Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Da gaske tsufa na farawa ne daga shekara 35?
- Marubuci, Mark Johansson
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Journalist
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
A waɗanne shekaru ne za ka iya ɗaukar kanka cewa ka zama babba ko ka yi girman da ka dawo daga rakiyar wasu abubuwa da ke faruwa a kusa da kai.
Wasu ra'ayoyin jama'a da aka tattaro sun nuna cewa shekara 35.
To idan haka ne wane lokaci ne a shekarun mutum za a ce na sheƙe-ayarsa?
Wasu mutanen da ganin shekarun ƙuruciya - wato goma sha wani abu (13 zuwa 19), ko kuma shekarun karatu a jami'a.
To amma yayin da mutum ya kai shekara 35 lokaci ne da zai iya dawowa daga rakiyar wasu abubuwa a rayuwarsa da kuma rayuwar aiki.
Wani nazari da aka yi a Jami'ar Kent ta Birtaniya ya nuna cewa shekara 35 ba lokaci ne kawai da mutum ke ganin yanzu shi ba yaro ba ne ko matashi - shekaru ne da kuma a lokacin mutane ke kaiwa ƙoli-ƙoli a jin kaɗaici a rayuwarsu, su ma mata a wannan shekaru suke kaiwa ƙoli-ƙolin rashin nuna karsashi da damuwa da abubuwa.
Bugu da ƙari shekara 35 , ita ce shekarar da a lokacin muke fara tsanar ayyukanmu, kamar yadda wani bincike da aka yi a kan ma'aikata sama da 2,000, kamfanin Birtaniya na Robert Half mai nazari a kan ma'aikata ya yi.
Wasu bayanai sun nuna cewa a lokacin da mutum ya dumfari shekara 35, nauye-nauye na iyali da buƙatu na kuɗi na ƙaruwa, lamarin da ke ƙara matsalolin da ke kan mutum a gida da kuma wurin aiki.
Ƙarin matsin?
Lokacin da ka kai shekara 35 a lokacin ne maganar fargabar rasa aikinka take ƙara damunka sosai.
Bayanan da aka samu daga ofishin ƙididdiga na Birtaniya kan nazari da aka yi a rubu'in farko na shekarar 2017, ma'aikatan da suke tsakanin shekara 35 zuwa 49 sun fi fuskantar barazanar rasa aikinsu ninki biyu a kan ma'aikatan da suke tsakanin shekara 25 zuwa 34.
Bugu da ƙari ma'aikatan da suke rukunin wannan shekaru (35 to 49) ba sa gamsuwa da aikinsu kamar abokan aikinsu da shekarunsu ba su kai wannan rukunin ba, kamar yadda nazarin ya nuna.
Haka kuma binciken ya nuna cewa mutum ɗaya daga cikin shida a ma'aikata a Birtaniya da suka wuce shekara 35 ba sa jin daɗin aikinsu kuma wannan yawa ya ninka biyu a kan ma'aikatan da suke ƙasa da shekara 35.
Matasan ma'aikata yawanci ba sa fuskantar matsi daga shugabannin aikinsu yayin da ma'aikatan da suka kai shekara 35 ke fama wajen amsa tambayoyin shugabannin wajen aikinsu, kamar yadda binciken ya nuna.
Ba laifi ba ne a ce wasu daga cikin bambance-bambancen da ake samu a tsakanin masu shekarun da ba su kai 35 ba da kuma na bayan da mutum ya wuce shekara 35 ɗin abu ne da mu da kanmu muke yin wannan iyaka, in ji Julia Clarke wadda ke aiki a wani kamfanin bincike Ipsos.
Clark ta ƙara da cewa abu ne da aka saba ka ga kamfanonin bincike su yi amfani da rukunin shekarun da ke da bambancin shekara goma ko ma fiye da haka a tsakaninsu, ta yadda zai iya kasancewa an samu bambanci a tsakanin waɗannan rukunan biyu.
Misali mutum mai shekara 20 galibi ya bambanta da wanda ke shekara 29, amma kuma duk da haka an sanya su a rukuni ɗaya.
Clark ta ce saboda haka ne rukunin shekarun na farko zai kasance daga masu shekara 18 zuwa 24, sai na gaba kuma masu shekara 24 zuwa 34, da sauransu.
Haka su ma matan da suka wuce shekara 35 waɗanda suke son haihuwa suna fuskantar damuwa game da haihuwa cewa kamar sun wuce lokacin haihuwa to amma bincie da aka yi da dama a baya-bayan nan sun nuna cewa, damar haihuwa a wajen mata ba ta raguwa sosai kamar yadda wasu mutane suke tunani.
A Amurka ana samun ƙaruwar matan da ke jinkirta lokacin da za su fara haihuwa har sai sun zarta shekara 30 domin su samu damar ci gaba da karatu da kuma samun aiki mai kyau.
Alƙaluman baya-bayan nan na hukumar yaƙi da cutuka ta Amurka, sun nuna cewa matan da suke shekarun farko-farko na gaba da 30 a yanzu suna haihuwar yara fiye da takwarorinsu mata da ke shekaru 20 da ɗoriya, a karon farko a tarihin ƙasar.
Akwai kuma dalilan kuɗi da ke sa jinkirta haihuwa. Wani nazari da aka yi a 2011 ( da aka wallafa a mujallar Population Economics ), ya gano cewa duk shekarar da mace ta jinkirta haihuwa hakan na ƙara yawan abin da take samu a aikinta da kashi tara bisa ɗari.
Jinkirta abu
Akwai wata gurguwar fahimta da ake yi cewa mutanen da suke 'yan shekara 20 zuwa sama da masu shekara 30 zuwa sama su ne shekarun da suka fi kyau a rayuwarmu kuma zagwanyewa ko raguwa a dukkanin fannonin rayuwarmu na farawa ne can gaba bayan waɗannan shekaru in ji Dilip Jeste, darekta a cibiyar nazari kan yawa shekaru cikin lafiya a Jami'ar California, San Diego.
To amma a zahiri waɗannan shekaru na cike da matsin-lamba da dama da kuma tsoro da fargaba da ke da alaƙa da matakin da mutum zai ɗauka ko hukuncin da zai yanke a rayuwarsa.
Ƙaruwar da ake samu ta rukunin da ya fi yawa a tsakanin jama'a a ƙasashen da suka ci gaba, haɗi da zaɓin da mutum yake da shi na ayyuka a wannan zaman da tattalin arziƙin duniya kusan yake haɗe, wannan ya sa da wuya mutum ya iya tsayawa a wani aiki ɗaya ko kuma wata ƙasa ko gari ɗaya - saɓanin yadda abubuwa suke ga mutanen baya.
''A baya mutane kan yanke hukunci babba kuma na tsawon lokaci tun suna shekara 20 da ɗoriya, to amma mutanen da suke wannan rukunin shekarun yanzu sukan yi ta jinkirta yanke wannan hukunci game da rayuwarsu har sai nan gaba," in ji Guest.
Ya ƙara da cewa : "Suna jinkirta aure, suna jinkirta haihuwa, saboda haka abubuwa da dama da ke matsa wa rayuwar mutum a da tun shekarunsa ba su yi yawa ba, yanzu suna samuwa ne a bayan shekara 30.''
To amma kamar yadda Guest ya ce, daɗin maganar shi ne sauran rayuwarka za ta kasance cikin farin ciki. Haka ne ba lalle ba ne tsufa ya kasance abin jin daɗi, to amma tunani da basirarka ka iya ƙaruwa yayin da kake ƙara tsufa tsawon gomman shekaru.
"Muna sanin kanmu sosai da sosai, muna yanke hukuncin da ya fi dacewa, sannan kuma ba ma nuna son-kai sosai a lokacin,'' wannan shi ne amfanin da ke tattare da girma ko tsufa - amfanin girma hankali in ji Guest.