ANPP na neman a bar mata mataimakin shugaban ƙasa: Ko haɗakar APC na rawa ne?

    • Marubuci, Ahmad Bawage
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Masu nazari kan siyasa na ganin cewa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya na neman bin sahun manyan jam'iyyun adawa na ƙasar da ke fama da rikice-rikicen cikin gida.

Hakan na zuwa ne bayan da tsagin tsohuwar jam'iyyar ANPP - da ke cikin haɗakar da ta samar da APC - ta hakikance kan cewa wajibi ne a bar mata kujerar mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Ƴaƴan tsohuwar jam'iyyar ta ANPP sun gargaɗi shugaba Bola Tinubu da kada ya kuskura ya ɗauki wani wanda ba ɗan tsohuwar jam'iyyar ba.

Ɓangaren na ANPP waɗanda suka yi iƙirarin cewa su ne na biyu mafi girman tasiri a lokacin da aka yi haɗaka a 2013 da ta haifar da jam'iyyar APC, sun nuna fushinsa kan cewa an yi watsi da ƴaƴansu tsawon shekaru.

A wani taron manema da suka gudanar a Abuja ranar Litinin, ɓangaren na tsoffin mambobin jam'iyyar ANPP, sun buƙaci cewa ya kamata a tafi da su ba tare da nuna bambanci ba daga gwamnatin shugaba Bola Tinubu, inda suka ce babu abin da aka yi har yanzu bayan shiga haɗaka da kuma taimaka wa APC samun nasara tun 2015.

Sun fitar da gargaɗi mai tsauri cewa muddin ba a bar musu kujerar mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen 2027 ba, to za su fara tunani game da zama ko ficewa daga haɗakar ta APC.

An yi watsi da mu - CPC

A ɗaya gefen, tun da farko, ɓangaren jam'iyyar CPC da suka shiga haɗaka wajen zama jam'iyyar APC, sun buƙaci cewa a ba su kujerar shugaban jam'iyyar APC na ƙasa bayan murabus ɗin Abdullahi Umar Ganduje.

Duk da cewa jam'iyyar APC ta sanar da naɗa Farfesa Nentawe Yilwatda a matsayin sabon shugabanta, ɓangaren ƴan tsohuwar CPC sun yi ta fafutukar ganin an bai wa ɗaya daga cikin mutanenta, Sanata Tanko Al-Makura tun da farko.

Masu sharhi dai na cewa wannan buƙatar da CPCn suka yi, ya nuna ƙaruwar ɓaraka da ke kunno kai cikin mambobin jam'iyyar mai mulki, waɗanda ke ganin an yi watsi da su a rabon muƙamai karkashin gwamnatin Tinubu.

Lamarin ya yi kamari ne bayan da wasu ƴan gani kashe-nin CPC suka yi barazanar soke goyon baya da suke bai wa jam'iyyar, inda suka ce an yi watsi da su da daɗewa.

Haka ma, ana ganin irin rikicin cikin jam'iyyar ne ya janyo ficewar jigogin jam'iyyar da ke alaƙa da tsohuwar CPC, irin su tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai, da tsohon attoni-janar Abubakar Malami da kuma tsohon sakataren gwamnatin tarayya Babachir Lawal.

Me hakan ke nufi?

Masanin kimiyyar siyasa a Najeriya kuma malami a kwalejin share fagen shiga jami'a da ke Kano, Kabiru Sufi ya ce bai kamata shugabanni su riƙa yin watsi da buƙatun da irin waɗannan mambobi suke bijiro da su ba.

Ya ce samun irin waɗannan ƙungiyoyi a cikin manyan jam'iyyu musamman waɗanda ke taka rawa a shugabanci a matakai da dama ba bakon abu ba ne.

"Yawanci ana kafa irin waɗannan ne don cimma muradunsu da dafa wa wasu masu riƙe da muƙamai baya," in ji Malam Kabiru Sufi.

Ya ce suna bijiro da irin waɗannan buƙatu ne idan suka ga cewa in sun rasa madafun iko ba za a ga tasirinsu ba.

"Yawaitarsu yakan ɗauke hankalin shugabanni idan kowa ya bijiro da buƙatarsa. Amma da wuya a samu waɗanda suke ficewa cikin jam'iyyar da suke ciki," in ji Sufi.

'Rashin biya musu buƙatu zai raunana karfin jam'iyyar'

Masanin kimiyyar siyasan ya ƙara da cewa duk lokacin aka kasa biya wa mambobin buƙatunsu, lamarin zai iya janyo wa jam'iyyar matsala.

"Wasu za su iya fusata har ma su fice daga jam'iyyar ta APC idan aka ƙi biya musu buƙatu.

"Hakan zai iya raunana jam'iyyar, kuma wasu za su iya yin zagon ƙasa ko da ba su fice ba," in ji Kabiru Sufi.

Ya ce abu ne mai kyau ba duk lokacin da suka zo da buƙatu a biya musu ko kuma a musanya musu da wata.

Ta yaya APC za ta iya warware wannan rikici?

Malam Kabiru Sufi ya ci gaba da cewa abin da ya kamata shugabannin jam'iyyar APC mai mulki su yi shi ne, ci gaba da bijiro da dabarun da za su biya wa irin waɗannan mambobi buƙatunsu ko musanya musu da wani abu n adaban.

"Saboda suna da ƙarfi kuma suna da muhimmanci duk da cewa haɗin-kan nasu bai cika tabbatuwa ba. Ba a cika son wofantar da buƙatunsu ba," in ji Sufi.

Ya ƙara da cewa bijirewarsu za ta iya kawo jam'iyyar nakasu ba kaɗan ba.

Sai dai ya ce yawan bijiro da buƙatun da suke yi ɗin yana ɗauke hankalin shugabanci na jam'iyya ko al'umma.

"Shi ya sa wani lokaci dole sai an yi musu abin da suke so.