Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 05/07/2025.

Rahoto kai-tsaye

Ahmad Bawage da Umar Mikail

  1. Mu kwana lafiya

    Ƙarshen rahotonnin kenan a wannan shafi na ranar Asabar.

    Muna tafe da wasu sababbi gobe Lahadi.

  2. Jirgin farko na 'yan ciranin da Trump ya kora sun isa Sudan ta Kudu

    Matafiya

    Asalin hoton, Getty Images

    Jirgin farko na 'yan ciranin da Amurka ta kora ya isa ƙasar Sudan ta Kudu bayan 'yan ciranin sun gaza samun nasara a ƙarar da suka shigar da matakin Shugaba Donald Trump.

    An tsare su a wani sansanin sojin Amurka da ke ƙasar Djibouti saboda dalilai na shari'a. Hukumomin Amurka sun ce an taɓa ɗaure mutanen kan wasu manyan laifuka da suka aikata kuma ɗaya daga cikinsu ɗan Sudan ta Kudu.

    Sai dai an sha fargabar cewa ƙasar na gab da faɗawa yaƙin basasa, har ma Amurka na gargaɗi ga mutanenta cewa su guji shiga saboda manyan laifuka da suka haɗa da garkuwa da mutane.

    Amma duk da haka Amurkar ta aika da maza takwas zuwa Juba babban birnin ƙasar. Lauyan mutanen ya ce an yi hakan ne don a hukunta su kuma matakin ya saɓa wa doka.

    Wata kotu ta yi umarnin dakatar da byunƙurin kai su Sudan ta Kudu, a madadin haka sai aka kai su sansanin sojin Amurka da ke ƙasar Djibouti tsawon sama da wata ɗaya.

    Ɗaya daga cikinsu ne kawai ɗan Sudan ta Kudu, yayin da sauran suka fito daga ƙasashe kamar Vietnam da Cuba da Myanmar.

  3. Malaman Jami'ar Jos sun shiga yajin aiki

    Jami'an Jos

    Asalin hoton, University of Jos

    Ƙungiyar malaman jami'a ta Academic Staff Union of Universities (ASUU) a Najeriya reshen Jami'ar Jos sun tsunduma yajin aiki saboda abin da suka kira tsaiko wajen biyan albashinsu na watan Yunin 2025.

    Shugaban reshen ƙungiyar, Jurbe Molwus, ya tabbatar cewa za su ci gaba da yajin aikin har sai an biya su haƙƙoƙinsu kamar yadda suka ƙulla yarjejeniya da gwamnati, a cewar rahoton kafar talabijin ta Channels TV.

    Ta ƙara da cewa duk lokacin da aka yi kwana uku a jere ba a biya su albashi ba, malaman za su dakatar da aiki, kuma tuni suka kafa kwamatin da zai saka ido kan tabbatar da ɗa'a ga umarnin ƙungiyar.

    "Matakin ya fara aiki daga ƙarfe 12:01 na dare a ranar Juma'a," a cewar wani saƙo da Mista Mlwus ya aika wa mambobin ƙungiyar.

  4. Me ke jawo warin baki kuma ta yaya za a magance shi?

    Warin baki

    Asalin hoton, Getty Images

    Kana kauce wa haɗuwa ko zuwa kusa da mutane saboda bakinka na wari? Kar ka damu wannan ba wani abu ba ne na daban kuma akwai hanyoyi da dama na maganace shi.

    Tsaftace haƙori abu ne da kusan za a iya cewa yaƙi ne da 'yan ƙananan halittu na bakteriya da ke kama wuri su zauna a tsakanin haƙoranmu da kuma harshenmu, da ba ranar daina shi.

    Idan ba ka kawar da waɗannan 'yan ƙananan halittu na bakteriya ba za su hayayyafa ne a nan har su janyo maka cutar da za ta yi illa sosai ga dadashinka.

    To amma akwai hanyoyin da za ka magance hakan.

  5. Tinubu ya sauka a Brazil

    Bola Tinubu

    Asalin hoton, Nigeria Presidency

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya isa birnin Rio de Janeiro na Brazil domin halartar taron ƙungiyar ƙasashe ta Brics karo na 17.

    Fadar shugaban ƙasa ta ce Shugaban Brazil Inacio Lula Da Silva ne ya gayyaci Tinubu taron na kwana biyu - a ranakun Lahadi da Litinin.

    Ƙasashen da ke cikin ƙungiyar su ne Brazil, da Rasha, da Indiya, da China, da Afirka ta Kudu, yayin da Najeriya ta zama abokiyar hulɗar ƙungiyar a shekarar da ta gabata.

    Mutanen da suka yi wa Tinubu rakiya sun haɗa da Ministan Harkokin Waje Yusuf Maitama Tuggar, da Gwamnan Binuwai Hyacinth Alia, da Gwamnan Neja Umaru Bago, da Gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu, da Gwamnan Delta Sheriff Oborevwori.

    Bola Tinubu

    Asalin hoton, Nigeria Presidency

  6. Kalli yadda ambaliya ta ɗaiɗaita wani yanki a Amurka

    Bayanan bidiyo, Latsa sama don kallon bidiyon

    Aƙalla mutum 24 ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwan da take wanke lardin Kerr na jihar Texas.

    Jimillar mutum 237 aka ceto ko kuma aka kwashe daga yankin zuwa yanzu, ciki har da 167 da aka ceto da jirgin helikwafta.

  7. Gwamnan jihar Osun Adeleke ya musanta komawa APC

    Ademola Adeleke

    Asalin hoton, @AAdeleke_01

    Gwamnan jihar Osun da ke kudancin Najeriya ya musanta rahotonnin da ke cewa ya fice daga jam'iyyar PDP mai adawa a ƙasar zuwa APC mai mulki.

    Ademola Adeleke ya jaddada biyayyarsa ga PDP tare da tabbatar wa kwantar wa da baya hankali, kamar yadda mai magana da yawunsa Mallam Olawale Rasheed ya bayyana cikin wata sanarwa a yau Asabar.

    "Ina tabbatar wa mazauna jihar Osun cewa har yanzu ina nan daram a PDP, ba zan koma wata jam'iyya ba," a cewar gwamnan.

    A ranar Laraba ne wasu jiga-jigai na jam'iyyar ta PDP suka sanar da shiga jam'iyyar haɗaka ta ADC domin ƙalubalantar Shugaba Tinubu na APC a zaɓen 2027.

    Cikin manyan 'yan PDP ɗin har da Atiku Abubakar, ɗantakararta na shugaban ƙasa a 2023, da tsohon shugaban majalisar dattawa David Mark, da tsohon gwamnan Jigawa Sule Lamido, da sauransu.

  8. Mahangar Zamani: Muhimmancin zama lafiya tsakanin uwargida da amarya

    Mahangar zamani

    Yayin da ake ci gaba da muhawara kan wadda ta fi "capacity" tsakanin uwargida da amarya, shirin Mahangar Zamani na wannan makon ya gayyato matashi Saleem Goje da matansa biyu, waɗanda ke zaune tare tamkar 'yanbiyu.

    Sun bayyana mana sirrin zaman nasu a lokacin da ake yawan alaƙanta zaman kishi a matsayin mai cike da rikici.

    Ku latsa nan domin kallon cikakken shirin a tasharmu ta YouTube.

  9. Matakan da muke ɗauka kan kisan matafiya a Plateau - Mutfwang

    Caleb Mutfwang

    Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato a Nijeriya ya ce gwamnatinsa ta na aiki tare da mahukunta a jihar Kaduna domin sanin abin da za su yi wa dangin matafiyan da aka kashe kwanan baya a jiharsa, waɗanda ƴan asalin Zaria ne.

    Gwamnan ya kuma ce rikice-rikice masu nasaba da rashin yardar da ke tsananin mabiya addinai da ƙabilu daban-daban, wanda kuma a wasu lokuta kan ritsa da matafiyan da ba su ji ba, ba su gani ba, ba lallai ne a iya kawo ƙarshensu cikin ɗan lokaci ba.

    A hirarsa da BBC, gwamna Mutfwang ya ce sun ɗauki matakan da suka dace a game da kisan mutanen, musamman domin ganin an yi wa iyalan waɗanda aka kashen adalci.

  10. An cafke ɗaya daga cikin gungun masu laifi da ake nema ruwa a-jallo a Sweden

    Masu gabatar da ƙara a Turkiyya sun ce sun cafke ɗaya daga cikin jagororin gungun masu laifi da ake nema ruwa a-jallo a Sweden.

    Isma'il Abdo wanda aka fi sani da "Strawberry" yana jagorantar wata ƙungiyar masu aikata miyagun laifuka mai suna Rumba a Sweden kuma ana zargin shi da kitsa haramtattun ayyuka daga ƙasashen waje.

    Yana cikin mutane goma sha tara da aka kama a yayin samamen da aka yi wanda ya kai ga ƙwace fiye da tan guda na ƙwayoyi da motoci da asusun banki da kadarori da dama.

    Rikici tsakanin ƙungiyar Abdo da wata da ba sa ga maciji da juna ya janyo kashe-kashe lamarin da ya sa aka yi amfani da sojoji domin daƙile tarzomar.

  11. Tinubu ya gaji tattalin arziki da ya kusa durkushewa - Wike

    Wike

    Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyeson Wike, ya ce gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta karɓi Najeriya ne lokacin da tattalin arzikin ƙasar ya kusa durkushewa.

    Wike ya bayyana haka ne a cikin shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels ranar Juma'a.

    Ya yi watsi da iƙirarin cewa gwamnatin Tinubu ta lalata ɓangaren tattalin arzikin Najeriya.

    "Ya gaji tattalin arzikin da ya samu tawaya, wanda kuma ya kusa durkushewa," in ji Wike.

    Ministan na Abuja ya ce Allah ne ya ceci Najeriya da ya kawo shugaba Tinubu saboda kaɗan ya rage a binne ƙasar.

    "Najeriya ta yi sa'a da zuwan Tinubu saboda ƙiris ya rage a binne ta. Mun yi farin ciki Tinubu ya zo ya ce hakan ba zai faru ba, 'Ba zan ba ri ku shiga matsala ba".

    Ya ce cire tallafin man fetur da aka yi yana da alfanu sosai saboda zai samar wa jihohi ƙarin kuɗaɗen kashewa, ba kamar yadda wasu ke cewa tsarin ba mai kyau bane duk da cewa an fuskanci matsaloli.

    Wike ya ce ya yi wuri a yi wa gwamnatin Tinubu alkalanci a ƙasa da shekara biyu kan mulki, inda ya yi kira da a ci gaba da marawa gwamnatin baya.

  12. Kogin Vistula a Poland ya yi raguwar da ba a taɓa gani ba a tarihi

    Vistula

    Asalin hoton, Getty Images

    Kogi mafi girma a Poland, Vistula, ya yi raguwar da ba a taɓa gani ba a tarihi a birnin Warsaw sakamakon matsanancin fari.

    Ƙwararru sun ce ana sa ran lamarin zai ƙara muni cikin ƴan kwanaki masu zuwa.

    Raguwar ruwan a kogin dai na barazana ga batun samar da ruwan sha da ma wutar lantarki.

    A Hungary mai maƙwabtaka, raguwar ruwan kogi da ba kasafai ake gani ba a Daanube yana shafar harkar jigilar kayayyaki ta ruwa da noma da kuma muhalli.

    Yankuna da dama a Turai na ci gaba da fuskantar matsanancin yanayi na zafi.

  13. Hotuna: Tawagar ƴan wasan Liverpool sun isa wurin jana'izar Jota

    Tawagar ƴan wasan Liverpool sun isa wajen da za a yi jana'izar tsohon abokinsu Diogo Jota da kuma ɗan uwansa Andre Silva.

    Cikin tawagar ta Liverpool akwai kocinsu Arne Slot da kuma sauran jagororin ƙungiyar.

    Gondomar

    Asalin hoton, PA Media

    Gondomar

    Asalin hoton, PA Media

    Gondomar

    Asalin hoton, PA Media

  14. Har yanzu PDP tana nan da ƙarfinta - Isa Ashiru

    Isa Ashiru

    Asalin hoton, Isa Ashiru/Facebook

    Yayin da fagen siyasar Najeriya ke ci gaba da ɗaukar ɗumi, wasu manyan ƴan siyasa a babbar jam'iyyar adawa ta PDP sun nanata cewa har yanzu jam'iyyar tana nan da ƙarfinta kuma a dunƙule.

    Shugabannin jam'iyyar sun kuma ce ana ci gaba da shirye-shiryen babban taron jam'iyyar don zaɓen shugabannin da za su ja ragamar ta.

    Honarabul Isa Ashiru Kudan, wanda ya yi wa jam'iyyar PDP takarar gwamnan jihar Kaduna har sau biyu - a shekarar 2019 da kuma 2023, ya shaida wa BBC cewa suna ɗaukar matakai waɗanda yanzu har sun kai ga warware rikice-rikicen da suka dabaibaye jam'iyyar.

    "A baya an yi ta samun hatsaniya tsakanin ƴan jam'iyyar mu, amma zuwa yanzu mun samu nasarar warware waɗannan rikice-rikice. Ba mu da wata matsala a yanzu.

    "Mu ƴan jam'iyyar PDP ne ba mu cikin wata haɗaka. Ba laifi bane idan ƴan haɗakar suka zo don mu haɗa kai wajen kayar da gwamnatin da ke mulki da ceton al'ummar Nijeriya kan halin da suka tsinci kansu," in ji Ashiru Kudan.

    Ɗan takarar gwamnan na jam'iyyar PDP a jihar Kaduna a zaɓen 2023 ya ce har yanzu jam'iyyarsu tana nan da karfinta, babu abin da ya sauya.

    "PDP na nan kuma duk wanda ya zo za mu karɓe shi mu kuma rungume shi don tafiya tare. Da yardar Allah za mu dawo da kafafuwan mu," in ji Ashiru.

  15. Hamas ta ce tana duba batun shawarar tsagaita wuta

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Wani Bafalasɗine ke kallon gine-ginen da hare-haren Isra'ila suka ruguza a sansanin Shati, da ke arewacin Gaza

    Hamas ta ce ta gabatar da matsayarta ga masu shiga tsakani game da shawarar tsagaita wuta a Gaza, sai dai ba ta tabbatar da ko za ta amince da sharuɗan shawarar ba.

    Wani babban jami'in Falasɗinawa ya shaida wa BBC cewa Hamas ta buƙaci a yi muhimman sauye-sauye uku.

    Tana neman a gaggauta kawo ƙarshen ayyukan gidauniyar agaji ta Gaza mai samun goyon bayan Amurka da Isra'ila.

    Tana kuma son sojojin Isra'ila su janye daga wuraren da suke riƙe da su kafin matakin tsagaita wuta na ƙarshe da aka cimma a watan Maris.

    A cewar wakiliyar BBC, Hamas ta ce tana neman tabbaci daga Amurka cewa Isra'ila ba za ta ci gaba da luguden wuta ba idan ba a cimma matsaya ta dindindin ba bayan cikar wa'adin yarjejeniyar tsagaita wutar.

  16. Ana shirin jana'izar ɗan wasan Liverpool Diogo Jota

    Gondomar, Portugal

    Iyaye da ƴan uwa da kuma abokai na can suna shirin gudanar da jana'izar shahararren ɗan wasan Liverpool Diogo Jota da kuma ɗan uwansa, André Silva.

    Jota da Silva sun rasu ne a daren Alhamis, bayan da motarsu ta yi hatsari a gundumar Zamora da ke ƙasar Sifaniya.

    Ɗan wasan na kan hanyarsa ta komawa Liverpool don fara atisayen tinƙarar sabon kaka mai zuwa lokacin da ya yi hatsari.

    Za a yi jana'izarsa da misalin karfe 10 na safiyar nan a garin mahaifarsa da ke Gondomar, a ƙasar Portugal.

    Mutane da dama daga faɗin duniya ciki har da abokan wasansa, sauran ƴan wasa da kuma shugabanni a duniya na ta aika sakonnin ta'ziyya kan rashin ƴan uwan biyu.

  17. Ambaliya ta kashe mutum 24 a Texas

    Texas

    Asalin hoton, Getty Images

    Ana ci gaba da gudanar da gagarumin aikin ceto a jihar Texas da ke Amurka bayan da ambaliyar ruwa ta yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 24.

    Ruwan Kogin Guadalupe ya ƙaru da mita takwas cikin mintuna 45 kacal a cikin dare.

    Jirage masu saukar ungulu sun duƙufa wajen kuɓutar da mutanen da suka haye saman bishiyoyi domin tsira da rai.

    Daga cikin waɗanda ba a ji ɗuriyarsu ba har da tawagar wasu ƴan mata da suke wani sansani a gaɓar kogin.

    Gwamnan Texas Greg Abbott ya bayyana lamarin a matsayin babban bala'i kuma tuni ya ayyana dokar ta ɓaci domin a ƙara haɓaka ayyukan agaji.

  18. Buɗewa

    Masu bibiyar mu barkan mu da safiyar Asabar.

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa.

    Ku kasance da mu domin kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.