Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Talata 25/11/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Talata 25/11/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir da Isiyaku Muhammad da Aisha Aliyu Jaafar

  1. Birtaniya ta ƙi amincewa da buƙatar Najeriya ta dawo da Ekweremadu gidan yarin ƙasar

    Ike Ekweremadu

    Asalin hoton, METPOLICE

    Birtaniya ta ƙi amincewa da buƙatar da gwamnatin Najeriya ta gabatar mata na dawo da Ike Ekweremadu gidan yari a Najeriya domin ya ƙarasa wa'adinsa.

    Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan ƙasar na zaman kaso ne a Birtaniya bayan kama shi da laifin safarar sassan jikin bil'adama.

    An yanke masa hukuncin ɗaurin shekara 9 da wata takwas a watan Maris ɗin 2023, saboda kitsa yadda za a cire ƙodar wani matashi domin a dasa wa ƴarsa Sonia da ke fama da ciwon ƙoda.

    A watan Nuwamba ne shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya aike da wata babbar tawaga birnin Landan domin tattauna hukuncin da aka yanke masa, da kuma duba yiwuwar dawo da shi Najeriya ya ƙarasa wa'adinsa.

  2. Musayar wuta tsakanin Rasha da Ukraine ya yi ajalin fararen hula da dama

    ginin da aka kai wa hari

    Asalin hoton, Reuters

    Rasha da Ukraine na kai wa juna hari inda ake samun rahotannin mutuwar fararen hula a ɓangarorin biyu.

    Jami'an Ukraine sun ce mutum biyu sun mutu a wani katafren hari na makami mai linzami da jirgin sama maras matuki da Rasha ta kai mata a babban birninta Kyiv, kan wasu gidajen zaman jama'a biyu.

    Harin ya kuma janyo katsewar wutar lantarki da ruwan famfo.

    Can a kan iyaka kuma Gwamnan yankin Rostov ya ce jiragen sama marasa matuƙa na Ukraine sun hallaka mutum uku da jikkata wasu goma.

    Wasu mutanen shida ma sun jikkata a Krasnodor.

    Jami'an ma'aikatar tsaron Rasha sun ce sun lalata jiragen sama marasa matuƙa sama da 200 na Ukraine.

  3. RSF ta amince da tsagaita wuta domin ayyukan jinƙai

    jagoran mayakan RSF

    Asalin hoton, AFP

    Ƙungiyar RSF da ke yaƙi da rundunar sojin Sudan ta sanar da dakatar da buɗe wuta, domin ayyukan jinƙai har na tsawon wata uku.

    Ƙungiyar ta sanar da hakan ne kwana daya bayan da rundunar sojin Sudan din ta yi watsi da wani daftarin dakatar da buɗe wuta da masu shiga tsakani na duniya suka gabatar, tana mai cewa yarjejeniyar ta fifita RSF.

    Kwamandan RSF din Mohamed Hamdan Dagalo ne ya yi sanarwar a wani bidiyo da aka naɗa.

    Yarjeniyoyin dakatar da buɗe wuta da aka rika yi a baya - sun rika rushewa, tun ba a je ko'ina ba.

    Dubban fararen hula aka kashe tun da yaƙin basasar ya ɓarke a 2023.

  4. Buɗewa

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Talata, daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu ɗaura daga inda muka tsaya a jiya a wannan shafin na labaran kai-tsaye.

    Za mu rika kawo muku irin wainar da ake toyawa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Ku kasance tare da mu.