Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Litinin 10/11/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Litinin 10/11/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir da Isiyaku Muhammed da Annur Muhammad

  1. Rufewa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labaran, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

    Amma kafin nan, yanzu a nan muke cewa mu kwana lafiya.

  2. Lebanon ta saki Hannibal Gaddafi bayan shekara 10 da tsare shi

    Hannibal Gaddafi

    Asalin hoton, AFP

    Hukumomin Lebanon sun saki Hannibal Gaddafi, ƙaramin ɗan tsohon shugaban Libya, Marigayi Muammar Gaddafi, bayan kusan shekara 10 a tsare ba tare da shari'a ba.

    An sake shi ne bisa sharaɗin belin da ya ƙunshi biyan dala duba 900.

    A shekarar 2015 ne hukumomin Lebanon suka tsare Hannibal Gaddafi, bayan da suka zarge shi da ɓoye bayanai kan wani fitaccen malamin shi'a da ya ɓace a Libya a 1978, a lokacin Hannibal na shekara biyu kawai a duniya.

    Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama sun sha musanta zarge-zargen da ake yi wa Hannibal.

  3. Uwargidan tsohon shugaban ƙasar Gabon na fuskantar shari'a

    Uwargidan tsohon shugaban ƙasar Gabon, Sylvia Bongo tare da ɗanta, Noureddin Bongo Valentin na fuskantar shari'ar da ta shafi zargin cin hanci da almundahana a birnin Libreville

    An ci gaba da gudanar da shari'a a kotun ɗaukaka ƙarar ƙarar, a bayan idon mutanen biyu, saboda rashin halartarsu kotun.

    A watan Mayun 2025 aka bayar da belin mutanen tare da basu damar tafiya zuwa birnin London.

    Rahotonni sun ce mutane tara cikin 12 abokan tsohon shugaban gabon, Ali Bongo - da su ma ake yi musu shari'ar - sun halarci zaman kotu

    Sylvia Bongo tare da ɗanta, Noureddin Bongo, sun musanta zarge-zargen da suka bayyana da rashin adalci.

  4. Wata ƙungiyar ƴanjarida na son Isra'ila ta dakatar da hare-hare kan mambobinta

    Wata ƙungiya mai wakiltar kafofin yaɗa labarai na duniya a Isra'ila da yankunan Falasɗinawa ta yi kira ga hukumomin Isra'ila su ɗauki matakin gaggawa na dakatar da hare-hare kan ƴanjarida da Yahudawa ƴan kama-wuri-zauna ke yi musu a Gabar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye.

    Ƙungiyar mai suna 'Foreign Press Association' na kafa hujja da wasu hare-hare biyu da aka kai wa ƴanjaridar ƙasashen waje da suka faru lokacin girbe ƴaƴan man zaitun a wannan shekara.

    Ƙungiyar ta ce ana kai wa ƴanjarida na ciki da na waje hare-hare, saboda ɗaukar labaran cutarwar da ake yi wa Falasɗinawa.

    Sojojin Isra'ila sun ce sun yi Allah wadai da cutarwar, sannan za su ci gaba da yin aiki domin tabbatar da tsaro a yankin.

  5. Wani fursunan da ke yajin cin abinci ya zargi jami'an gidan yari da muzguna masa

    Wani tsohon soja na musamman na Ukraine, wanda ke cikin kwana na 10 na yajin cin abinci a wani gidan yari da ke Italiya, ya zargi jami'an gidan yarin da muzguna masa domin tilasta masa amincewa da dasa abin fashewa a bututun iskar gas ɗin Nordstream na Rasha.

    An kama Serhiy Kuznetsov ne a watan Agusta bisa umurnin kama shi daga Jamus wadda ke son a tasa ƙeyarsa zuwa Rasha domin ya fuskanci tuhume-tuhumen da ake masa na ta'addanci.

    Ana tsare da shi ne a wani gidan yari mai tsatsauran matakan tsaro, a keɓance, kuma ba a bari ya motsa jiki yadda ya kamata.

    Sai dai mista Kuznetsov ya ce yin hakan ba zai sa ya amince da yin wani laifi ba.

  6. Shugaban Syria na ganawa da Trump

    Shugaban Syria, Ahmed al-Sharaa na tattaunawa da Shugaba Trump na Amurka.

    Ana sa ran tataunawar za ta ƙunshi batun shigar da Syria ƙawancen yaƙi da IS da Amurka ke jagoranta, da kuma bu katar Syria ya ɗage mata tarin takunkuman da duniya ta ƙaƙaba mata.

    Tattaunawar gagarumar nasara ce ga Mista Sharaa - wanda a baya ya taɓa jagorantar wata ƙungiyar yantawaye mai alaƙa da al Qaeda, inda har aka sanya ladan dala miliyan 10 da wanda ya taimaka aka kama shi.

    Ƙasa da shekara guda kenan, tun bayan da ƙawancen ƙungiyoyin ƴantawaye suka kawo ƙarshen yaƙin basasar ƙasar na tsawon shekara 13, ta hanayar tumɓuke shugaba Bashar al-Assad

  7. Mutum takwas sun mutu bayan wata fashewa a Delhi

    Fashewa

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƴansanda a Delhi, babban birnin Indiya sun ce aƙalla mutum takwas sun mutu bayan wata fashewar a kusa a birnin da ya fi kowane yawan al'umma a ƙasar.

    Jami'an yansandan sun ce aƙalla mutum 19 ne suka jikkata a fashewar da ta auku a kusa da wani fitaccen gini da aka gina tun ƙarni na 17.

    Ƴansandan sun ce har yanzu ba su gano abin da ya haifar da fashewar ba.

    Wasu bidiyoyi sun nuna hayaƙin motocin da suke ƙonewa ya turnuƙe saman inda lamarin ya faru.

  8. Donald Trump ya yi barazanar maka BBC a kotu

    Trump

    Asalin hoton, EPA

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya aike wa BBC wasiƙar gargaɗin ɗaukar matakin shari'a a kanta game da wani rahoto na musamman da ya jirgita wasu jawabansa gabanin magoya bayansa su afka wa ginin majalisar dokokin Amurka a watan Janairun 2021.

    Rahoton na musamman da BBC ta shirya ya gwama wasu jawaban Trump biyu wuri guda a wani abu da shugaban BBC ya bayyana da kuskuren da ya haifar da ɗaukar mataki.

    Lamarin ya tilasta wa shugaban BBC da shugabar sashen labarai ajiye ayyukansu, bayan da suka musanta cewa BBC tana nuna son kai a labaranta.

  9. EFCC ta ayyana neman tsohon gwamnan Bayelsa ruwa-a-jallo

    Tsohon gwamnan Bayelsa

    Asalin hoton, Timipre Sylva/X

    Hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da Rashawa a Najeriya ta ayyana neman tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Timipre Sylva ruwa a jallo.

    Cikin wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafinta na X ta ce tana neman Mista Sylva ne bisa zargin wata badaƙalar kuɗi da yawansu ya kai dala miliyan 14.8.

    EFCC ta zargi tsohon gwamnan ne da karkatar da kuɗin da aka yi niyyar amfani da su wajen gina matatar man fetur a ƙasar.

    Hukumar ta ce wata kotu ce a jihar Legas ta bayar da sammacin kama tsohon ƙaramin ministan na man fetur na Najeriya.

    Hukumar yaki da cin hancin ta kuma buƙaci duk wanda yake da bayanan da za su taimaka wajen kama tsohon gwamnan ya gabatar mata da su.

  10. Ba a nuna son kai a labaran BBC - Tsohuwar shugabar sashen labarai

    Shugabar sashen labarai ta BBC, da ta yi murabus ta sake jaddada cewa ba a nuna son kai a labaran BBC, bayan ta ajiye aiki sakamakon fuskantar suka kan wani shirin BBC da aka sauya wani angare na jawabin Donald Trump.

    Deborah Turness, ta shaida wa ma'aikatan BBC cewa ta ajiye aikin ne saboda ita ce wadda komai ya rayata a wuyanta.

    Shugaban kafar BBC ya nemi afuwar yan majalisar Birtaniya kan abin da ya kira kuskure wajen yanke hukunci.

    Ana ta samun ra'ayoyin mabanbanta a Birtaniya game da kafar yaɗa labaran, inda wasu ke kiran a kawo sauyi, wasu kuma na ganin bi-ta-da-kullin siyasa ne kawai.

  11. Ƴar tsohon shugaban Afirka ta Kudu, Zuma ta ƙaryata zargin tayar da tarzoma

    Zuma

    Asalin hoton, Getty Images

    An fara zaman shari'ar ƴar tsohon shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma, a wata babbar kotun kasar da ke Durban.

    Ana zargin Duduzile Zuma-Sambudla da laifin amfani da soshiyal media wajen tunzura tashin hankali lokacin wata zanga-zanga a shekara hudu da su ka gabata bayan an kama mahaifinta kan zargin saba wa umurnin kotu bisa wani bincike kan cin hanci, inda aka ruwaito kusan mutum 350 sun mutu lokacin zanga-zangar.

    Wakiliyar BBC ta ce Duduzile Zuma-Sambudla ta musanta aikata laifin, kuma lauyanta ya ce hujjojin gwamnati ba su da karfi.

    Miss Zuma Sambudla ta ce ana kokarin amfani da shar'iar ne wajen yi wa mahaifinta ramuwar gayya ta siyasa saboda ya kirkiro jam'iyyarsa kuma ya yi adawa da jam'iyyar African National Congress.

  12. Ƴanbindiga sun yi garkuwa da mata shida a Kano

    Bindiga

    Asalin hoton, NPF

    A Najeriya, wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari garin Ƴankwaɗa da ke Karamar Hukumar Shanono ta Jihar Kano, inda suka yi awon gaba da mata shida ciki har da masu shayarwa, tare da harbin mutum ɗaya.

    Wannan na zuwa ne mako guda bayan kai irin wannan harin a wasu kauyuka a ƙananan hukumomin Shanono da Tsanyawa, da suka yi iyaka da Jihar Katsina wadda da taɗe tana fama da hare-haren ‘yan bindiga.

    Wani mazaunin yankin da abin da ya faru da ya zanta da BBC ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce maharan sun isa garin ne da misalin ƙarfe na 10:30 zuwa 11 na dare.

    "Wannan karon sun canja salo ne, inda suka shigo a ƙafa maimakon a babura da suka zaba zuwa domin su ɓatar da kama. Sai da suka shiga tsakiyar gari sai suka buɗe wuta. Da mutane suka watse, sai suka shiga gida-gida suka kwashe mata guda shida ciki har da masu shayarwa, sannan suka harbi wani mutum ɗaya a gidansa."

    Sai dai ya ƙara da cewa daga cikin matan da aka kwasa, guda biyu sun koma, "amma sun tafi da guda huɗu daga cikinsu. Sannan wanda aka harba yana jinya."

    BBC ta yi yunƙurin jin ta bakin kakakin rundunar ƴansanda na jihar Kano, amma haƙarta bai cimma ruwa ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

  13. Kotu ta saki Sarkozy makonni kaɗan bayan ɗaure shi

    Sarkozy

    Asalin hoton, Reuters

    Wata kotu a Paris ta saki tsohon shugaban Faransa Nicolas Sarkozy daga gidan yari makonni kaɗan bayan yanke masa hukuncin shekara biyar a kurkuku.

    An yanke masa hukunci ne bayan samunsa da laifin karɓar kuɗi daga hannun tsohon shugaban ƙasar Libya, Muammar Gaddafi domin amfani da shi a zaɓen.

    Yanzu tsohon shugaban ƙasar zai kasance a ƙarƙashin kulawar kotun kafin lokacin da zai ɗaukaka ƙara domin kotun gaba.

    Sarkozy ya bayyana wa kotun a wayar bidiyo cewa yana "shan wahala" a zamansa a gidan yari, sannan ya nanata cewa bai aikata laifin komai ba.

  14. Trump ya yi afuwa ga wasu abokan siyasarsa a matakin tarayya

    Trump

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Amurka Donald Trump ya yi afuwa ga wasu mutane na hanun damarsa da ake zargi da yunƙurin yin tsaiko ga zaɓen Amurka na 2020.

    Daga cikin waɗanda ya yi wa afuwar akwai tsofaffin lauyoyinsa, Rudy Giuliani da Sidney Powell da tsohon shugaban ma'aikatansa Mark Meadows kamar yadda ma'aikatar shari'a ta ƙasar ta bayyana.

    Wannan afuwar na nufin ba za su fuskanci hukunci ba kn zarge-zargen da suke fuskanta a matakin gwamnatin ƙasar, amma za su iya fuskantar hukunci a jihohinsu.

  15. 'Rikici tsakanin Boko Haram da ISWAP ya yi ajalin mayaƙa'

    bOKO HARAM

    Asalin hoton, others

    Rahotanni daga yankin arewa maso gabashin Najeriya na nuna cewa rikicin cikin gida tsakanin ɓangaren Boko Haram da tsagin ISWAP ya yi sanadiyar mutuwar aƙalla mayaƙa guda 200 a tsakaninsu.

    Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa ricikin ya yi ƙamari ne a tsakanin ɓangarorin ƙungiyar guda biyu a yankin Dogon Chiku da ke gaɓar Tekun Chadi a ranar Lahadi, wanda ya kasance ɗaya daga rigingimu da ya fi zafi saboda bambancin ra'ayi.

    "Mun ƙirga aƙalla gawarwaki guda 200," in ji wani mai suna Babakura Kolo a zantawarsa a AFP.

    Wani tubabben ɗan Boko Haram da ke bibiyar harkokinsu da ya ce a kira shi da suna Saddiku ma ya tabbatar da rikicin, inda ya ce, "an kashe aƙalla ƴan ISWAP 200 a rigimar, sannan an kwashe muku makamai da dama, sannan aka kashe ƴan tsagin Boko Haram guda huɗu."

    Ya ƙara da cewa wannan ne rigima mafi zafi da aka yi a tsakanin ɓangarorin mayaƙan guda biyu tun bayan rabewarsu saboda saɓanin fahimta a shekarar 2016.

    Wata majiyar tsaro ma ta tabbatar da aukuwar rigimar, inda ta ce "muna da bayanan sirri kan rigimar, kuma mun samu labarin mutuwar mayaƙa sama da 150, wanda kuma labari ne mai kyau a wajenmu.

  16. Ya kamata jami'o'i masu zaman kansu su shiga ASUU - Shugaban NLC

    ASUU

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya NLC, Joe Ajaero ya yi kira da a janyo jami'o'in Najeriya masu zaman kansu su shiga cikin ƙungiyar ASUU.

    Ajaero ya buƙaci ƙungiyar ASUU ta fara tattaunawa da shugabannin jami'o'in na Najeriya domin fahimtar da su buƙatar shiga ƙungiyar domin a gudu tare a tsira tare, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

    Ajaero ya bayyana haka ne a ranar Lahadi a lokacin da yake jawabi a lokacin da aka tattaunawa da shugaban ASUU, Farfesa Christopher Piwuna a shirin Toyin Falola.

    Shugaban na NLC ya ce "dole a daina cin zarafi tare da yi wa mambobin ASUU," in ji shi, sannan ya bayyana mamakinsa kan yadda gwamnatin ta gaza wajen tabbatar da alƙawarin da ta sa hannu tun a shekarar 2009.

    Ya ce asali an ƙirƙiri ASUU ne domin raba kan NLC, sanan a cewarsa aka hana ASUU zama a ƙarƙashin NLC, matakin da ya ce sun ƙalubalanta a kotu, kuma suka samu nasara.

    Ya ƙara da cewa an ƙirƙiri jami'o'i masu zaman kansu ne domin karya lagon ASUU, inda ya ce dole a yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da cewa sun shiga ƙungiyar ta ASUU.

  17. Guguwa ta raba mutum miliyan 1 da muhallinsu a Philippines

    Guguwa

    Asalin hoton, Reuters

    Wata mahaukaciyar guguwar da ta abka wa kasar Philippines a jiya Lahadi ta ratsa ta tekun kudancin China, inda ta yi barna da haddasa ambaliya.

    Kusan mutum miliyan daya suka nemi mafaka a wani wuri na musamman da aka tanadar.

    Sai dai ba kasafai Hukumomin kasar ke bayar da rahoton girman barnar da aka yi ba.

    Wakilin BBC ya ce amabliya ta mamaye gidaje da dama yayin da aka samu yankewar hanyoyi da gadoji lantarki a tsibirin Luzon

  18. Majalisar Amurka ta sulhunta da gwamnati kan ci gaba da ayyukan gwamnati

    US

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƴanmajalisar dattijan Amurka sun cimma wani babban mataki na kawo karshen tankiyar da ke tsakaninsu da ta kai ga dakatar da ayyukan gwamnati.

    Wakiliyar BBC ta ce wannan na zuwa ne bayan shafe sa'o'i ana tattaunawa a karshn mako sanatocin jam'iyyar Democrats sun amince ne su goyi bayan tsawaita wa'adin kudaden gwamnati har zuwa karshen watan Janairu da kuma goyon baya ga kunshin kudade na tafiyar da muhimman hukumomi.

    Sai dai Yarjejeniyar ba ta kunshi tabbacin tsawaita tallafin inshorar lafiya ba wanda ya kasance babbar buƙatar 'yan jam'iyyar Democrat bayaan tsallake majalisar Dattijani.

    Yanzu za su mika kudirin zuwa majalisar wakilai su amince kafin amincewar shugaban Trump

  19. An sake gabatar da tsohon shugaban Koriya ta Kudu Yoon Suk Yeol a kotu

    China

    Asalin hoton, EPA

    Masu gabatar da kara na Koriya ta Kudu sun gabatar da wasu sabbin tuhume-tuhume kan tsohon shugaban kasar Yoon Suk Yeol.

    Masu gabatar karar na tuhumar tsohon shugaban ne da taimaka wa abin da suka kira abokan gaba bayan dokar soji da ya ayyana a bara.

    An zargi tsohon shugaban da bayar da umarnin jirage marar matuka a makwabbiyar kasar koriya ta Arewa da nufin haifar da tashin hakali don tabbatar da matakin da ya dauka na ayyana dokar soji.

    A watan Afrilu ne aka tsige Mr Yoon yayin da yake ci gaba da fuskantar shari'a.

  20. Boren fursunoni a Ecuador ya yi ajalin mutum 31

    Prison

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomi a Equador sun ce akalla fursunoni 31 aka kashe sakamakon bore a gidan yarin Machala a yankin El Oro.

    Hukumar kula da gidajen yari ta kasar ta ce an samu gawarwakin mutum 27 a ranar Lahadi bayan rikicin farko da ya yi sanadiyar mutuwar mutum hudu tare da jikkata wasu da dama.

    Rahotanni sun ce rikicin ya barke ne bayan sauya tsarin yan gidan yarin.

    Equador dai ta dade tana fama da mummunan rikici a gidajen yari a shekaru da dama