Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Laraba 30/07/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Laraba 30/07/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Aisha Babangida, da Abdullahi Bello Diginza, da Umar Mikail

  1. Matakin Birtaniya na amincewa da ƙasar Falasɗinu goyon bayan Hamas ne - Netanyahu

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce matakin da Birntaniy ta ɗauka na barazanar amincewa da ƙasar Falasɗinu tsantsar goyon baya ne ga ƙungiyar Hamas.

    A ranar Talata ne, Firaministan Birtaniya, Keir Starmer, ya bayyana cewa ƙasarsa za ta amince da kafa ƙasar Falasɗinu a watan Satumba, matuƙar Isra’ila ba ta dakatar da yaƙi da cika wasu sharuɗɗa ba.

    Sai dai Netanyahu ya soki matakin da cewa tamkar nuna goyon baya ne ga abubuwan da Hamas ke yi.

    ''Starmer ya nuna wa munanan ayyukan Hamas goyin baya ta yadda za ta ci gaba da ayyukanta na ta'addanci da cutar da mutane'', kamar yadda ya wallafa a shafinsa na sada zumunta

    Matakin na Birtaniya ya yi kama da na Faransa, wadda ta ce za ta goyi bayan kafa ƙasar Falasɗinu a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya da za a yi a watan Satumba.

    Shugaban Falasɗinawa, Mahmoud Abbas, ya yi maraba da wannan ci gaba, amma Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce hakan zai ƙarfafa Hamas ne kawai.

    A halin yanzu dai, har yanzu ana fama da mummunar matsalar jin ƙai a Gaza, inda ake ci gaba da fafatawa.

    Masana lafiya da Majalisar Ɗinkin Duniya sun ce yunwa na ƙara tsananta a Gaza.

    Yau ne rana ta ƙarshe ta taron kwanaki uku da Majalisar Ɗinkin Duniya ke yi, don neman mafita tsakanin Isra’ila da Falasɗinawa.

  2. Amincewa da ƙasar Falasɗinu: Birtaniya ta gindaya wa Isra'ila sharuɗɗa

    Keir Starma

    Asalin hoton, Reuters

    Firaministan Birtaniya, Keir Starmer ya shimfiɗa wa Isra'ila wasu jerin sharuɗan da ya ce idan ba ta cika ba, Birtaniya za ta amince da ƙasar Falasdinu.

    A ranar Talata ne Mista Starmer ya ce idan har Isra'ila ba ta cika waɗannan sharuɗa ba zuwa watan Satumba Birtaniya za ta amince da ƙasar Falasɗinu.

    Sharuɗɗan da firaministan ya gindaya sun haɗa da:

    • Amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta
    • Bai wa Majalisar Dinkin Duniya damar sake shigar da agaji Gaza
    • Amincewa da yuarjejeniyar zaman lafiya na dogon lokaci wanda zai ''samar da ƙasashe biyu"
    • Tabbatar da cewa ba za a ci gaba da ƙwace Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye ba

    Haka kuma Keir Starmer ya kuma sake jaddada buƙatun da Birtaniya ke da su kan Hamas da suka haɗa da:

    • Amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta
    • Sakin duka sauran Isra'ilawan da take riƙe da su
    • Amincewa ba za ta saka hannu a tafiyar da gwamnatin Gaza ba
    • Miƙa duka makamanta
  3. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BC Hausa barkanmu da safiyar wannan rana ta Laraba, da Hausawa ke yi wa kirari da 'Ta bawa ranar samu'.

    Ku kasance da mu, domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

    Kada ku manta za ku iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta.