Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 02/07/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir da Umar Mikail

  1. David Mark ya sanar da ficewarsa daga PDP

    David Mark

    Asalin hoton, Social Media

    Tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya David Mark ya sanar da ficewa daga jam'iyyar adawa ta PDP saboda abin da ya kira "rikicin cikin gida game da shugabanci", kamar yadda kafar yaɗa labarai ta Channels TV ta ruwaito.

    Sanata Mark ya jagoranci majalisar dattawa daga 2007 zuwa 2015, amma yanzu yana cikin jagororin adawa da ke shirin ƙalubalantar gwamnatin APC a jam'iyyar haɗaka ta ADC.

    Cikin wasiƙa daya aike wa shugaban PDP a mazaɓarsa da ke Otukpo Ward a jihar Binuwai, tsohon sanatan ya ce rigingumun da jam'iyyar ke fama da su sun mayar da ita "abar dariya a tsakanin al'umma".

    "Na rubuto wannan wasiƙa ne domin na ayyana maka a hukumance matakin da na ɗauka ficewa daga kasancewata ɗan jam'iyyar PDP nan take," a cewar wasiƙar.

    Rahoton na Channels ya ce Mark na cikin mutanen da aka kafa PDP tare da su lokacin da ta zama jam'iyyar siyasa a 1998.

  2. Jirgin sojoji yayi hatsari a Somaliya

    ...

    Asalin hoton, Munasar Mohamed

    Wani jirgin sojin sama ya yi hatsari a filin jirgin saman Aden Adde da ke birnin Mogadishu a safiyar ranar Laraba kamar yadda shugaban hukumar kula da sufurin Jiragen Sama ta Somaliya Ahmed Maalim ya tabbatar wa da BBC.

    Jirgin saman wanda ya tashi ne daga tashar soji ta Balidoogle da ke yankin Lower Shabelle, ya fadi ne a sashen sojoji na filin jirgin saman.

    Mutane takwas ne ke cikin jirgin, ciki har da matuƙan jirgin.

    Bayan faduwar jirgin, wata babbar gobara ta tashi, amma har yanzu ba a san halin da mutanen da ke cikin jirgin suke ciki ba.

    Hatsarin ya janyo jinkiri a tafiyar jirgin Turkish Airlines da aka tsara saboda matsalar tsaro, duk da haka jiragen Daallo Airlines da wasu ƙananan jiragen cikin gida sun ci gaba da aiki a filin jirgin.

    Har yanzu ba a gano musabbabin hatsarin jirgin ba, amma ana gudanar da bincike, in ji Ahmed Maalim,

  3. INEC za ta fitar da sabbin ƙa’idojin duba sakamakon zaɓe a Najeriya

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    A shirye-shiryen da take yi gabanin babban zaɓen Najeriya na shekarar 2027, hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) ta bayyana shirin ta na fitar da ƙarin ƙa’idoji da za su jagoranci yadda za a duba sakamakon zaɓe da aka riga aka bayyana.

    Shugaban INEC, farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan a taron kwata na biyu da kwamishinonin zaɓe na jihohi (RECs) a Abuja .

    Ya jaddada cewa kwamishinonin zaɓe su ɗauki cikakken nauyin aikinsu bisa ƙundin tsarin mulki.

    Farfesa Yakubu ya kuma bayyana damuwa kan yadda mutane ke fassara Sashe na 65 na dokar zaɓe ta 2022 .wadda ke ba INEC damar duba sakamakon zaɓe ta hanyoyi daban-daban, inda ya ce hukumar na aiki kan sabbin ƙa’idoji da za su bayyana yadda ake nazari da sake duba sakamakon zaɓe.

    "Sabbin dokokin za su kasance ƙari ne ga dokokin gudanar da zaɓe na 2022, kuma za a wallafa su a shafin hukumar nan bada jimawa." shugaban hukumar ya ƙara da cewa.

    Ya kara da cewa INEC ta riga ta gana da shugabannin jam’iyyu da ƙungiyoyin fararen hula da 'yan jarida da jami’an tsaro domin samun haɗin kai.

    Haka kuma, dukkan jihohin Najeriya da Abuja sun riga suna da sabbin kwamishinonin zaɓe (RECs) masu cikakken iko.

  4. Amurka ta dakatar da jigilar wasu makamai zuwa Ukraine

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Amurka ta tabbatar da cewa an dakatar da jigilar wasu makaman da ƙasar ke kai wa Ukraine.

    Hakan ya faru ne saboda fargabar cewa makaman da Amurka ke da su a ƙasa sun yi kaɗan.

    Ukraine dai ta daɗe tana neman tallafiin ƙarin makamai da za ta yi amfani da su wurin kare biranenta daga hare-haren da Rasha ke kai wa.

    Wata mai magana da yawun fadar White House Anna Kelly ta ce an yanke shawarar dakatar da bayar da makaman ne domin bayar da fifiko ga muradun Amurka.

  5. Isra'ila ta amince da sharuɗɗan yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, in ji Trump

    Trump da Netanyahu

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Isra'ila ta amince da sharuɗɗan da za su tabbatar da cimma yarjejeniyar tsagaita wuta na kwanaki sittin a Gaza.

    A sanarwar da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, Mista Trump ya ce yana fatan Hamas za ta amince da wannan yarjejeniya domin, a cewarsa, lamarin ba sauƙi zai yi ba sai dai ma ya kara taɓarɓarewa.

    Wakilin BBC ya ce sanarwar ta Trump na zuwa ne gabanin ganawar da zai yi da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a ranar Litinin mai zuwa, inda shugaban na Amurka ya ce zai tsaya tsayin daka kan wannan batun.

    Yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a baya dai ta ruguje ne a watan Maris lokacin da Isra'ila ta karya ta kuma ta ci gaba da kai hare-hare a Gaza.

  6. Assalamu Alaikum

    Ma'abota BBC Hausa barkanmu da hantsin Laraba - ta bawa ranar samu.

    Ni ne Umar Mikail zan kawo muku rahotonnin abubuwan da ke faruwa daga sassan duniya, musamman a Najeriya da Nijar da maƙwabtansu.

    Zan yi hakan ne bisa sa idon Usman Minjibir.