David Mark ya sanar da ficewarsa daga PDP
Tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya David Mark ya sanar da ficewa daga jam'iyyar adawa ta PDP saboda abin da ya kira "rikicin cikin gida game da shugabanci", kamar yadda kafar yaɗa labarai ta Channels TV ta ruwaito.
Sanata Mark ya jagoranci majalisar dattawa daga 2007 zuwa 2015, amma yanzu yana cikin jagororin adawa da ke shirin ƙalubalantar gwamnatin APC a jam'iyyar haɗaka ta ADC.
Cikin wasiƙa daya aike wa shugaban PDP a mazaɓarsa da ke Otukpo Ward a jihar Binuwai, tsohon sanatan ya ce rigingumun da jam'iyyar ke fama da su sun mayar da ita "abar dariya a tsakanin al'umma".
"Na rubuto wannan wasiƙa ne domin na ayyana maka a hukumance matakin da na ɗauka ficewa daga kasancewata ɗan jam'iyyar PDP nan take," a cewar wasiƙar.
Rahoton na Channels ya ce Mark na cikin mutanen da aka kafa PDP tare da su lokacin da ta zama jam'iyyar siyasa a 1998.