Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 22/10/2025.

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 22/10/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Umar Mikail

  1. Me ya sa Boko Haram ke ci gaba da kai wa sojoji hari?

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Masana kan harkokin tsaro a Najeriya sun yi ƙarin bayani kan dalilan da suka sa har yanzu ƙungiyar Boko haram ke ci gaba da kai hare hare kan jam'ain tsaron ƙasar.

    Duk da iƙirarinda gwamnatoci da hukumomin tsaro a Najeriya ke fitar wa masu nuna yadda aka karya ƙarfin ƙungiyar, an ga yadda daga lokaci zuwa lokaci Boko Haram ke iya kai hari kan jami'n tsaron Najeriya.

    Masanan sun ce mayƙan boko Haram na kai hare haren ne saboda yadda suke amfani da sabbin dabaru da na fasaha da suke samu daga ƙungiyoyin da suke ƙwance da su da ke irin ayyukansu a afrika da ma sauran ƙasashen duniya.

    Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka (mai ritaya) ya yi wa BBC ƙarin bayani kan yadda yake kallon sake dawowar hara haren na Boko Haram.

  2. Assalamu Alaikum

    Barkanmu da sake saduwa a shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa a yau Laraba.

    Shafin na yau zai fi mayar da hankali ne kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwabtanta, da kuma sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kuma kallon bidiyo.

    Ku kasance da mu.