Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wane ne sabon sarkin Gusau Abdulkadir Ibrahim Bello?
Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da naɗin Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello a matsayin sabon sarkin Katsinan Gusau.
Hakan ya biyo bayan rasuwar mahaifinsa Dr Ibrahim Bello a daren Juma'a 25 ga watan Yulin 2025 bayan doguwar jinya a wani asibiti da ke Abuja, babban birnin Najeriya.
Alhaji Abdulkadir zai maye gurbin ne a matsayin Sarki na 16 na masarautar.
Sanarwar da sakataren gwamnatin jihar Zamfara, Malam Abubakar Mohammad ya fitar ta ce an yi amfani da dokoki da tanade-tanaden doka ne wajen amincewa da naɗin, wanda masu zaɓen sarkin masarautar suka zaɓa.
An zaɓi sabon sarkin ne daga cikin sama da ƴaƴa 20 da mahaifinsa ya bari.
Tarihin Abdulkadir Bello
Sabon sarkin, wanda za a riƙa yi wa laƙabi da Abdulkadir II, shi ne babban ɗa da ke raye ga marigayi tsohon sarki Dr Ibrahim Bello, kuma kafin naɗa shi, shi ne Bunun Gusau.
An haife shi ne a ranar 1 ga watan Disamba, 1977.
Ya yi karatun firamare da sakandare a garin Gusau, sannan ya yi karatun digiri a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, inda ya karanta kimiyyar da ta shafi fasahar rayuwa da tsirrai (Biotechnical engineering).
Kafin naɗin nasa, Sarki Abdulƙadir II na aiki ne a hukumar kula da asibitoci da ke ƙarƙashin ma'aikatar lafiya ta jihar Zamfara.
Gwamna Lawal ya taya sabon sarkin murna, sannan ya yi kira gare shi da ya yi koyi da magabatansa, musamman ganin shi tsatson Malam Sambo Ɗan Ashafa ne.
Ƙalubalen da ke gaban sabon sarki
A tattaunawarsa da BBC, sakataren masarautar Gusau, Sambo A. Sambo ya ce babban abin da ya kamata sabon sarkin ya mayar da hankali a kai shi ne haɗa kan ƴan'uwa.
"Tun daga lokacin zaɓe, zuwa lokacin da aka tura wa gwamna sunan mutum uku, masu zaɓen sarki da ɗaukacin fada kowa ya goyi bayan nadin.
"Ya (sabon sarkin) yi kira ga ƴan'uwansa cewa su haɗa kai a tafi tare, gidan sarautar ba nasa ba ne shi kaɗai," in ji Sambo.
Sakataren na masarautar Gusau ya ce sabon sarkin ya samu tarbiyya mai kyawu daga tsohon sarki Ibrahim Bello.
"Mutum ne mai yawan haƙuri," kamar yadda ya shaida wa BBC.