Rufewa
Masu bin wannan shafi nan muka kwo ƙarshen labarai da rahotonnin.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.
Amma kafin na muke cewa mu kwana lafiya
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 02/07/2025.
Usman Minjibir da Umar Mikail
Masu bin wannan shafi nan muka kwo ƙarshen labarai da rahotonnin.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.
Amma kafin na muke cewa mu kwana lafiya
Jami'an Hamas sun tuhumi shugaban wata ƙungiya mai adawa da Hamas da ke ayyukanta a kudancin Gaza da laifukan cin amanar ƙasa ta hanyar haɗa kai da Isra'ila.
An buƙaci Yasser Abu Shabab ya mika wuya kan zargin da ake yi masa na alaƙa da Isra'ila da ɓarnata kayan agajin da ake bai wa fararen hula.
Abu Shabab ya musanta zarge-zargen, inda ya jajjada cewa ƙungiyarsa na yi wa motocin da ke ɗauke da kayan agaji rakiya domin wucewa lafiya, zuwa yankuna masu aminci.
Isra'ila ta amince da tallafa wa ƙungiyar - wadda ke adawa da Hamas a Gaza.
Hukumar Alhazan Najeriya ta kamala jigilar alhazan ƙasar da suka sauke farali a aikin hajjin bana.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X, ta ce ta kammala aikin kwaso alhazan daga ƙasa mai tsarki a yau Laraba 2 ga watan Yulin 2025.
Kimanin alhazan Najeriya 41,291 ne suka sauke farali a wanan shekara, kamar yadda hukumar ta bayyana.
Jirgin ƙarshe da ya ɗauko alhazan jihar Kaduna ya taso da safiyar yau.
Ministan harkokin wajen Isra’ila ya ce ba za a yi wasa da duk wata dama ta sakin wadanda Hamas take garkuwa da su a Gaza ba.
Gideon Saar's ya bayyana hakan ne bayan shugaban Amurka Donald Trump ya ce Isra’ila ta amince da yarjejeniyar sakin mutanenta da aka kama, da kuma tsagaita wuta ta kwana 60.
Sai dai rahotannin sun ce abu ne mai wahala jam’iyyu masu tsatstauran ra’ayi su amnice da matakin.
Ita ma Hamas ta ce tana duba yiwuwar amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta.
Hare-haren Isra'ila ta sama sun kashe babban daraktan asibitin Indonesia da ke arewacin Gaza.
Jami'an lafiya sun ce Marwan Sultan ya mutu tare da matarsa da sauran danginsa a lokacin da wani harin Isra'ila ya faɗa an gidansa.
An yi saurin garzayawa da su asibitin Al-Shifa, inda aka tabbatar da mutuwarsu.
A makonnin da suka gabata ne - dakarun IDF suka rushe Asibitin Indonesia bayan da suka yi zargin cewa mayaƙan Hamas na amfani da shi.
Dakta Sultan ya sha kiran duniya ta bai wa ma'akatan lafiya da ke Gaza kariya.
Babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya, PDP ta gargaɗi ƴanƴanta da ke shirin shiga sabuwar haɗakar ADC.
Yayin da yake jawabi ga manema labarai bayan taron kwamitin amintattun jam'iyyar, shugaban jam'iyyar na ƙasa Amb. Iliya Damagum ya ce jam'iyyar za ta ɗauki tsattsauran mataki kan mambobinta da ke ƙoƙarin shiga haɗakar.
Damagum ya ce ƙoƙarin da haɗakar ke shirin yi ba zai yi tasiri ba, yana mai cewa da dama daga cikin mambobin haɗakar za su koma jam'iyyunsu.
“Yana da kyau su sani cewa babu inda ya kamata a haɗu domin tunkarar gwamnatin APC da ya wuce jam'iyyar PDP, amma in suna ganin ba haka ba, to su je su gwada su gani, amma dai na san dole za su dawo'', in ji shi.
Shugaban riƙon ya kuma gargaɗi ƴan PDP da ya ce suna ƙoƙarin ''sayar da jam'iyyar''.
Kawo yanzu dai akwai jiga-jigan PDP cikin sabuwar haɗakar ta ADC, ciki har da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar a zaɓen da ya gabata.
A farkon makon nan ne dai jam'iyyar PDP ta gudanar da taronta na kwamitin zartaswa da a ciki ta ce ta ɗinke ɓarakar da ta ɗauki tsawon lokacin tana fama da shi cikin jam'iyyar.
Tsohon Ministan Shari'a na Najeriya, Abubakar Malami ya ce a shirye haɗakar ADC take wajen yaƙi da gwamnatin APC domin kawo ''gyara kan yadda ake tafiyar da gwamnati''.
Malami -wanda ya kasanec minista a zamanin gwamnatin tsohon shugaban Najeriya, Mumammadu Buhari - ya ce ukuɓar da gwamnati Tinubu ta sanya talakwan NAjerya a ciki ba za ta misaltu ba
A hirarsa da BBC Abubakar Malami ya ce sun fito fili ne domin su yaƙi jam'iyyar APC mai mulki, musamman yadda ta bar abubuwa da dama sun tabarbare a ƙasar, ciki har da tsaro da tattalin arziki da kuma sauran dangogin wahalhalu da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta jefa talakawa.
''A duk lokacin da wata tarayya ta zo da wasu tsare-tsare na ƙuntata wa al'umma, da sanya su cikin halin wahala to wajibi a taru wuri guda su dauki mataki domin kawo sauyi ta hanyar maido da kaykkyawan tsari, da zai ɗaɗa wa mutane'', in ji shi.
Abubakar Malami ya kuma ce a shirye suke su jajirce wajen yai da gwamnati mai ci.
''Mun yanke hukunaicn ɗaukar mataki domin yaƙi da rashin tsaro da ynuwa domin maido da najeriya kan turba mai kyau da tsari'', in ji shi.
Ƙungiyar Hamads ta ce tana nazarin sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin Gaza da aka gabatar mata, tana mai cewa manufar yarjejeniyar ita ce kawo ƙarshen hare-hare Isra'ila da janye dakarunta daga yankin.
Ƙungiyar ta ce tana tuntuɓar abokan shawararta, sannan ta jinjina wa ƙoƙarin masu shiga tsakanin.
Shugaban Amurka ne ya gabatar da yarjejeniyar tsagaita wutar ta kwana 60, wadda ya ce tuni gwamnatin Isra'ila ta amince da ita.
To sai dai rahotonni na cewa da dama cikin ministoci masu ra'ayin riƙau ba su gamsu da ita ba, yayin da Firaminista Benjamin Netanyahu ya dage cewa yana son kawo ƙashen Hamas.
Kotu a Amurka ta samu fitaccen wamaƙin gambarar ƙasar, Sean ''Diddy'' Combs da laifuka biyu da suka haɗa da safara da kawalci.
A yanzu mawaƙin na fuskantar hukuncin ɗurin shekara 10 ruɓi biyu kan laifukan biyu da aka same shi da aikatawa kan tsoffin ƴan matansa biyu.
Duka ƴan matan sun tabbatar wa kotun cewa mawaƙin ya ci zarafinsu ta hanyar lalata.
Sai dai kotun ba ta same shi da sauran manyan laifukan da ake tuhumarsa da su ba da suka haɗa da zamba da safarar mutane domin tilasta musu karuwanci, laifukan da za su iya kai shi ga ɗaurin rai da rai.
Tsohon ministan shari'a na Najeriya, Abubakar Malami ya sanar da ficewa daga jam'iyyar APC tare da komawa haɗakar ƙawancen jam'iyyu hamayya ta ADC.
Cikin wata sanarwa da tsohon ministan ya fitar a shafinsa na sada zumunta, ya ce ya ɗauki matakin ne domin bayar da tasa gudunmowa wajen ceto Najeriya daga durƙushewa.
Abubakar Malami ya bayyana dalilan rashin nuna halin ko'ina kula da gwamnatin APC ke yi wa matsalolin da suka addabi Najeriya.
''Zubar da jini ya yi yawa, ga matsalar tsaro da ke addabar yankunanmu musamman arewaci da ke fama da ƴanfashi da masu garkuwa da mutane da matsalar ta'addanci, amma duk da waɗannan, gwamnatin APC ta fifita siyasa maimakon kare rayukan ƴanƙasa'', kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Tsohon ministan ya kuma zargi gwamnatin APC da haifar da tashin farashin kayyaki, musamman na abinci da rashin ayyukan yi, amma duk da haka ya ce gwamnati a mayar da hankalinta kan siyasa.
Abubakar Malami - wanda ɗan jihar Kebbi ne daga arewa maso yammacin Najeriya - ya zargi gwamnatin Tinubu da aiwatar da naɗe-naɗe don siyasa ba don ci gaban ƙasa ba.
''Wanna ne dalilin da ya sa na shiga ADC, domin haɗa ƙarfi wuri guda da nufin kawar da wannan gwamnati, domin samar da sabuwar tafiya da za ta inganta rayuwar ƴan Najeriya'', in ji shi.
Haɗakar hammayar ADC a Najeriya ta tabbatar da naɗin Tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Ƙasar, Sanata David Mark a matsayin sabon shugabanta na ƙasa.
Sanata David Mark, ya bayyana cewa ƙawancen ADC, haɗaka ce da ta shafe watanni ana tattaunawa domin samar da ita.
Ya ambato manyan matslolin tsaron da ke addabar jahohin Kaduna da Katsina da Zamfara da Sokoto da Borno da Yobe da sauran su, da cewa duk wani da ya damu da halin da ake ciki mai alaƙa da hakan, ya amince da shiga wannan haɗaka tasu.
Ya ce duk waɗanda suka hallara a taron da zuciya ɗaya suka amince da dunkikewar.
David Mark ya kuma ce daga cikin fatansu shi ne ceto Najeriya da kuma al'ummar kasar.
A taron haɗakar na jiya ne aka tabbatar da naɗin tsohon gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola a matsayin sakataren jam'iyyar na ƙasa.
Gamayyar jam'iyyun hamyyar Najeriya na ci gaba da gudanar da taronsu a yau, inda ake sa ran za su bayyana dunƙulewa a jam'iyar ADC.
Taron da ke gudana a babban ɗakin taro na Yar'adua Centre da ke tsakiyar birnin Abuja ya samu halartar jigaji-jigan 'yan siyasa daga jam'iyyu daban-daban da suka haɗa da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyar LP, Peter Obi.
Sauran sun haɗa da tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai da Rotimi Amaechi da tsohon gwamnan Osun, Rauf Aregbisola da tsohon shugaban Majalisar Dattawan ƙasar, Sanata David Mark da sauran su.
Wani abin da ya ɗauki hankalin jama'a shi ne ganin tsohon ministan shari'ar Najeriya kuma babban lauyan gwamanatin ƙasar lokacin gwamnatin Bahari, wato Abubakar Malami SAN a wurin taron.
Kafin nan dai jiga-jigan 'yan siyasar sun gudanar da wani taro a jiya Talata, inda suka bayyana fata mai ƙarfi na shirin hadewa ƙarƙashin jam'iyar ta ADC.
Rundunar Yan sandan jihar Jigawa ta ce suna ci gaba da bincike kan wani matashi da suka kama bisa zargin sa da kashe mahaifiyarsa.
‘Yan sandan suna zargin matashin ne dan shekara 30 da sanadin ajalin mahaifiyarsa mai shekara 75 ne ta hanyar buga mata bulon kasa a kanta.
Kawo yanzu dai jami'an tsaron suna tsare da wadda ake zargin a sashen binciken manyan laifuka.
Cikin wata sanarwa da ‘yan sandan suka fitar, sun bayyana cewa lamarin ya auku ne a unguwar Dantanoma cikin karamar ƙaramar hukumar Gumel a jihar Jigawa.
SP Shi'isu Lawan Adam shi ne kakakin ‘yan sandan, ya ce da farko sun sami labarin cewa rikici ne ya barke tsakanin matashin da mahaifiyarsa, kuma ba tare da ɓata lokaci ba jami’ansu suka garzaya zuwa gidan, amma suna zuwa sai suka tarar dattijuwar yashe a kwance.
Rahotanni na cewa ana fama da irin wannan matsala ta samun sabani tsakanin iyaye da 'ya'yansu, ko a farkon watan Mayun shekarar nan ma, sai da aka kama wani matashi a jihar Jigawan, wanda ake zargi da kashe mahaifinsa da adda a garin Sara da ke karamar hukumar Gwaram.
Kotun a Bangladesh ta yankewa tsohuwar Piray Minista, Sheikh Hasina zaman gidan yari na watannin shida sakamakon saɓa umarnin Kotu.
Ta kuma samu Shiek Hasina da ke zaman gudun hijra a India da laifi a kalamanta da ta yi a watan Disambar 2024, tana mai kallon su a matsayin barazana ga masu ba da sheda.
Wakiliyar BBC ta ce hukuncin zai fara aiki da zarar ta sanya kafarta a Bangladesh.
Wannan ne hukuncin farko da aka yanke mata tun bayan da ta ajiye muƙaminta tare da koma wa Delhi, babban birnin Indiya da zama.
Mutum Dubu daya da dari hudu ne suka rasa rayukansu yayin zanga-zangar da a kai a ƙasar, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya.
Ukraine ta bayyana damuwarta a kan matakin da shugaba Trumph ya ɗauka na dakatar da bai wa Kyiv wasu daga makamai, tana mai cewa zai sanya Rasha ta samu ƙwarin gwiwa a yakin da suke yi.
Ministan harkokin ƙasar ya gayyaci Amurika teburin tattaunawa ta fuskar duflomasiyya.
Ya kuma gode wa Amurika da gudunmawar da take ba su, amma duk wani jan ƙafa da za a samu wajen taimakawa tsaron Ukraine, zai sa ta fuskanci ƙarin hare-hare a yaƙin da take yi.
Wakilin BBC ya ce, Amurikar dai ba ta kai ga bayyana irin makaman da matakin zai shafa ba.
Fadar Kremlin ta gode wa Amurika a kan matakin, tana mai cewa matakin zai ƙara matso da kawo ƙarshen yaƙin.
Ga wasu hotuna da ke nuna bayan hatsarin jirgin soji a filin jirgin saman birnin Mogadishu na ƙasar Somalia.
Kungiyar ƙasashen Afrika ta AU ta ce jirgin wanda sojojin Uganda ke amfani da shi, ya taso ne daga sansaninsu na Baa-le-do-go da ke Arewa maso Yammacin ƙasar.
Kungiyar ƙasashen Afrika ta AU ta ce jirgin ta mai saukar ungulu ɗauke da mutum takwas, yayi hatsari a filin jirgin saman birnin Mogadishu na ƙasar Somalia.
Kungiyar ta ce jirgin wanda sojojin Uganda ke amfani da shi, ya taso ne daga sansaninsu na Baa-le-do-go da ke Arewa maso Yammacin ƙasar.
Ƙungiyar ta kuma ce mutane uku da suka kuɓuta na kwance a asibiti, inda ake ci gaba da neman ragowar fasinjojin da jami’ai. Hukumar kula da sufurin jirgin sama ta Somalia na gudanar da bincike kan musabbabin háɗarin.
Tsohon mataimaki na musamman ga tsohon shugaban Najeriya, Garba Shehu ya kare salon mulkin shugaba Muhammad Buhari.
Malam Garba Shehu ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da gidan talbijin na Arise TV, inda ya amince da cewa duk da wani lokacin ana bayyana shugabancin Buhari da mai jan ƙafa amma ya ce hakan na faruwa ne sakamakon ƙoƙarinsa na bin ƙa'ida wajen aiwatar da al'amura a ƙoƙarinsa na sauyin da yake yi daga mulkin soji zuwa na farar hula.
Sai dai kuma tsohon mataimakin na Buhari, ya ce ƴan Najeriya ba su da haƙuri kasancewar suna son sha yanzu magani yanzu ko da kuwa za a saɓa ƙa'idojin dimokraɗiyya.
"Yana da jan ƙafa? E, shi ma da kansa ya kan yi barkwanci dangane da hakan. Kuma ya yawan faɗin hakan lokacin da ya hau mulki a matsayinsa na soja, yana yin abun da ya ga damar yi sannan ya bayar da umarnin a kama da rufe mutane. To amma yanzu a matsayinsa na shugaban mulkin dimokraɗiyya, akwai buƙatar bin ƙa'idojin doka kafin aiwatar da al'amura." In ji Malam Garba Shehu.
Nan gaba kaɗan ne a ranar Laraba ake sa ran gamayyar 'yansiyasar adawa a Najeriya da suka dunƙulewa a jam'iyyar ADC domin ƙalubalantar Shugaba Bola Tinubu na jam'iyyar APC a zaɓen 2027, za su bayyana yadda za a kasafta tsarin jagorancin jam'iyyar.
Bayanai sun nuna cewa manyan 'yansiyasar sun amince ne su ɗunguma zuwa jam'iyyar ADC da tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata David Mark ke jagoranta, bayan gaza cimma kafa wata sabuwar jam'iyya sakamakon jan ƙafa wajen yi wa jam'iyyar rijista da hukumar zaɓen ƙasar ke yi.
Hakan ya biyo bayan wani taro da suka gudanar ranar Talata, inda ake sa ran za su sanar da cikakkiyar matsayarsu ranar Laraba.
Ɗantakarar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, da na Labour Party, Peter Obi, na cikin jiga-jigan adawar da suka shafe yinin Talata suna tattaunawar, inda kowane ɓangare ya gana da abokan tafiyarsa kafin cimma matsayar.
Wells Carlton Hotel and Apartments da ke Asokoro, Abuja ya soke wani taron da aka shirya domin ƙaddamar da jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a matsayin dandalin haɗin kan jam’iyyun adawa a Najeriya.
Sai dai a safiyar ranar Laraba, otal ɗin ya ce soke taron ya biyo bayan wani “batun bin doka na cikin gida” ba tare da bayyana dalilin soke taron dalla-dalla ba.
A wani saƙo da otal ɗin ya aika, wanda ɗan jarida kuma ɗan siyasa Dele Momodu ya wallafa a shafinsa na Instagram, otal ɗin ya ce ba haka zancen yake ba.
“Muna matuƙar bakin ciki da sanar da ku cewa, saboda wani batun bin doka da muka gano yanzu, ba za mu iya ci gaba da karɓar taronku da aka shirya ba.”
“Mun fahimci cewa saura ƙasa da awanni 24 taron ya gudana, kuma muna ba da haƙuri sosai bisa wannan jinkiri da ƙalubalen da hakan ka iya jawo muku.”
Wannan lamari ya haifar da ƙarin ce-ce-ku-ce daga ’yan adawa, inda aka zargi gwamnati da tsoratarwa da katsalandan.
Taron ADC na da nufin haɗa manyan ’yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban, ciki har da Atiku Abubakar da David Mark da Peter Obi da Nasir El-Rufai da Rotimi Amaechi, da wasu tsofaffin gwamnoni da ministoci.