Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Litinin 10/11/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Litinin 10/11/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir da Isiyaku Muhammed da Annur Muhammad

  1. Sojoji sun kuɓutar da mutum 86 da aka yi garkuwa da su a Borno

    Soja

    Asalin hoton, Other

    Rundunar sojin ƙasan Najeriya ta ce sojojinta sun samu nasarar kuɓutar da mutum 86 daga masu garkuwa da mutane, sannan ta kama ƴanbiniga da masu taimaka musu guda 29 a sassa daban-daban na jihar Borno da ke arewa maso gabas.

    A wata sanarwa da kakakin aikin soji na musamman na Hadin Kai, Sani Uba ya fitar, ya ce sojojin bataliya ta musamman ta 135 a ƙarƙashin sashe na 2 ne suka yi artabu da ƴan Boko Haram a ranar 9 ga watan Nuwamba a yankin Dutse Kura.

    "Ƴan Boko Haram sun kai hari ne kan matafiya a hanyar Buratai zuwa Kamuya. Nan ne sojojinmu suka kai ɗauki, wanda ya sa maharan suka tsere, amma sai sojojin suka bi bayansu a hanyar zuwa Mangari har suka ci ƙarfinsu," kamar yadda sanarwar ta nuna.

    Ya ce daga bisani sojojin sun baza ƙomarsu a dazukan, inda suka samu nasarar gano sansanin mayaƙan guda 11, "inda muka ceto mutum 86 ciki har da mata da ƙananan yara, sannan muka ƙwato bindigar AK-47 da harsasai da sauran makamai."

  2. Kashe-kashe sun ragu da kashi 81 a Najeriya - Gwamnati

    Tinubu

    Asalin hoton, PRESIDENCY NG

    A Najeriya, Gwamnatin kasar ta ce alkalummanta da ta tattara sun nuna ana samun nasarar shawo kan matsalar tsaron da ta addabi sassan kasar da sama da kashi 80 cikin dari.

    Wannan na zuwa yayin da gwamnatin Birtaniya ta yi gargadi ga 'yan kasarta da su kaurace wa yin balaguro a wasu sassan Najeriya bayan nuna damuwa kan karuwar hare-haren ta'addanci da satar mutane.

    Jihohin da gwamnatin Birtaniya ta yi gargadin sun hada da Borno da Yobe Katsina da Zamfara da Adamawa da Gombe da kuma wasu jihohin na kudanci.

    Sai dai gwamnatin Najeriya ta ce alkalummanta na shekarar 2025 sun nuna ana samun saukin hare-haren da ake kai wa da satar jama'a.

    Gwamnatin ta ƙara da cewa daga shekarar 2024 zuwa yanzu, ta samu nasarar gabatar da ƴanta'adda da ƴanbindiga sama 124 a kotu da aka yanke wa hukunci, sannan ta ce akwai wasu kamar jagororin Ansaru da waɗanda suka kai hari a asibitin Owo a 2022 da na Yelwata da sauransu da suke fuskantar shari'a.

  3. Likitoci sun zargi mayaƙan RSF da ɓoye gawarwakin fararen hula a Sudan

    rRSF

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata kungiyar likitocin Sudan ta zargi dakarun RSF da kwashe daruruwan gawarwaki a titunan El Fasher a yankin domin boye ta'asar da ake zargin an yi wa fararen hula.

    Kugiyar Lkitocin ta ce an binne wasu gawarwakin a makeken kabari yayin wasu kuma aka kone.

    Likitocin sun kuma yi Allah wadai da abin da suka kira kisan kiyashi tare da kiran gudanar da bincike.

    Yakin Sudan wanda ya barke a 2023 ya kashe dubban mutane tare da raba mutum miliyan 12 da gidajensu

  4. Buɗewa

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Litinin, ranar da Hausawa ke cewa ko narasa na tsoronta.

    A yau ma za mu ci gaba da kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Ku kasance tare da mu.