Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya. Laraba 6 ga Agustan 2025

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, Usman Minjibir, da Umar Mikail

  1. Jam'iyyun hamayya a Kamaru sun soki matakin kotu na hana Kamto takara

    Jam'iyyun hamayya a Kamaru sun soki matakin Kotun Tsarin Mulkin ƙasa na dakatar da takarar jagoran ƴan adawar ƙasar, Maurice Kamto a babban zaɓen ƙasar na watan Oktoba.

    Jami'an Jam'iyyar MRC wadda Maurice Kamto ya kafa ta soki matakin kotun, kamar yadda gidan redion RFI ya ruwaito.

    Jam'iyyar MANIDEM ta zaɓi Kamto ya yi mata takara a zaɓen da ke tafe sai dai hukumar zaɓen ƙasar ta bayyana cewa ɗantakara Dieudonne Yegba shi ne halastaccen ɗantakarar jam'iyyar ta MANIDEM.

    Kotun ta kuma soke takarar wani ɗan takarar da hukumar zaɓen ƙasar ta amince da shi, hakan ya kuma ƙara rage yawan ƴan takarar da za su fafata a zaɓen na Oktoba zuwa 12, ciki har da shugaba mai ci, Paul Biya mai shekara 92 a duniya.

  2. Trump ya lafta wa Brazil harajin kashi 50 cikin 100

    Harajin Amurka na kashi 50 cikin 100 kan kayayyakin Brazil ya fara aiki a yau Laraba - mafi girma da gwamnatin Trump ta lafta wa wata ƙasa.

    Harajin zai shafi muhimman kayayyakin Brazil da suka ƙunshi har gahawa.

    Wakiliyar BBC ta ce Brazil ce ta fi fitar da gahawa a duniya kuma ta fi shigar da shi a Amurka.

    Matakin na nufin farashi zai sauya ga masu sayen kayayyakin a Amurka da kuma masu samar da shi a Brazil.

    Shugaba Trump ya lafta wa Brazil harajin ne a matsayin martani ga tuhumar da ake wa abokinsa, tsohon shugaban Brazil Jair Bolsonaro wanda ke fuskantar shari'a kan zargin juyin mulki.

  3. Ƙudirin faɗaɗa mamayar Gaza zai ƙara jefa Falasɗinawa cikin hatsari - MDD

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana rahotannin da ke kwarmata yiwuwar faɗaɗa ayyukan soji na Isra'ila a zirin Gaza da matuƙar masu tayar da hankali idan har da gaske ne.

    Mataimakin Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Miroslav Jenca ya shaida wa taron kwamitin tsaro cewa matakin zai iya haifar da mummunan sakamako ga miliyoyin Falasɗinawa da kuma ƙara jefa rayukan sauran mutanen da aka yi garkuwa da su cikin hatsari.

    An kira taron ne bisa buƙatar Isra’ila bayan bayyanar wasu bidiyo da ke nuna biyu daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su – cikin mummunan yanayi.

  4. Assalamu Alaikum

    Masu bibiyarmu, barka da warhaka. Da fatan mun wayi gari lafiya.

    A yau ma za mu ci gaba da kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran ƙasashen duniya a wannan shafi namu na Kai Tsaye daga BBC Hausa.

    Sunana Nabeela Mukhtar Uba da zan kasance tare da ku kafin na miƙa ragama ga sauran abokan aikina zuwa anjima.

    Kuna iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta - Fesbuk da X da ma Instagram inda a nan ma za ku iya karanta ƙarin labarai har ma da kallon hotuna da kuma bidiyo.

    Da fatan za ku ci gaba da kasancewa da mu.