Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 19/06/2025.

Rahoto kai-tsaye

Daga Haruna Kakangi da Aisha Babangida

  1. Bidiyon ɓarnar da harin Iran ya yi wa ciki da wajen asibitin Isra'ila a Beersheba

  2. Isra'ilawa na ɗaga ɓaraguzai don neman waɗanda suka maƙale bayan harin Iran

    Hukumomin Isra’ila sun ce mutum uku sun jikkata sosai sakamakon harin makami mai linzami da Iran ta harba zuwa yankin a baya-bayan nan.

    Harin ya lalata gine-gine ciki harda asibitin Soroka na Isra'ila, lamarin da ya sa Isra'ilawa da ƴan sanda da ma'aikatan ceto ke ɗaga ɓaraguzai don neman waɗanda suka maƙale bayan harin na Iran

    Wani mutum, wanda harin da makamai masu linzami da Iran ta kai ya rushe masa ɗaki ya samu ya tsere.

  3. Wane bom mai ƙarfi na Amurka ne zai iya lalata rumbunan nukiliyar Iran?

    Daga cikin makaman da za a iya harbawa su keta ƙarƙashin ƙasa har su iso wurin da rumbunan ajiyar sinadaran nukiliyar Iran suke, daya ne kawai ba a yi amfani da shi ba zuwa yanzu, kuma Isra'ila ba ta da shi a yanzu.

    Makamin shi ne GBU-57A/B - wanda ya kasance bom marar nukiliya mafi ƙarfi a duniya - da zai iya lalata rumbunan ajiyar sinadaran ƙera makamin nukiliya, kuma Amurka ce kadai ta mallake shi a duniya.

    Wannan tsararren makami mai nauyin kilogiram 13,600 zai iya ketawa ƙarƙashin ƙasa domin wargaza rumbunan sinadaran ƙera nukiliyar Iran da ke binne can ƙarƙashin duwatsu.

    Zuwa yanzu Amurka ba ta bai wa Isra'ila makamain ba.

    To amma shi wannan makami ya yake, mene ne kuma ƙalubalen amfani da shi.

  4. Harin Iran ya lalata wani asibiti a Isra'ila