Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Laraba 30/07/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Laraba 30/07/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Aisha Babangida, da Abdullahi Bello Diginza, da Umar Mikail

  1. Mu kwana lafiya

    Ƙarshen rahotonnin kenan a wannan shafi na ranar Laraba.

    Mu hadu da ku gobe domin samun wasu sababbi daga Sashen Hausa na BBC.

  2. Trump ya ƙaƙaba wa Brazil harajin kashi 50

    Jami'an gwamnatin Amurka sun ce za su saka wa alƙalin kotun ƙoli ta Brazil takunkumi saboda zargin sa da "bayar da umarnin" tsarewa da kuma daƙile 'yancin faɗar albarkacin baki.

    'Yan awanni bayan sanar da takunkuman kuma sai Shugaba Donald Trump ya sanya hannu kan waani umarnin shugaban ƙasa da ya ƙara harajin kayayyaki kan Brazil zuwa kashi 50 cikin 100 kan dukkan kayan da ta shigar da Amurka.

    Mai Shari'a Alexandre de Moraes ne yake jagorantar shari'ar da ake yi wa tsohon shugaban Brazil Jair Bolsonaro inda ake zargin sa da yunƙurin juyin mulki bayan shan kaye a zaɓen 2022.

    Bolsonaro ya musanta zargin kuma ya kira alƙalin da ɗan kama-karya.

  3. Ƙasashe sun fara janye gargaɗin ambaliyar tsunami

    Wasu ƙasashen da ke yankin arewacin Pacific sun janye gargaɗin da suka aika bayan aukuwar mummunar girgizar ƙasa a gabashin Rasha.

    Guguwar ta afka kusa da Kamchatka, inda mutane da dama suka ji rauni. Tun da farko Japan ta bayar da umarnin kwashe kusan mutum miliyan biyu.

    Wakiliyar BBC ta ce ana iya ganin mutane da dama a saman rufin gidajensu a yankin Hokkaido da ke Japan yayin da mahukunta ke ci gaba da bukatar mazauna yankunan da ke gabar ruwan gabashin kasar su bar wajen ko kuma su koma wurare masu tudu.

    A Hawaii da kuma California na Amurka, an shawarci mutane da su guji zuwa gefen tekuna.

    Akwai yiwuwar igiyar ruwa mai tsawon mita uku za ta afka wa gabɓar ruwan Chile da Costa Rica da kuma wasu tsibiran yankin Pacific.

    Har yanzu Taiwan ba ta janye nata gargaɗin ba.

  4. Ƙasashen Larabawa sun nemi Hamas ta zubar da makamanta

    Ƙasashen Larabawa da dama sun nemi ƙungiyar Hamas ta zubar da makamanta kuma ta haƙura da mulkin Zirin Gaza domin kawo ƙarshen yaƙin da Isra'ila ke yi a zirin.

    Ƙasashe 17 ne ciki har da Tarayyar Turai ƙungiyar hadin kan Larabawa suka fitar da sanarwa mai shafi bakwai a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya da ke kiran a farfaɗo da batun kafa ƙasa biyu, wato ta Falasɗinu da kuma Isra'ila.

    "A yunƙurin kawo ƙarshen yaƙin nan, dole ne Hamas ta kawo ƙarshen ikonta a Gaza kuma ta miƙa makamai ga Hukumar Falasɗinawa...kamar yadda manufar kafa ƙasar Falasɗinu ta tanada," a cewar sanarwar.

    A ranar Litinin ne hukumar ta Falasɗinawa wato Palestinian Authority ta nemi Hamas da Isra'ila duka su fice daga Gaza domin ba ta damar karɓe iko da zirin.

    Sanarwar ta kuma yi Allah wadai da harin Hamas na ranar 7 ga watan Oktoban 2023, wanda ya jawo ɓarkewar yaƙin.

  5. Sojin Najeriya sun ce sun kashe 'yan Boko Haram tara a jihar Borno

    Rundunar sojin Najeriya ta ce ta yi nasarar kashe mayaƙan Boko Haram tara a jihar Borno da ke area maso gabashin ƙasar.

    Dakarun rundunar musamman ta "Operation Hadin Kai" ne suka kashe 'yanbindigar a yankunan kananan hukumomin Konduga, da Bama, da Gwoza.

    Bayanai sun ce mayakan sun yi yunƙurin tarwatsa gadar da ta haɗa Marte da Dikwa kafin sojojin su fatattake su, inda suka gano bama-bamai 17 a ƙarƙashin gadar.

    Mai magana da yawun rundunar, Kyaftin Reuben Kovangiya, ya faɗa cikin wata sanarwa cewa an kuma gano makamai, da alburusai, da sauran kayan aiki na mayaƙan.

    Ya ce dakarunsu sun yi wa mayakan kwanton bauna bayan yi masu ƙawanya, yayin da a gefe guda kuma jiragen sama ke yi masu luguden wuta, lamarin da ya sa aka kashe tara daga cikinsu.

    Daga cikin tarin makaman da akwa ƙwace daga hannun mayaƙan sun haɗa da bindigogi ƙirar AK-47, da kirar PKT a ƙananan hukumomin Konduga, Bama da Gwoza.

  6. Sojojin Sudan ta Kudu da Uganda sun kashe juna a kan iyaka

    Sojojin Sudan ta Kudu da na Uganda sun yi musayar wuta a kusa da iyakarsu, lamarin da ya yi sanadin rasa rayukan akalla mutum shida.

    Mai magana da yawun rundunar sojin Uganda ya ce sojojin Sudan ta Kudu sun tsallaka iyakar Uganda ta ɓangaren yankin West Nile sannan suka ƙi barin wajen.

    Ya ce an kashe ɗaya daga cikin sojojin ƙasarsa.

    Jami'ai a babban birnin Sudan ta Kudu Juba sun ce musayar wutar ta jawo kashe musu sojoji biyar.

    Kasashen biyu dai sun jima suna da kyakkyawar alaka a tsakaninsu. Shugaban Uganda Yoweri Museveni ya taimaka wa 'yantawayen Sudan ta Kudun wajen kwatar 'yancinsu daga Sudan.

  7. Za mu kammala titin jirgi na Kaduna zuwa Kano a 2026, in ji gwamnatin Najeriya

    Gwamnatin Najeriya ta ce za a kammala aikin titin jirgin ƙasa daga Kaduna zuwa Kano a cikin shekarar 2026 mai zuwa, kamar yadda Ministan Sufuri Sa'idu Ahmed Alkali ya bayyana.

    Da yake magana yayin wani taron tuntuɓa tsakanin 'yan ƙasa da gwamnati da ke gudana a jihar Kaduna da ke arewacin ƙasar, ministan ya ce lokacin da Shugaba Tinubu ya hau mulki kashi 15 cikin 10 na aikin kawai aka kammala.

    "Amma zuwa yanzu an kammala kashi 53 cikin 100," in ji shi cikin wata sanarwa da ma'aikatar yaɗa labarai ta fitar a yau Laraba.

    A 2024 gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa ta samu rancen kuɗin da za ta kammala aikin daga wani bankin kasuwanci na ƙasar China, abin da ministan ya jaddada a yau din.

  8. Gwamnatin Najeriya ta ce ta samu kuɗin gina titin jirgi daga Maiduguri zuwa Aba

    Gwamnatin Najeriya ta ce ta samu duka kuɗin gudanar da aikin gina layin dogo daga birnin Maiduguri na jihar Borno zuwa garin Aba na jihar Abiya.

    Ministan Sufuri Saidu Alkali ne ya bayana hakan a yau yayin wani taron bita da ake gudanarwa a Kaduna, kamar yadda wata sanarwa daga ofishinsa ta bayyana.

    "Layin dogon mai tsawon kilomita 1,443 zai ratsa jihohin Borno, da Yobe, da Gombe, da Bauchi, da Filato, da Kaduna, da Nasarawa, da Binuwai," in ji sanarwar da kakakin ministan Rabiu Ibrahim ya fitar.

    Sai dai sanarwar ba ta bayyana inda gwamnatin ta samo kudin ba. Akasarin manyan ayyuka masu tsada kamar wannan akan yi su ne ta hanyar bashi ko kuma lamuni.

    Ministan ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya ta gyara layin dogo na dakon kaya tsakanin Legas zuwa Kano.

  9. Trump zai sanya harajin kashi 25 kan kayayyaki daga Indiya

    Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa daga ranar 1 ga Agusta, zai ƙaƙabawa Indiya harajin kashi 25 kan kayayyakin da take shigowa da su zuwa Amurka.

    Ya kuma ce za a ƙara wani hukunci na musamman saboda Indiya na sayen makamashi da makaman yaƙi daga Rasha.

    A wata sanarwa da ya wallafa a dandalinsa na Truth Social, Trump ya bayyana Indiya a matsayin abokiyarta amma ya zarge ta da sanya haraji mai yawa — wanda ya kira "mafi tsauri a duniya".

    Ya kuma soki cinikayya tsakanin Indiya da Rasha, musamman a lokacin da duniya ke ƙoƙarin ganin Rasha ta dakatar da yaƙin da take yi a Ukraine.

    Babu wani martani daga gwamnatin Indiya a halin yanzu, duk da cewa suna tattaunawa da Amurka kan yarjejeniyar kasuwanci.

    A bara, Amurka ta yi asarar dala biliyan 45.8 wajen cinikayya da Indiya.

  10. NNPCL ya musanta sayar da matatar mai ta Fatakwal

    Babban kamfanin man fetur na Najeriya, NNPCL ya musanta raɗe-raɗin sayar da matatar mai ta birnin Fatakwal.

    Shugaban kamfanin Bashiru Ojulari ne ya bayyana haka a wani taron tuntuɓa da kamfanin ya shirya a shalkwatarsa da ke Abuja.

    Ojulari ya ce NNPCL ba shi da aniyar sayar da wata matata mallakinta, sai dai ma ƙoƙarin gyara su domin yin daidai da zamani.

    An fara raɗe-raɗin sayar da matatar ne bayan wata hira da shugaban kamfanin ya yi a taron OPEC a birnin Vienna na ƙasar Austria a farkon watannan.

    A lokacin Ojulari ya yi wata hira da jaridar Bloomberg, kan batun sayar da matatar inda ya ce “komai zai iya faruwa”.

    Tun daga wancan lokacin ne aka yi ta maganganu game da makomar matatar.

  11. An yi arangama tsakanin sojojin Sudan ta Kudu da na Uganda

    Sojoji daga Sudan ta Kudu da na Uganda sun yi musayar wuta a kusa da iyakarsu lamarin da ya yi sanadin rasa rayukan akalla mutum shida.

    Mai magana da yawun rundunar sojin Uganda ya ce sojojin Sudan ta Kudu sun tsallaka iyakar Uganda ta bangaren yankin West Nile sannan kuma sun ki barin wajen.

    Ya ce an kashe daya daga cikin sojojin kasarsu. Jami'ai a Juba sun ce an yi musayar wutar ne a iyakar inda aka kashe musu sojoji biyar.

    Kasashen biyu dai sun jima suna da kyakkyawar alaka a tsakaninsu. Shugaban Uganda Yoweri Museveni ya taimakawa 'yan tawayen Sudan ta Kudun wajen kwatar 'yancinsu daga Sudan.

  12. Mamakon ruwan sama ya haifar da ambaliya a Maiduguri

    Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno sun tsere daga gidanjensu bayan wata mummunar ambaliya ta auka wa wasu sassan birnin sakamakon ruwan sama mai ƙarfin gaske.

    Rahotonni daga birnin sun ce lamarin ya shafi unguwannin Damboa road da Moduganari Ngomari da Bulunkutu Abuja da sauransu.

    An dai wayi gari da mamakon ruwan sama a faɗin birnin, lamarin da ya haifar da ambaliyar.

    A shekarar da ta gabata ne aka samu wata mummunar ambaliya da ta raba fiye da mutum miliyan guda da muhallansu a birnin na Maiduguri.

  13. 'Ƙarin mutum bakwai sun mutu saboda yunwa a Gaza'

    Ma'aikatar lafiyar Hamas ta ce a cikin sa'oi 24 da suka gabata ƙarin wasu mutum bakwai sun mutu sakamakon rashin abinci mai gina jiki.

    Ma'aikatar ta rawaito cewa mutanen da suka mutu sakamakon yunwa tun bayan fara yaƙin Gaza sun kai 151.

    Yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare a sassan yankin wanda Isra'ilan ta toshe muhimman hanyoyin shigar da kayan agaji, masu aikin ceto sun ce an kashe karin wasu Falasdinawa 14.

    Yawancinsu an kashe su ne a lokacin da suke jiran karɓar kayan agaji.

    Isra'ila dai na ɗora alhakin hakan akan Hamas.

  14. Yara 13 sun mutu a Sudan saboda rashin abinci

    Jami'an lafiya a Sudan sun ce yara 13 sun mutu sakamakon tsananin ƙarancin abinci a sansanin 'yan gudun hijira da ke jihar gabashin Darfur.

    Kungiyoyi likitoci a Sudan sun ce yanayin jin kai a sansanin Lagawa na ƙara tsananta inda rahotanni ke cewa ana samun ƙaruwar rashin abinci mai gina jiki musamman a tsakanin ƙananan yara.

    Sansanin 'yan gudun hijirar na ɗauke da aƙalla mutum 7,000, kuma yana fuskantar hare-hare daga ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai akai-akai.

    A farkon shekarar da muke ciki ne aka ayyana masifar yunwa a wasu sassan na Darfur inda mayaƙan RSF suka yi wa ƙawanya tsawon shekara guda.

  15. Sanatocin arewacin Najeriya sun yi allah wadai da kisan mutane a Zamfara

    Ƙungiyar sanatocin arewacin Najeriya ta yi allah wadai da kisan gillar da aka yi wa wasu fararen hula 35 a ƙaramar hukumar Ƙauran Namoda a jihar Zamfara.

    Cikin wani saƙon jaje da ƙungiyar ta aike ranar Laraba a Abuja, shugaban ƙungiyar Sanata Abdulaziz Yar’adua,ya jajanta wa al'ummar yankin musamman iyalan waɗanda lamarin ya shafa.

    A farkon makon nan ne ƴanbindiga suka yi wa su mutanen yankan rago duk kuwa da biyan kuɗin fansa da aka ce iyalansu sun yi domin kuɓutar da su.

    Jihar Zamfara na daga cikin jihohin Najeriya da ke fama da ayyukan ƴanbindiga masu sace mutane domin neman kuɗin fansa.

    Wasu masu sharhi dai na ci gaba da sukar gwamnati da masu ruwa da tsaki a harkar tsaron ƙasar kan rashin samar da zaman lafiya a yankin.

  16. Girgizar ƙasar Rasha: 'Ba wanda ya rasa ransa'

    Fadar gwamnatin Rasha ta yi martani a hukumance kan girgizar ƙasar da ta auka wa wani yankin gabashin ƙasar.

    Kakakin fadar gwamnatin ƙasar, Dmitry Peskov ya shaida wa manema labarai cewa ''duka gargaɗin'' da gwamnatin ƙasar ta fitar ta taimaka matuƙa.

    ''Mun gode wa Allah babu wanda ya rasa ransa sada wannan bala'i'', kamar yadda ya bayyana.

    Girigizar ƙasar mai ƙarfin maki 8.8 ta kasance mafi muni da aka taɓa gani cikin gomman shekaru.

    Bala'in ya haifar da ambaliya ruwa sakamakon janyo igiyar ruwa daga tekun Pacific.

  17. Mummunar girgizar ƙasar Rasha ta haifar da guguwar tsunami a wasu ƙasashe

    Wata mummunar girgizar ƙasa da ba a taɓa ganin irinta ba cikin shekaru ta auka wa wasu yankunan gabashin Rasha.

    Girgizar ƙasar mai ƙarfin maki 8.7 ta shafi nisan kilomita 126 daga yankin Petropavlovsk zuwa Kamchatsky, tare da zurfin kilomita 18 a cewar hukumar binciken yanayin ƙasa ta Amurka.

    Ministan kula da ayyukan jin ƙai na yankin Sergei Lebedev,ya ce bala'in ya haifar da guguwar tsunami da ta haifar da mummunar ambaliya a jihar Kamchatka.

    Gwamnan jihar Kamchatka, Vladimir Solodov ya ce "girgizair ƙasar ta kasance mafi muni cikin gomman shekaru.

    Girgizar ƙasar ta kuma haifar da gargaɗin samun ambaliya a wasu yankunan tekun Pacific da ya shafi wasu sassan ƙasashen gabashin Asiya da Turai da Amurka.

    Tuni dai hukumomin Japan suka umarci aƙalla mutum miliyan biyu su fice daga wasu yankunan ƙasar sakamakon fargabar samun ambaliya bayan girgizar ƙasar.

  18. An sanya dokar ta-ɓaci a wani yankin Rasha bayan ambaliya

    Hukumomi a yankin Sakhalin na ƙasar Rasha sun ayyana dokar ta ɓaci a tsibirin Kuril da ke arewacin ƙasar da gundumar Severo-Kurilsk sakamakon mummunar ambaliya ruwa ta auka wa yankunan.

    Magajin garin tsibirin Kuril, Alexander Ovsyannikov ya ce an kwashe ''duka mutanen'' da ke yankin.

    Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito magajin garin na cewa duka mutanen yankin a yanzu suna wurin da ya kira tudun mun-tsira.

    An yi ta yaɗa hotuna da bidiyon yadda ambaliyar ke tafiya da motoci da gidaje a garin Severo-Kurilsk mai tashar jiragen ruwa.

  19. IMF ya sabunta hasashen bunƙasar tattalin arzikin Najeriya

    Asusun Bayar da Lamuni na Duniya, IMF ya sabunta hasashensa kan bunƙasar tattalin arzikin Najeriya na shekarar 2025 da 2026.

    IMF ya bayyana sabon hasashen a watan Yulin da muke ciki wanda a ciki ya yi ƙiyasin samun ƙarin bunƙasar tattalin arzikin Najeriya.

    Asusun ya yi hasashen samun jarin bunƙasar tattalin arzikin Najeriya da kashi 3.4 a 2025, ƙari a kan hasashen kashi 3.0 da ya yi a watan Afrilu.

    Haka kuma IMF ya yi hasashen cewa tattalin arzikin Najeriya zai samun ƙarin baunƙasa da kashi 3.2 a 2026, saɓanin hasashen kashi 2.7 da ya yi a watan na Afrilu.

  20. Ma'aikatan jinya 25,000 sun fara yajin aiki a Najeriya

    Ƙungiyar ma'aikatan jinya da unguzomomi ta Najeriya ta fara yajin aikin gargaɗi na mako guda a faɗin ƙasar.

    Ƙungiyar mai mambobi aƙalla 25,000 ta ca ta fara yajin aikin ne domin nuna rashin jin daɗinta kan rashin albashi mai kyau da ƙarancin ma'aikata da rashin biyansu alawus da kuma rashin kariya a wajen ayyukansu.

    Shugaban ƙungiyar, Morakinyo Rilwan ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa sun yanke shawarar fara yajin aikin ne bayan ƙarewar wa'adin kwanaki 15 da ƙungiyarsu ta bai wa gwamnati.

    Yajin aikin dai ya shafi ma'aikatan jinya da ungozomomin da ke aiki a asibitocin gwamnatin tarayya a cewar shugaban ƙungiyar.

    Mataƙin ma'aikatan jinyar na zuwa ne yayain da ake ci gaba da takun saƙa tsakanin ƙungiyar likitocin ƙasar da gwamnatin tarayya kan walwalar likitocin.