Yaƙin Iran da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 01/06/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai kan yaƙin Iran da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Litinin 01/06/2026.

Skip Bidiyo and continue reading
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Sadis Buba
  • Pantami
  • xxx
  • Nafiu Gombe
  • Mace da ƴarta mai lalaurar Autism
  • wata mata
  • BBC reporter

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, A'isha Babangida, Haruna Kakangi

  1. An haramta wa ƴara buɗe shafukan sada zumunta a Malaysia

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Malaysia ta fara hana ƴan ƙasa da shekara 16 daga buɗe shafukan sada zumunta.

    Hukumar kula da harkokin sadarwa ta ƙasar ta ce dole ne shafuka kamar Fesbuk da Instagram da Tikok da YouTube su tantance shekaru kan bayanan gwamnati da aka bayar.

    Malaysia ta bi sahun ƙasashen da suka bijiro da matakai makamancin haka domin kare yara daga ganin abubuwan da ba su kamata ba a shafukan sada zumunta.

    Kamfanonin da suka gaza martaba matakin zai fuskanci tarar kusan dala miliyan biyu da rabi.

  2. Malamai sun shiga yajin aiki kan sace ɗaliban Oyo

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar malamai ta Najeriya ta umarci malama makarantun firamare da sakandare a jihar Oyo su shiga yajin aiki daga yau Litinin har sai abin da hali ya yi.

    Umarnin ya fito daga shugabancin ƙungiyar na ƙasa a matsayin nuna damuwa kan ci gaba da tsare malamai da kuma ɗaliban da aka sace, wanda zuwa yanzu ba a da tabbaci kan lokacin da za a kuɓutar da su ba.

    A cewar ƙungiyar, ci gaba da tsare ɗaliban da malaman na ƙara haifar da fargaba a tsakanin malamai tare da sa iyaye yin baya-baya da tura ƴaƴansu zuwa makaranta.

    Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa lamarin ya zo ne bayan umarnin da Shugaba Bola Tinubu ya bayar a ranar Lahadi na ɗaukan jami'an tsaron gandun daji 1,000 domin taimakawa wajen kuɓuto da malamai da ɗaliban da aka sace.

    A wata sanarwa da shugaban ƙungiyar reshen Oyo Kwamared Hassan Fatai ya sanyawa hannu, NUT ta ce an ɗauki matakin domin jawo hankalin hukumomi su gaggauta ruɓanya ƙoƙarinsu na ganin an sako waɗanda akae garkuwa da su ba tare da ɓata lokaci ba.

  3. Amurka ta kai 'hare-haren martani' kan Iran

    Donald Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Sojojin Amurka sun ce sun kai hare-hare kan wuraren samar da jirage marasa matuƙa na Iran a birnin Goruk da kuma tsibirin Qeshm a ƙarshen mako.

    Rundunar sojin Amurka a gabas ta tsakiya ta bayyana a shafinta na sada zumunta cewa an kai hare-haren ne a matsayin martani ga abin da ta kira “Matakan tsokana daga Iran”, waɗanda suka haɗa da harbo wani jirgin leƙen asiri marar matuƙi na Amurka, wanda take ikirarin yana shawagi ne a sararin samaniyarta.

    A matsayin martani, dakarun juyin juya halin Musulunci na Iran sun ce sun kai hari kan wani sansani da sojojin Amurka ke amfani da shi, sai dai ba su bayyana sunan sansanin ba.

    Tun da fari, Kuwait ta ce ta dana garakuwar tsaron sararin samaniyarta, don harbo wani makami mai alinzamia da Iran din ta harba.

  4. Mutum huɗu sun warke daga cutar Ebola

    xxx

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomin lafiya a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo sun yi murnar warkewar mutum huɗu da suka tsira daga cutar Ebola.

    Suna daga cikin mutanen farko da aka sallama daga cibiyoyin jinya tun bayan barkewar cutar da aka samu a yanzu.

    A wani biki da aka gudanar a Bunia, wanda shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya halarta, an yaba wa mutanen da suka warke wadanda dukkaninsu ma’aikatan lafiya ne bisa jarumtar da suka nuna.

    Mutanen sun kamu da Ebolar ne yayin da suke kula da masu cutar, kuma sun ce sun ji dadi kwarai-kwarai da suka samu lafiya.

  5. Barkan mu da warhaka!

    Barka da zuwa shafin BBC Hausa na kai-tsaye na ranar Litinin 1 ga watan Yuni 2026.

    Wannan shafi zai kawo muku duk muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya tsokaci kan abubuwan da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta: facebook, X, Instagram da kuma YouTube.