Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 22/10/2025.

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 22/10/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Umar Mikail

  1. Sai da safe

    Nan za mu rufe wannan shafi na ranar Laraba.

    Za mu zo muku da wasu sababbi gobe da safe. Kafin nan, kuna iya duba ƙasa domin karanta baki ɗayan labaran da muka kawo a yau.

    Umar Mikail ke cewa sai da safenku.

  2. Saudiyya ta naɗa Salih Fawzan a matsayin babban mai fatawa

    Dr. Ṣāliḥ bin Fawzān Al-Fawzān

    Asalin hoton, Inside Haramain

    Hukumomi a Saudiyya sun naɗa Sheikh Dr. Ṣāliḥ bin Fawzān Al-Fawzān a matsayin babban malami mai fatawa na ƙasar.

    Daga yau Laraba ne Sheikh Ṣāliḥ Al-Fawzān zai kama aiki a muƙamin addini mafi girma na Saudiyya, inda zai jagoranci nazarce-nazarce na addini tare da jagorantar majalisar manyan malamai.

    Dr. Ṣāliḥ mai shekara 90 zai maye gurbin Sheikh Abdulaziz Al-Sheikh wanda ya rasu a watan Satumba.

  3. Majalisar dokokin Isra'ila ta amince da ƙudirin mallake Gaɓar Yamma da Kogin Jordan

    Majalisar dokokin Isra'ila

    Asalin hoton, Reuters

    Majalisar dokokin Isra'ila ta kaɗa ƙuri'a kan samar da wani ƙudirin mallake Gaɓar Yamma da Kogin Jordan a matsayin yankin Isra'ila.

    Ƙudirin wanda wani ɗanmajalisar Isra'ila mai tsattsauran ra'ayi ya gabatar na zuwa ne a daidai lokacin da Mataimakin Shugaban Amurka JD Vance ke ziyara a ƙasar domin tattauna batun tsagaita wuta a Gaza.

    A watan da ya gabata, Shugaba Trump ya ce ba zai bari Isra'ila ta mamaye yankin ba, wanda Falasdinawa ke kallo a matsayin tasu kasar.

    Jam'iyyar Likud ta Firaminista Benjamin Netanyahu ba ta amince da ƙudurin dokar ba, sai dai sauran mambobin gwamnatinsa hadaka sun amince.

  4. Zazzaɓin Lassa ya kama ƙarin mutum 13 da kashe 4 a Najeriya

    Zazzaɓin lassa

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar kiyaye yaɗuwar cutuka a Najeriya NCDC ta ce an samu ƙarin mutum 13 da aka tabbatar sun kamu da zazzaɓin Lassa, da kuma mutuwar mutum huɗu cikin kwana bakwai.

    Rahoton hukumar da ya binciki makon 29 ga watan Satumba zuwa 5 ga watan Oktoba, ya ce an samu sababbin masu cutar ne a jihohin Edo da Ondo, waɗanda su ne kan gaba tsakanin jihohin ƙasar 36 tun daga farkon 2026.

    Sababbin alƙaluman sun nuna cewa yanzu Najeriya na da jimillar mutum 924 da suka kamu da cutar, da 172 da suka rasa ransu a johohi 21 da kuma ƙananan hukumomi 106 a 2025.

    Adadin waɗanda suka mutu ya kai kashi 18.6 cikin 100, inda aka samu ƙarin kashi 1.6 idan aka kwatanta da 17.0 da aka samu a irin wannan lokacin na shekarar 2024.

    NCDC ta ce fiye da kashi n90 cikin 100 na mutanen an same su a jihohin Edo da Ondo da Bauchi da Ebonyi.

  5. Shugabar gidan tarihi na Louvre ta amsa gazawarta bayan sace kayayyakin ƙawa

    Kayan tarihin Paris

    Asalin hoton, Reuters

    Daraktar da ke kula da gidan adana kayyayakin tarihi na Louvre da ke birnin Paris ta amince cewa ta gaza wajen kare gidan.

    An yi wa Laurence des Cars tambayoyi bayan sace kayyaykin ado na kimanin yuro miliyan 88 a ranar Lahadi.

    Cikin ƙasa da minti takwas, barayin suka sace kayyayakin da suka haɗa da kambunan sarakuna. Ta daura alhakin satar kan salon tsaron gidan tarihin na baya, wanda ba shi da wani tasiri a yanzu.

    Rahoton binciken farko-farko ya nuna cewa ɗaya daga cikin ɗakuna uku na gidan tarihin Louvre ba shi da kyamarar tsaro ta CCTV.

    Tun da farko Des Cars ta miƙa takardar ajiye aiki, wadda aka ƙi amincewa da ita.

  6. Adadin mutanen da gobarar tankar mai ta kashe a jihar Neja ya kai 40

    Tankar mai a jihar Neja

    Asalin hoton, Reuters

    Adadin mutanen da suka mutu sakamakon fashewar tankar man fetur a jihar Neja ya ƙaru zuwa 40, a cewar hukumar kiyaye haɗurra ta Najeriya.

    Kwamandar sashe ta hukumar da ke Minna a arewacin Najeriya, Aishat Saadu, ta faɗa wa BBC cewa mutum 35 ne suka rasa rayukansu nan take a ranar Talata, inda biyar suka mutu daga baya a asibiti.

    "An mayar da mutum 14 [da suka ji rauni] Abuja yau [Laraba], 'yan'uwan mutum ɗaya sun mayar da shi Ilorin, yayin da sauran 26 ke cibiyar lafiya ta gwamnatin tarayya da ke Bida zuwa yammacin nan," a cewarta.

    Rahotonni sun ce babbar motar da ke ɗauke da man fetur daga Legas ta yi hatsari ne saboda rashin kyawun hanya, abin da ya sa mutane suka fito ɗibar man da ke kwarara daga cikinta.

    Shaidu sun ce motar ta yi bindiga ne yayin da mutanen ke tsaka da kwarfar mai, wadda ta haddasa fashewa mai ƙarfi da gobarar da ta mamaye su kuma ta ƙone wasu daga cikinsu ƙurmus.

    Iriin wannan fashewar tanka ta halaka aƙalla mutum 147 a jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya a watan Oktoban 2024.

    Tankar mai a jihar Neja

    Asalin hoton, Reuters

  7. 'Yan Najeriya fiye da miliyan 8 ne suka yi rajistar zaɓe ta Intanet zuwa yanzu – Inec

    Katin zaɓe a Najeriya

    Asalin hoton, Inec

    Hukumar zaɓe a Najeriya Inec ta ce ‘yan Najeriya fiye da miliyan takwas ne suka kammala rajistar zaɓe matakin farko a intanet yayin rajistar masu kaɗa ƙuri’a da ake gudanarwa a faɗin ƙasar.

    Cikin rahoton da hukumar ta fitar a Abuja, Inec ta ce baya ga mutum miliyan 8,003,196 da suka yi rajistar a matakin farko, miliyan 1,700,000i ne suka kammala cikakkiyar rajistarsu.

    Bisa ga ƙididdigar mako na tara, Jihar Imo ce ta fi kowa yawan masu rajista da 826,850, wanda ya yi daidai da kashi 10.32 cikin 100. Sai Legas da 604,619 (kashi 7.56%), da Ogun mai 510,062 (6.37%).

    Jihar da ta fi ƙarancin masu rajista ita ce Yobe da mutum 2,714 kacal - wato kashi 0.03 cikin 100.

    Haka kuma, an dakatar da rajistar a Jihar Anambra bisa tanadin sashe na 9 (6) na Dokar Zabe ta 2022, har sai bayan zaɓen gwamna da za a gudanar ranar 8 ga watan Nuwamba.

    Rahoton ya nuna cewa mata (4,190,890) sun fi maza yin rajistar a matakin farko, idan aka kwatanta da maza (3,812,306).

  8. Labarai da dumi-dumi, Sai ranar Litinin za a bayyana sakamakon zaɓen Kamaru

    Zaɓen Kamaru

    Asalin hoton, Reuters

    Majalisar tsarin mulki ta Kamaru ta ce sai a ranar Litinin mai zuwa za ta sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar tun ranar 12 ga watan Oktoba.

    Sanarwar da Constitutional Council ta fitar a yau Laraba na zuwa ne bayan ta kammala zaman sauraron ƙorafe-ƙorafe a yau, inda ta yi watsi da akasarin buƙatun soke wani ɓangare ko kuma baki ɗayan zaɓen.

    Sanarwar ta ce za a sanar da sakamakon da misalin ƙarfe 11:00 na safiya agogon ƙasar a birnin Yaounde..

    A makon da ya gabata ne majalisar ta ce akwai yiwuwar za ta fitar da sakamakon a gobe Alhamis kafin ta sauya shawara a yanzu.

    Tuni mazauna biranen ƙasar suka fantsama tituna domin yin zanga-zangar nuna ɓacin rai kan zargin yin maguɗi a zaɓen.

    Ɗantakarar adawa Issa Tchiroma Bakary ya ayyana kansa a matsayin wanda ya yi nasara kuma ya kira Shugaban Ƙasa Paul Biya ya amince da shan kaye. Sai dai gwamnatin ƙasar ta yi watsi da sanarwar tasa.

  9. Tallafin rigakafin polio na duniya zai ragu da kashi 30 a 2026

    Rigakafin polio

    Asalin hoton, Getty Images

    An rage kasafin kudin shirin kawar da cutukan Polio na duniya mai suna GPEI da kashi 30 cikin 100 a shekarar 2026.

    Shirin da ke haɗa ƙungiyoyi kamar hukumar lafiya ta duniya WHO da Gidauniyar Gates, GPEI ya ce akwai gibin dala biliyan 1.7 cikin kasafin kudin har zuwa shekarar 2029.

    Babban dalilin wannan giɓin shi ne raguwar tallafin ƙasashen waje, musamman Amurka, wadda take rage tallafin da ta saba bai wa WHO.

    Sakamakon wannan raguwar, za a samu raguwar ayyuka a wuraren da ba su da haɗarin kamuwa da cutar, sai dai idan aka samu ɓarkewar annoba, kuma za a mayar da hankali kan inganta yadda ake gudanar da aikin.

    Jamal Ahmed, daraktan shirin kawar da polio na WHO, ya ce: “Raguwar tallafin da aka samu yna nufin wasu ayyuka ba za su gudana ba.”

    Sauran ƙasashen da ke bayar da gudunmawar kuɗi kamar Jamus da Birtaniya ma sun rage tallafin da suke bayarwa, in ji mai magana da yawun GPEI.

  10. Isra'ila ta karya dokokin duniya wajen hana shigar kayan agaji Gaza - Kotun Duniya

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Kotun duniya ICJ ta bayyana cewa Isra’ila ta karya dokokin ƙasashen duniya lokacin da ta hana shigar da kayan agaji ga Falasɗinawa a Zirin Gaza.

    A lokacin da ta bayyana ra'ayinta wanda ke a matsayin shawara, kotun ta ce kasancewar Isra’ila ce mai mamaye yankin akwai wajabcin bayar da damar shigar da taimako cikin sauƙi zuwa yankin a kanta, sannan ya zama wajibi ta kauce wa yin amfani da yunwa a matsayin makamin yaƙi.

    Kotun ta kuma bayyana cewa Isra’ila na da wajabcin haɗa hannu da ƙungiyoyin agaji na Majalisar Dinkin Duniya (MDD), musamman Unrwa.

    Babban zauren MDD ne ya buƙaci kotun ta bayyana ra'ayinta kan lamarin bayan da Isra'ila ta haramta ayyukan hukumar bayar da agajin jin ƙai ta Unrwa tana zargin ƙungiyar da haɗa kai da Hamas.

  11. Zaɓen shugaban Kamaru: Magoya bayan ƴan adawa na ci gaba da zanga-zanga

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Magoya bayan babban ɗan'adawa a Kamaru Issa Tchiroma Bakary sun sake fitowa kan wasu titunan birnin Garwa da ke arewacin kasar inda suke zanga zanga a yayin da ake dakon sakamakon zaben shugaban kasar.

    A gobe Alhamis ne ake sa ran sanar da sakamakon zaben inda sakamakon farko-farko da ke fitowa ke nuna cewa shugaban kasar mai ci Paul Biya ne ke kan gaba.

    Masu zanga zangar dai na kiran da ayi adalci wajen sanar da wanda ya samu nasara a zaben shugaban kasar.

    Yau Laraba ne ya kamata a ce dokar hana hawa babur ta fara aiki a wasu biranen ƙasar, musamman Garoua.

    Hakan na zuwa ne sakamakon arangama da aka samu tsakanin magoya bayan Issa Tchiroma Bakary da jami'an tsaro a ranar Talata.

    Hakan ya biyo bayan korafe-korafen jam’iyyar adawa kan yadda aka gudanar da zaben, inda suke zargin cewa gwamnati na ƙoƙarin murɗe sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da aka yi a ƙasar.

    A garin Garoua na arewacin kasar, an kama aƙalla masu zanga-zanga 20 a ranar 21 ga Oktoba, kuma ana sa ran za su fuskanci shari’ar soji bisa laifin tada tarzoma da rikici, in ji Ministan Gudanar da Harkokin Cikin Gida, Paul Atanga Nji.

    A kokarin daƙile rikice-rikicen, hukumomi a sashin Menoua na yammacin Kamaru sun haramta duk wasu zanga-zangar jama’a da tafiye-tafiye da hawa babur da kuma sayar da mai a kwalabe tun daga ranar 21 ga Oktoba har zuwa wani lokaci da ba a kayyade ba.

  12. Me ya sa ake samun yawan fashewar tankar man fetur a Najeriya?

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Aƙalla mutum 33 ne suka mutu a fashewar tankar man fetur ta baya-bayan nan bayan kifewarta a titin Agaie zuwa Bida cikin ƙaramar hukumar Katcha a lardin Essa na jihar Neja.

    Rahotanni sun ambato Aishatu Sa'adu, kwamandar hukumar kiyaye aukuwar haɗurra ta jihar Neja na cewa tankar ta zame a kan titi, lokacin da direbanta ya yi ƙoƙarin kauce wa wani rami.

    Bayanai sun kuma ce aƙalla mutum 40 ne suka ji raunuka a gobarar da ta tashi, yayin da aka taru domin kwalfar man fetur da ke tsiyaya daga tankar da ta faɗi.

    Babban Daraktan hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Neja, Abdullahi Baba-Ara ya ce da safiyar Larabar nan ƙarin mutum uku suka cika a asibiti, abin da ya sa alƙaluman mamatan ya kai 33 yanzu.

    Ya ce tankar da ta faɗi ta taho ne inda ta gogi wata 'yar'uwarta da take giftawa a lokacin.

  13. Babu hujjar da ke nuna kisan ƙare-dangi kan wasu mabiya addini - Sarkin Musulmi

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Mai alfarma Sarkin Musulmi a Najeriya, Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya bayyana cewa babu wasu bayanan da ke nuna cewa an yi wa masu bin wani addini Krista ko Musulmi kisan ƙare-dangi a ƙasar.

    Sarkin ya faɗi hakan ne a yayin buɗe taron Majalisar Sarakunan Arewa a Birnin Kebbi, 2025.

    Sarkin ya ce, “Babu yadda za a kashe wani mutum, ko Musulmi ko Kirista, ba tare da sanin sarakuna ko shugabannin al’ummar da wannan mutumin ya fito ba.”

    Ya kuma ƙalubalanci kowa, a cikin gida ko waje, da su kawo hujja ta gaske kan wani kisan ƙare dangi a Najeriya.”

    Sultan Sa’ad ya gargadi jama’a da kada su gaskata duk abin da suka gani ko karanta a kafafen sada zumunta, yana mai cewa yawancin bayanan da ake yaɗawa ba gaskiya bane.

    “Yawancin abin da aka wallafa a kafafen sada zumunta ba gaskiya bane. Dole mutane su tabbatar da sahihancin bayani kafin su ɗauke shi a matsayin gaskiya,” in ji shi.

    Sarkin ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta hanzarta tsara dokoki da za su kula da ayyukan masu amfani da kafafen sada zumunta domin rage yaɗa labaran ƙarya.

  14. Kotu ba ta da hurumin yi wa wasu auren dole - Ƙungiyar Lauyoyi

    ...

    Asalin hoton, FB/Maiwushirya

    Ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya ta ce matakin kotun Majistare a Kano na ‘tilasta aure’ tsakanin Ashiru Idris Maiwushirya da Basira Ƴarguda ya ci karo da ƴancinsu na bil'adama.

    Ta kuma ce hakan zai ƙara rage amincin da jama’a ke da shi ga ɓangaren shari’a.

    A ranar Litinin ne dai kotun ta bai wa hukumar Hisbah ta Kano umarnin ɗaura aure tsakanin matasan biyu, bayan wasu bidiyoyi da suka riƙa wallafawa a shafukan sada zumunta da ke nuna kusanci a tsakaninsu.

    Kotun ta yanke hukuncin ne bayan an gurfanar da matasan biyu a gabanta, bisa zargin su da yaɗa bidiyoyi na 'rashin ɗa'a' a shafin sada zumunta. Tuni dai hukumar Hisba ta ce ta fara shirye-shiryen auren ƴan tiktok ɗin da ke jihar.

  15. An ba da umarnin yin bincike kan jerin sunayen masu laifin da Tinubu ya wa Afuwa

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Babban ministan shari'a na Najeriya kuma babban lauyan gwamnati, Lateef Fagbemi, ya bayar da umarni ga hukumomi da dama su gudanar da bincike kan jerin sunayen masu laifin da shugaban ƙasar Bola Tinubu ya yi wa afuwa, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

    Hukumomin da za su gudanar da wannan binciken sun haɗa da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC), hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA), da kuma Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya.

    Ana hasashen cewa binciken zai iya kai ga cire fiye da rabin sunayen mutanen da aka yi wa afuwa.

    Shugaba Bola Ahmed Tinubu dai na jira a mika masa jerin sunayen da aka tantance domin ya sanya hannu na karshe, a yunkurin tabbatar da cewa duk wanda zai amfana daga afuwar ya cancanta.

    Tinubu dai ya yi amfani da ikon da ƙundin tsarin mulki ya ba shi wajen yi wa mutum 175 da aka samu da laifuka daban-daban afuwa.

    Fagbem ne ya sanar da hakan a yayin taron Majalisar mahukunta da aka gudanar a ranar Alhamis, 9 ga Oktoba, 2025.

  16. Majalisar dattawa za ta yi dokar ɗaurin rai da rai ga masu lalata ƙananan yara

    ...

    Asalin hoton, @NgrSenate

    Majalisar Dattawa ta gabatar da wani muhimmin ƙudurin doka da zai bayar da damar yanke hukuncin daurin rai da rai ga duk wanda aka samu da laifin lalata ƙananan yara ba tare da yiwuwar biyan tara ba.

    Wannan mataki na daga cikin sauye-sauyen da aka yi wa Dokar Laifuka ta shekarar 2025.

    Shugaban Majalisar, Opeyemi Bamidele, wanda ya jagoranci muhawarar kan kudurin, ya ce sauye-sauyen na da nufin karfafa dokokin kare yara da kuma kawar da nuna bambanci a kan jinsi wajen gurfanar da masu laifukan lalata.

    A halin yanzu, hukuncin shekaru biyar a gidan yari ake yanke wa wanda aka kama da laifin lalata yara, amma a ƙarkashin wannan kuduri idan aka amince da shi, hukuncin rai da rai zai fuskanta.

    Bugu da ƙari, Majalisar ta kuma gabatar da hukuncin shekaru 10 a gidan yari ga masu aikata fyaɗe.

  17. ASUU ta janye yajin aiki, ta bai wa gwamnati wata ɗaya ta cika buƙatunta

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar malaman jami’o’in Najeriya ASUU ta dakatar da yajin aikin gargadi na tsawon makonni biyu da ta fara, inda ta bai wa gwamnatin ƙasar wata ɗaya domin ta magance buƙatunta.

    Shugaban ƙungiyar, farfesa Chris Piwunayayin wata ganawa da manema labarai, ya ce ƙungiyar ta yanke shawarar dakatar da yajin aikin ne domin bai wa gwamnati dama ta nuna kyakkyawan niyya wajen tattauna matsalolin da suka shafi albashi da kayan aiki da inganta yanayin aiki a jami’o’in kasar.

    Ƙungiyar ta ce abun da yasa suka janye yajin aikin shine gwamnati ta gabatar da matsayarta kan sabunta yarjejeniysar shekarar 2009 kuma da kiraye-kirayen da suka samu daga mutane da dama daga ƙasar domin sun janye yajin aikin.

    Wannan ne ya sa ƙungiyar ta bai wa gwamnatin ƙasar wata ɗaya domin ta magance buƙatunta.

    Kungiyar ta kuma gargadi gwamnati da kada ta yi wasa da wannan lokaci, inda ta ce idan buƙatun nasu basu samu warware ba, za ta ɗauki mataki na gaba.

    Wasu daga cikin buƙatun ƙungiyar sun haɗa da;

    • Sabunta yarjejeniyar shekarar 2009
    • Bayar da kuɗaɗen gudanarwa ga jami'o'i
    • Biyan su haƙƙinsu na aikin da suka yi a baya na wata uku da rabi.
    • Tabbatar da an tura kuɗaɗensu da ake cirewa daga albashinsu zuwa ƙungiyoyinsu.

    Shugaban ƙungiyar malaman jami'o'in Najeriya (ASUU) reshen Jami'ar Bayero ta Kano (BUK), Farfesa Ibrahim Tahir Suraj, ya shaidawa BBC cewa duk da cewa gwamnati ta fara biyan wasu buƙatunsu kamar tura kuɗaɗensu da ake cirewa daga albashinsu zuwa ƙungiyoyinsu, inda ya ce an biya su na wata ɗaya, babbar buƙatar da suke so gwamnati ta warwaremu shine na Sabunta yarjejeniyar shekarar 2009.

  18. Mutum fiye da 40 sun mutu bayan mummunan hatsarin mota a Uganda

    ...

    Asalin hoton, Joseph Muyingo

    Rundunar ‘yan sandan Uganda ta ce mutane 46 ne suka mutu bayan wasu motoci da dama suka yi karo a babban titin Kampala-Gulu, lamarin da ya faru da misalin ƙarfe 12:15 na dare.

    A baya ‘yan sanda sun sanar da cewa mutum 63 ne suka mutu, amma daga bisani suka gyara bayan sun gano cewa wasu daga cikin mutanen da aka ƙirga sun suma ne kawai.

    Rahoton ‘yan sandan ya bayyana cewa hatsarin ya faru ne lokacin da motoci biyu masu ɗaukar fasinjoji suka yi ƙoƙarin wuce wata babbar mota lamarin da ya janyo yin karo da sauran motoci wanda ya haifar da hatsarin da ya janyo mutuwar mutane da dama da kuma raunata wasu.

    An kai waɗanda suka jikkata zuwa asibitoci daban-daban a garin Kiryandongo, yayin da aka ƙaddamar da bincike kan musabbabin lamarin.

    ...

    Asalin hoton, Joseph Muyingo

    ...

    Asalin hoton, Joseph Muyingo

    ...

    Asalin hoton, Joseph Muyingo

  19. Kotun duniya za ta bayar da ra’ayi kan ikon Isra’ila a kan hukumomin MDD a Falasdinu

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Kotun duniya ICJ na shirin gabatar da wani muhimmin ra’ayi a yau, kan ko Isra’ila na da wani nauyi a shari’ance dangane da hukumomin Majalisar Dinkin Duniya da ke aiki a yankunan Falasdinawa da ta mamaye.

    Hukuncin dai zai kasance martani ga bukatar da Majalisar Dinkin Duniya ta mika ta neman a fayyace komai.

    Kotun za ta kuma yi ƙarin bayani a kan ko matakin da Isra'ila ta dauka na soke hukumar kula da 'yan gudun hijirar Falasdinawa ta UNRWA ya saɓa wa yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya.

    Haka kuma za ta yi ƙarin bayani kan ko takunkumin da Isra'ila ta sanya na hana shigar da kayan jin kai Gaza ya saɓa ƙa'ida.

    Duk da cewa ba lallai ne a aiwatar da abun da za ta ce ba, sai dai ra'ayin kotun na da matuƙar tasiri a Diflomasiyyance.

  20. Za a tattauna kan mataki na gaba na yarjejeniyar zaman lafiya a Gaza

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Mataimakin shugaban Amurka, JD Vance, zai gana da firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu don tattauna kan mataki na gaba na yarjejeniyar zaman lafiya a Gaza.

    Bayan ya isa ƙasar a ranar Talata, Vance ya ce an samu ci gaba fiye da yadda ake tsammani.

    Ana sa ran zai matsa wa shugabannin Isra'ilar lamba don su ci gaba da tattaunawa game da batun.

    Amurka dai na son a ci gaba da shirin kafa rundunar tabbatar da zaman lafiya ta kasa da kasa da kafa sabuwar gwamnati a Gaza da kuma kwance ɗamarar Hamas.