Nawa jihohin Najeriya ke samu daga tarayya kuma yaya suke kashe kuɗin?

Asalin hoton, Fadar shugaban ƙasa/X
Ƴan Najeriya sun ci gaba da muhawara kan maƙudan kuɗaɗen shiga da matakan gwamnati uku suka raba a Najeriya cikin watan Janaurin da ya gabata.
Hukumar raba arzikin ƙasar, FAAC ta ce matakan gwamnatin uku, wato gwamnatin tarayya da jihohi da kuma ƙananan hukukomi sun raba naira tiriliyan 1. 963 a watan da ya gabatan.
Cikin wata sanarwar darakta yaɗa labaran ofishin babban akanta na ƙasa , Bawa Mokwa ya fitar a farkon makon da muke ciki ya ce an samu nasarar tara kuɗaɗen ne ta hanyar harajin cikin gida da aka tara a watan na naira tiriliyan 1.08 da kuma naira biliyan 846.507 da aka tara daga harajin VAT, sai kuma naira biliyan 38.110 da aka tara daga harajin tura kuɗaɗe ta intanet.
Sanarwar ta ce bayan kasafta kuɗaɗe gwamnatin tarayya ta samu naira biliyan 653.500, yayin da jimillar jihohin ƙasar 36 da birnin Abuja suka samu naira biliyan 706.469, sai kuma ƙananan hukumomi da suka samu naira biliyan 513.272.


