya bayyana da masu ikirarin jihadi da suke kashe mutane.

    Shi ma babban jami'in kare haƙƙin ɗan'adam na Majalisar Ɗinkin Duniya, Volker Turk da gwamnatin Jamus duk sun yi irin wannan kira.

  2. Wakilan Gabas ta Tsakiya na ganawa a Jordan kan tsaron yankin

    Manyan wakilan ƙasashen Syria da Turkiyya da Iraƙi na taro a birnin Jordan domin tattauna batun tsaron yankin Gabas ta Tsakiya.

    Bayan rikicin da ake ciki a yanzu haka, ana sa ran taron zai mayar da hankali wajen magance fargabar sake bayyanar ƙungiyar ISIS.

    Ƙasashen Yamma da gwamnatin yankin sun sha yin gargaɗin cewa ƙungiyar ISIS na sake haɗa mayaƙanta tun bayan hamɓarar da gwamnatin Bashar al-Assad na Syria a watan Disamba.

  3. Harin Isra'ila ya kashe mutum biyu a Gaza

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Kafofin yaɗa labaran Isra'ila sun ce wani harin jirgi maras matuƙi da Isra'ila ta kai birnin Gaza ya kashe mutum biyu.

    Sojojin Isra'ila sun tabbatar da kai harin kan wasu gungun Falasɗinawa da suka ce suna yunƙurin dasa bom a kusa da sojojin Isra'ila.

    A makon da ya gabata ne dai matakin farko na yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin Gaza ta ƙare, kuma aka kasa shiga tattaunawar mataki na biyu, sakamakon saɓanin da aka samu tsakanin ɓangarorin biyu.

    Sai dai bayanai na cewa a yanzu Hamas ta aminci da tsawaita matakin farko na yarjejeniyar da za ta bayar da damar dakatar da hare-hare a yankunan Falasɗinawa

  4. Girke-girken Ramadan: Yadda ake sarrafa taliyar ɗanwake wato ɗanwake pasta

    A filinmu na girke-girken Ramadan na yau, Radiya Sani Shinkafi ta nuna mana yadda ake iya sarrafa taliyar danwake ko danwake pasta.

    Ku biyo Radiya domin ganin yadda ake yin wannan haɗin.

    Bayanan bidiyo, Latsa alamar da ke sama domin kallo
  5. Isra'ila za ta yanke wutar lantarkin Gaza

    Netanyahu

    Asalin hoton, Reuters

    Isra'ila ta sanar da yunƙurinta na yanke wutar lantarkin Gaza, a wani mataki da ake ganin za ta ɗauka ne domin tursasa Hamas ta saki dukkan sauran waɗanda take garkuwa da su guda 59.

    Ministan makamashin ƙasar, Eli Choen ya ce ya umarci kamfanin rarraba wutar lantarki na ƙasar da ta yanke layin wutar lantarkin da ke zuwa zirin.

    Ya ƙara da cewa gwamnatin ƙasar za ta yi amfani duk wata hanya da za ta iya domin dawo da waɗanda ke hannun Hamas ɗin gida, ciki har da yanke hanyoyin ruwan sha.

    A makon jiya ne Isra'ila ta hana shigar da abinci da man fetur da sauran kayan agaji Gaza..

  6. PDP ta sake ɗage babban taronta na ƙasa

    PDP

    Asalin hoton, PDP

    Babbar jam'iyyar a Najeriya wato PDP ta sake ɗage babban taronta na ƙasa wato taron NEC, wanda yanzu aka mayar ranar 15 ga Mayun 2025.

    Jam'iyyar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da jam'iyyar ta fitar, wadda babban sakatarenta, Sunday Ude-Okoye ya sanya wa hannu.

    Asali jam'iyyar ta sanar za ta yi babban taron ne a ranar 13 ga Maris, sannan aka ɗage saboda wasu zaɓukan cike gurbi da aka yi a wasu jihohi da yankuna.

    Tun a shekarar da ta gabata ce dai aka saka ranar babban taron na 98, amma ana ɗagewa, wanda wataƙila hakan bai rasa nasaba da wasu matsaloli da jam'iyyar ke fuskanta.

  7. 'Ƴancirani na bayar da gudunmowa a ci gaba da wanzuwar Singapore'

    Lee Hsien Loong

    Asalin hoton, Getty Images

    Tsohon firaministan Singapore mai ƙarfin faɗa a ji, Lee Hsien Loong ya ce ƴan cirani na da matuƙar muhimmanci wajen ci gaba da wanzuwar ƙasar.

    Ya ce sakamakon yadda ƙasar ke fuskantar ƙarancin haihuwar jarirai kowace shekara, dole ana buƙatar ƴan ciranin domin inganta tattalin arzikin ƙasar.

    Yayin da yake jawabi a wani taron maraba da wasu mutanen da suka samu takardun izinin zama ƴan ƙasar, Mista Loong ya ce sabbin zuwan za su taimaka wajen inganta rayuwa a Singapore.

    Sai dai ya amince cewa hanyoyin da ake bi wajen bayar da takardun izinin zama ƴanƙasa a Singapore da na matuƙar tsauri.

    Kusan kashi ɗaya bisa uku na al'ummar Singapore miliyan shida ƴan ƙasashen waje ne da ke aiki a ƙasar.

  8. Shugaban Ghana na ziyarar aiki a Nijar

    Sojoji

    Asalin hoton, CNSP

    Shugaban ƙasar Ghana John Dramani Mahama na ziyarar aiki a Jamhuriyar Nijar mai maƙwabtaka.

    Mahama ya gana da shugaban mulkin sojin Nijar Janar Abdurahman Tiani a fadar gwamnatin ƙasar da ke birnin Yamai.

    Ziyarar na zuwa ne kwana guda bayan ya ziyarci ƙasar Mali.

    Hotuna

    Asalin hoton, CNSP

    Kawo yanzu dai babu cikakken bayani kan abin da shugabannin biyu suka tattauna.

    Sai dai a lokacin da ya kai ziyara Mali ranar Asabar, John Mahama ya ce yana ziyarar ne don daidaita lamura, kuma zai yi ƙoƙari samar da haɗin kai tsakanin ƙasashen yankin Sahel da Ecowas.

    ..

    Asalin hoton, CNSP

    A baya-bayan nan ne dai Nijar da makwabtantan Mali da Burkina suka kafa sabuwar ƙungiyar ƙasashen yankin Sahel, bayan ficewarsu dga Ecowas.

    ..

    Asalin hoton, CNSP

  9. Hikayata: Labarin Mugun Nama

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin sauraron shirin

    A filinmu na Hikayata a yau mun kawo maku 'Labarin Mugun Nama', wanda Fatima Isa da ke zaune a birnin Katsina ta rubuta, wanda kuma abokiyar aiki, Badriyya Tijjani Ƙalarawi ta karanta.

    Marubuciyar ta gina labarin kan yadda wasu mazan aure ke neman matan banza a waje, duk kuwa da irin kulawar da matansu ke nuna musu a cikin gida.

    Fatima Isa ta yi ƙoƙarin nuna yadda wannan matsala ta shiga tsakanin wasu ma'aurata har ta kai su ga samun saɓani, daga ƙarshe iyayen matar suka ba ta haƙuri ta ci gaba da zama a gidansa.

    Matar ta yi ƙoƙarin nuna masa abin da yake yi bai dace ba, har ta ba shi damar ƙara aure, amma ya bijire, ƙarshe ya gamu da kaidin matan banza, inda wata cikin matan da yake bi ta yanke masa gaba, saboda ta gano yana neman wata matar bayan ita.

    Wannan dai shi ne labari na ƙarshe a jerin labarai 15 da suka cancanci yabo, da muka saba kawo maku a duk shekara bayan kammala gasar Hikayata.

  10. An harbe wani mutum riƙe da bindiga a kusa da fadar White House

    Amurka

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar tsaron farin kaya ta Amurka ta ce ɗaya daga cikin jami'anta ya harbe wani mutum riƙe da makami a kusa da fadar White House ranar Asabar ta maraice.

    Hukumar tsaron farin kaya - wadda ke da alhakin tsaron shugaban Amurka - ta ce mutumin ya je babban birnin Amurka daga jihar Indiana a mota

    ƴansandan Indianan ne suka sanar da su game da bulaguron mutumin.

    Kakakin hukumar, Anthony Guglielmi ya ce tuni aka garzaya da mutumin zuwa asibiti, kuma ba a san halin da yake ciki ba.

    Ya ƙara da cewa babu jami'in hukumar ko guda ɗaya da ya jikkata a lokacin faruwar lamarin.

  11. Da gaske tsufa na farawa ne bayan shekara 35?

    Wani mutum

    Asalin hoton, Getty Images

    A waɗanne shekaru ne za ka iya ɗaukar kanka cewa ka zama babba ko ka yi girman da ka dawo daga rakiyar wasu abubuwa da ke faruwa a kusa da kai.

    Wasu ra'ayoyin jama'a da aka tattaro sun nuna cewa shekara 35.

    To idan haka ne wane lokaci ne a shekarun mutum za a ce na sheƙe-ayarsa?

    Wasu mutanen da ganin shekarun ƙuruciya - wato goma sha wani abu (13 zuwa 19), ko kuma shekarun karatu a jami'a.

    To amma yayin da mutum ya kai shekara 35 lokaci ne da zai iya dawowa daga rakiyar wasu abubuwa a rayuwarsa da kuma rayuwar aiki.

    Karanta cikakken labarin a nan

  12. Ƴanbindiga sun kashe shugaban Miyetti Allah na jihar Kwara

    shugaba

    Asalin hoton, MACBAN

    Ƙungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) na alhinin kisan da aka yi wa shugabanta na jihar Kwara, Idrissu Abubakar.

    A ranar Asabar ne wasu ƴanbindiga ɗauke da makamai suka auka gidan shugaban ƙungiyar tare da halaka shi.

    Kisan shugaban Miyetti Allah na jihar Kwaran shi na zuwa ne kusan wata biyu bayan kashe shugaban ƙungiyar na jihar Katsina, Alhaji Sirajo Ahmad Mairana.

    Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar mai ɗauke da sa hannun babban sakatarenta na ƙasa, Bello Aliyu Gotomo, ta yi Allah wadai da kisan da aka yi wa Idrissu Abubakar mai shekara 33.

    Sanarwar ta ambato shugaban ƙungiyar na ƙasar, Baba Othman Ngelzarma na cewa an kashe Idrissu Abubakar da mislain ƙarfe 10:00 na daren da ya gabata bayan komawa gida daga sallar Tarawih.

    Ƙungiyar ta ce cikin shekara biyu da suka gabata, ƴanbindiga sun kashe shugabanninta bakwai na jihohi da na ƙananan hukumomi.

  13. EU za ta kashe euro biliyan 800 kan tsaron ƙasashenta

    ggg

    Asalin hoton, others

    Shugaban Sashen Tsaro na Ƙungiyar Tarayyar Turai ya bayyana shirin ƙungiyar na kashe euro biliyan 800 kan tsaro ƙasashen ƙungiyar nan da shekara huɗu masu zuwa.

    Yayin da yake zantawa da BBC, Andrius Kubilius ya ce ƙudirin wani mataki ne aikewa da saƙon gargaɗi kan Rasha da ta jingije ƙudurinta na mamayar ilahirin Ukraine.

    Mista Kubilius - da aka naɗa kan muƙamin a karon farko a watan Disamba - ya ce za a kashe kuɗin tare da Ukraine kuma za a yi amfani da su wajen sayaen makaman da ake ƙera a Ukraine.

    A mako mai ƙarewa ne Faransa da Birtnaiya suka fara bai wa ma'aikatar tsaron Ukraine tallafin kuɗi, wanda suka samu ta hanyar kuɗi ruwa daga kadarorin Rasha da ƙasashen suka ƙwace na biliyoyin daloli.

  14. Sudan ta zargi Sudan ta Kudu da kafa asibiti don 'samar wa RSF makamai'

    Sudan ta soki makwabciyarta Sudan ta Kudu saboda bayar da dama da ta yi na kafa asibiti a kusa da kan iyakarta, saboda fargabar kar a yi amfani da shi wajen samar wa mayaƙan RSF makamai.

    Ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa - wadda aka jima ana zargi da goyon bayan RSF - ce ta bai wa Sudan ta Kudu kyautar asibitin.

    Dama dai an zargi ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawar da amfani da wani asibiti a gabashin Chadi wajen samar wa RSF makamai - zargin da ƙasar ta musanta.

    Ministan ma'adinai na sudan, Mohamed Bashir Abunommo ya bayyana asibitin da ''sansanin farmaki'' da aka lullu ɓe a matsayin asibiti.

  15. Zariya za ta samu ƙarin manyan makarantu biyar daga tarayya a 2025 - Kakakin Majalisa

    Kakakin majalisa wakilan Najeriya

    Asalin hoton, Hon. Tajudeen Abbas/X

    Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Hon. Tajudeen Abbas ya ce mazaɓarsa ta Zariya za ta samu ƙarin manyan makarantu gwamnatin tarayya biyar da na sakandire biyu a kasafin kuɗin 2025.

    Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya, NAN ya ruwaito kakakin majalisar na bayyana a haka a lokacin liyafar buɗe-baki da Hon. Tajudeen ya shirya tare da al'ummar mazaɓarsa a ranar Asabar.

    Ya ce matakin yunƙuri ne na ƙarfafa kambin Zariya a matsayinta na cibiyar ilimi mai zurfi.

    Kakakin Majalisar ya ce sabbin makarantun da mazaɓar tasa za ta samu sun haɗa da Kwalejin Ayyukan Noma ta Tarayya da Makarantar Kula da Kiwon Dabbobi da Baye ta Tarayya da Kwalejin Fasaha ta Tarayya.

    Sauran sun haɗa da Cibiyar Horas da Ayyukan Cigaba da Cibiyar Tattara Fasahohi da makarantar Masu Buƙata ta Musamman - wadda ta ƙunshi furamare da sakandire, da kuma Sakandiren gwamnatin Tarayya, kmar yadda NAN ya ruwaito.

  16. 'An kama kusan mutum 200 a tattakin bikin Ranar Mata a Turkiyya'

    Mata

    Asalin hoton, Reuters

    Waɗanda suka shirya tattakin bikin Ranar Mata ta Duniya a Turkiyya sun ce an kama mutane kusan 200 a dandalin Taskim da ke Santanbul, babban birnin ƙasar - da aka haramta zanga-zangar siyasa a tsawon shekaru.

    Hotunan da aka fitar a shafukan sada zumunta sun nuna yadda rukunin masu zanga-zangar suka doshi inda ƴansanda suka kafa shige, lamarin da ya haifar da hargitsi, sannan wasu matan ana ta jansu,

    Kawo yanzu dai ƴansandan ƙasar ba su ce komai ba game da lamarin.

    Daya daga cikin masu zang-zangar ta ce da fari ba ta yi niyyar fita zanga-zangar ba, amma daga baya da na ji an haramta sai ta ce sai ta shiga.

    Kafin dai a samu hargitsin fiye da mata 3,000 sun yi tattaki cikin lumana a tsakiyar birnin, riƙe da alluna da takardun da aka rubuta saƙonnin neman kawo ƙarshen cin zarafin mata.

  17. Ministar tsaron Argentina ta tsallake rijiya da baya a hannun masu zanga-zanga

    Patricia Bullrich

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministar kula da tsaron ƙasa a tsaron Argentina, Patricia Bullrich ta tsallake rijiya da baya a hannun masu zanga-zanga bayan da ta shiga cikinsu a birnin Bahía Blanca da ambaliya ta ɗaiɗaita.

    Aƙalla mutum 13 ne suka mutu, sannan dubbai suka rasa muhallansu sakamakon ambaliyar da ta aukawa yankin a makon da ya gabata.

    Masu zanga-zangar sun riƙa zagin Ms Bullrich da ɗora wa gwamnati laifin abin da ya faru da su.

    A wata hira da kafar yaɗa labaran ƙasar, ministar ta ce yanayin ya yi muni sosai, amma gwamnati na bakin ƙokarinta wajen ganin an kai agaji

  18. Masu goyon baya da masu adawa da shugaban Koriya ta kudu sun gangami a ƙasar

    masu zanga-zanga

    Asalin hoton, Reuters

    Dandazon mutane sun yi fitar farin ɗango a birnin Seoul na Koriya ta Kudu domin gangamin adawa da magoya baya da masu sukar shugaban ƙasar da aka tsige.

    An datse tituna a wasu yankuna kafin soma gangamin neman a soke tuhumar da ake yi wa Yoon Suk Yeol.

    A gefe guda kuma wasu na gangamin ganin ta dole an shire shugaban ƙasar da ake cewa ya yi a 'bin kunya'.

    A jiyar Asabar ne aka saki Mista Yoon daga gidan yari bayan tsare shi tun watan Disamba kan yuƙurin kafa dokar soji - da ba ta samu karɓuwa ba - a ƙasar.

  19. 'Hamas za ta amince da tsawaita matakin farko na yarjejeniyar tsagaita wuta saboda Ramadan'

    Isra'ila ta sanar da aike da wakilai zuwa Qatar a gobe Litinin domin tattauna tsawaita matakin farko na yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin Gaza.

    Sanarwar na zuwa ne bayan kafofin yaɗa labaran Larabawa sun bayar da rahoton cewa ƙungiyar Hamas ta Falasɗinawa ta nuna za ta amince da tsawaita matakin farko na yarjejeniyar saboda watan Ramadan.

    Ƙungiyar ta rasa ƙwarin gwiwwa a makon da ya gabata sakamakon katse shigar da kayan agaji zuwa Gaza da ƙaddamar da sabbin hare-haren sama bayan kawo ƙarshen mataki na farko na yarjejeniyar da ake kai.

  20. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai tseye barkanmu da hutun ƙarshen mako.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Kuna iya ziyartar shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.