Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 19/06/2025.

Rahoto kai-tsaye

Daga Haruna Kakangi da Aisha Babangida

  1. Za mu fitar da matsayarmu kan ko za mu shigar wa Isra'ila yaƙi nan da mako biyu - Trump

    Shugaba Trump ya ce sai nan da mako biyu zai yanke hukunci kan ko zai shigar wa Isra'ila yaƙin da take yi da Iran ko kuma akasin haka.

    A wata sanarwa da sakatariyar yaɗa labaran fadar gwmanatin Amurka ta karanto, Shugaban ya ce akwai yiwuwar a zauna a teburin sulhu.

    Kafin wannan sanarwa, mataimakin ministan harkokin wajen Iran, Saeed Khatib-zadeh ya fada wa BBC cewa ba su da matsalar tattaunawar diflomasiya idan aka daina jefa musu bama-bamai.

    Ya kuma ce duk da Iran a shirye take ta shiga tattaunawar diflomasiya - babu batun ragawa Isra'ila.

    Kuma illahirin yankin zai shiga cikin bala'i muddin Amurka ta yi ƙoƙarin shiga yaƙin.

  2. Finland za ta fice daga yarjejeniyar hana mallakar nakiyoyi

    Finland ta yanke hukuncin ficewa daga yarjejeniyar hana mallakar nakiyoyi saboda fargabar barazanar soji daga Rasha.

    Majalisar dokokin Finland ce ta kaɗa kuri'ar ficewa daga yarjejeniyar wadda ƙasashe irin su Lithuania, Latvia, Estonia and Poland duk ke shirin ficewa daga cikinta.

    Shugaban Finland, Alexander Stubb, ya ce bukatar hakan ta taso ne ganin cewa Rasha ƙasa ce mai danniya wadda ke amfani da nakiyoyi cikin rashin imani.

    Masu fafutika ciki harda wadanda suka lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel, sun bayyana lamari a matsayin mai ban takaici kasancewar zai jefa rayukan al'umma a cikin hadari.

  3. Shugaban WHO ya yi allah wadai da hari kan cibiyoyin lafiya

    Babban daraktan Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ya yi alla wadai da hare-hare kan cibiyoyin lafiya a rikicn da ake yi tsakanin Isra'ila da Iran.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Dakta Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce ''rahotonnin hare-hare kan cibiyar lafiyar abin razani ne''

    Mista Tedros ya bayar da misali kan harin da aka kai asibitin Soroka a Isra'ila da rahoton mutuwar ma'aikatan agaji na Red Cresent a Iran.

    "Muna kira ga duka ɓangarorin da ke rikici da juna su kauce wa hari kan cibiyoyin lafiya, da ma'aikatan lafiya da majinyata a kowane lokaci. Babban magani shi ne zaman lafiya," kamar yadda ya rubuta.

  4. Ministan tsaron Isra'ila ya ce ba za su bar Ayatollah Khamenei a raye ba

    Ministan tsaron Isra'ila ya ce ba zai yiwu su bar jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei a raye ba.

    Israel Katz ya yi barazana ga Ayatollah yana mai cewa ya zama tilas ya ɗauki alhakin hare-hare da makamai masu linzami da Iran ta yi a kan wani asibiti da ke kusa da Tel Aviv.

    Kafin harin an yi ƙoƙari kwashe marasa lafiya da dama, saboda a ceto rayukansu.

    Iran ta ce ta kai harin ne kan sansanin sojoji da ke kusa da asibitin.

    Kalaman Mista Katz na nuna cewa sojojin Isra'ila a yanzu za su yi ƙoƙarin ganin sun kashe Ayatollah -- bayan kashe kwamandojinsa na soji da dama.

  5. Dubban ƴan Afghanistan na cikin masu tserewa daga Iran

    Wakilin BBC da yanzu haka ke lardn Herat da ke yammacin Afghanistan - da ya yi iyaka da Iran - inda dubban ƴan Afghanistan ke komawa a kowace rana.

    ''Na hadu da gomman ƴan Afganinstan masu ɗauke da cikakkun takardun izinin zama a Iran amma suka guje wa ƙasar bayan harin Isa'ila'', n ji wakilin na BBC

    Saifullahi mai shekara 24 daga Kabul na daga cikinsu. Ya shafe wata biyu yana zaune a Esfahan na Iran, ya kuma bayyana yadda ya sha wahala kafin samun tikitin jirgi.

    ''Na shafe tsawon kwana uku kafin samun tikitin komawa Afghanistan. Kuma farashinsa na ninka har sau uku sannan ga wahalar samu.''

    Esfahan na a tsakiyar Iran, wanda ke da nisan kilomita 240 kudu da Tehran babban birnin ƙasar. Kuma hare-haren Isra'ila sun faɗa kan birnin.

    Mehran mai shekara 35 na aiki ne a wani kamfanin gine-gine na tsawon shekaru a Iran.

    Ya ce ya ga ƴan Iran da kansu na barin birane zuwa ƙauyuka. Ya ƙara da cewa farashin abinci ya yi tashin gwauron zaɓo, biredi ya yi wahala ko a gidajen biredi.

    “Ina aiki a wasu wurare har guda uku da ake gine-gine, waɗanda duka aka dakatar da su bayan harin. don haka na ɗauki matakin ficewa daga ƙasar.

  6. Majalisar tattalin arzikin Najeriya ta ɗage zamanta karo na 150

    Majalisar tattalin Arzikin Najeriya ta ɗage zamanta karo na 150 da ta tsara gudanarwa yau Alhamis 19 ga watan Yunin 2025, kamar yadda gidan talbijin na Channels ya ruwaito.

    Majalisar - wadda mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ke jagoranta - na da alhakin shawartar shugaban ƙasa kan abubuwan da suka shafi tattalin razikin ƙasa, tare da ɗaukar wasu matakai masu alaƙa da ci gaban tattalin arzikin ƙasa.

    Mambobin majalisar sun ƙunshin gwamnonin jihohin ƙasar 36 da gwamnan Babban Bankin ƙasar da wasu manyan jami'an gwamnati masu alaƙa da tattalin arzikin.

    Babu dai wani dalili a hukumance na ɗage zaman majalisar tattalin arzikin, to amma wasu na ganin hakan ba ya rasa nasaba da taron ƙaddamar da ayyuka da shugaban ƙasar ke jagoranta a jihar Kaduna, inda aƙalla gwamnoni 11 ke halarta tare da Tinubun.

  7. China da Rasha sun buƙaci amfani da lalama don kawo ƙarshen yaƙin Isra'ila da Iran

    Shugaban China da na Rasha sun yi alla-wadai da hare-haren Isra'ila kan Iran tare da kiran a tsagaita wuta.

    Shugaba Xi Jinping da Vladimir Putin sun tattauna ta waya inda suka nuna goyon-bayan amfani da hanyoyin diflomasiya wajen shawo kan rikicin.

    Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Aragchi zai tattauna da takwarorinsa na Faransa da Jamus da Birtaniya a Geneva a gobe Juma'a.

    Mataimakinsa, Saeed Khatibzadeh ya shaida wa BBC cewa, Iran a shirye take ta shiga tattaunawar diflomasiya, sai dai babu batun ragawa Isra'ila.

  8. Netanyahu ya ziyarci asibitin Soroka da harin Iran ya lalata

    Firaministan Isr'ila Benjamin Netanyahu ya ziyarci asibitin Soroka ta harin makami mai linzami na Iran ya faɗawa.

    Alƙaluman jami'ai sun ce fiye da mutum 70 ne suka jikkata a harin da aka ƙaddamar cikin dare.

    Asibitin na Soroka na a birnin Beersheba da ke kudancin ƙasar

  9. Tinubu na ziyarar aiki a jihar Kaduna

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu na ziyarar aiki a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin ƙasar.

    Tinubu na ziyarar ne domin ƙaddamar da wasu ayyuka da gwamnan jihar, Sanat Uba Sani ya aiwata tsawon shekara biyu da ya shafe yana mulkin jihar.

    Cikin ayyukan da shugaban ya ƙaddamar sun haɗa da wani asibitin ƙwararru mai gadaje 300 da gwamnatin jihar ta gina don bunƙasa harkokin lafiya.

    Haka kuma shugaban ya ƙaddamar da cibiyar koyar da sana'o'i, sai kuma motocin safa masu amfani da iskar gas ta CNG guda 100.

    Shugaba Tinubu na samun rakiyar mataikaminsa na musamman kan harkokin siyasa, Sanata Ibrahim Masara, da mai taimaka masa kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu da wasu jiga-jigan gwamnati.

    Haka kuma shugaban ya samu tarba daga gwamnan jihar Kaduna tare da takwarorinsa na makwabtan jihohi.

    Wakilin BBC da ke birnin Kaduna, ya ce ɗaruruwan mutane ne suka yi dandazo domin yi wa shugaban maraba tare da ɗaga tutoci da alluna ɗauke da rubuce-rubuce.

    Ziyarar shugaban na zuwa ne kwana guda bayan ziyarar jaje da ya kai jihar Benue da ke fama da rikice-rikice.

  10. Starmer ya shawarci Trump kada ya far wa Iran

    Firaministan Birtaniya, Keir Starmer ya buƙaci Donald Trump kada ya ɗauki matakin soji kan Iran.

    Mista Starmer ya ce akwai ''mummunan hatsarin bazuwar'' yaƙin, inda ya yi kira ga duka ɓangarorin sun rungumi sulhu.

    Ya ƙara da cewa a baya an samu ''jerin tattauna masu yawa da Amurka, kuma ina ganin wanann ita ce hanyar warware matslar''.

    Kalaman nasa na zuwa ne yayin da sakataren harkokin wajensa, David Lammy ke shirin ganawa da takwaransa na Amurka, Marco Rubio kan yadda za a taƙaita bazuwar yaƙin.

    Da maraicen yau Alhamis ne Mista Lammy da Mista Rubio za su gana don tattauna halin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya.

  11. Kotu ta bayar da belin Sanata Natasha kan naira miliyan 50

    Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da belin Sanata Natasha kan kuɗi naira miliyan 50.

    Haka kuma kotun ta ɗage ƙarar zuwa ranar 23 ga watan Satumba domin ci gaba da sauraronta.

    Gwamnatin Najeriya ce dai ta gurfanar da ƴarmajalisar a gaban kotu kan zargin ɓata sunan Shugaban Majalisar Dattawa, Godswil Akpabio da tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello.

  12. Jagoran addinin Iran ya buƙaci Iraniyawa su 'ci gaba da jajircewa'

    Jagora addinin Iran, Ayatolla Ali Khamenei ya shaida wa ƴanƙasar kada su karaya.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, jagoran addinin ya ce shaida wa Iraniyawa cewa ''idan maƙiya suka gano gazawarku, ba za su ƙyale ku ba''.

    Jagoran addinin ya kuma yi kira da ƴanƙasar su “ci gaba da jajircewa kamar yadda aka san su, ku ci gaba da wannan ɗabi'a ta ƙarfafa kanku.,”

  13. Hotunan ɓarnar da hare-haren Isra'ila suka yi a Iran

    A ranar 17 ga watn Yuni ne wani jrigin saman Isra'ila ya faɗa kan shalkwatar kafar yaɗa labaran Iran a birnin Tehran.

    Harin ya sa an katse yaɗa shirye-shirye a lokacin da aka ƙaddamar da shi.

    Kafororin yaɗa labaran Iran sun ce aƙalla mutum guda ya mutu a harin.

    Ga wasu hotuna da ke nuna irin ɓarnar da harin ya yi

  14. Waɗanne makamai ne Amurka ke turawa Gabas ta Tsakiya?

    Yayin da ake ci gaba da raɗe-raɗin yiwuwar shigar Amurka yaƙin Isara'ila don kai wa Iran hare-hare, tuni ƙasar ta fara tura wasu makaman yaƙi zuwa yankin Gabas ta Tsakiya.

    Kawo yanzu akwai aƙalla dakarun Amurka 40,000 a yankin Gabas ta Tsakiya, kamar yadda wani jami'in Amurka ya bayyana a farkon wannan wata.

    Aƙalla jiragen sojin Amurka 30 ne aka aika daga sansanonin soji a Amurka zuwa wasu ƙasashen Turai cikin kwanakin nan.

    Duka jiragen tankokin yaƙi ne da ake ake amfani da su wajen zuba wa jiragen yai mai.

    An ga wani jirgin ruwan Amurka na dakon kaya mai suna 'USS Nimitz' na keta tekun kudancin China ya nufi Gabas ta Tsakiya ɗauke da na'urorin kakkaɓo makamai masu linzami.

    Akwai kuma wasu jirajen ruwa na yaƙi da ke tekun Oman da na Persa, kuma tuni suna taimaka wa Ira'ila wajen kakakɓo makamai masu linzami da Iran ta harba.

    Amurkan ta kuma tura jiragen yaƙi samfurin F-16 da F-22 da F-35 zuwa sansanoninta a Gabas ta Tsakiya, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.

  15. Rasha ta gargaɗi Amurka kan shiga yaƙin Isra'ila da Iran

    Kakakin gwamnatin Rasha, Dmitry Peskov ya shaida wa kamfanin dillancin labaran ƙasar TASS cewa shigar Amurka cikin yaƙin Isra'ila da Iran ka iya haifar da ''mummunar ƙazancewar yaƙin''.

    Amurka da Rasha na goyon bayan ɓangarorin biyu da ke yaƙi da juna.

    Yayin da Donald Trump ya buƙaci Iran ta “miƙa wuya ba tare da sharadi ba”, kuma rahotonni ke cewa yana duba yiwuwar kai mata hari, ita kuwa Rasha na kallon Iran a matsayin babbar ƙawa.

    A farkon wannan shekarar ne, Vladimir Putin ya sanya hannu kan wata ƙawance mai ƙarfi da takwaransa na Iran, Masoud Pezeshkian, inda wani ɓangare na yarjejeniyar ya buƙaci ƙulla ƙawancen tsaro tsakanin ƙasashen biyu.

    Haka kuma Iran na samar wa Rasha jirage marasa matuƙa, da suka taka muhimmiyar rawa a yaƙin da ƙasar ke yi da Ukraine.

    Ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta yi Allah wadai da hare-haren Isra'ila kan Iran, haka kuma jiya mataimakin ministan harkokin wajen ƙasar ya gargaɗi Amurka da kada ta bai wa Isra'ila taimakon soji.

    “Saboda hakan zai iya dagula yanayin da ake ciki,” kamar yadda ya bayyana.

    Da alama rikicin zai haifar da cin karo tsakanin Rasha da Amurka, kuma zai iya zama babbar barazana a dangantakar Amurka da Rasha, wadda ta ɗan fara inganta bayan sake zaɓar Donald Trump.

  16. Gwamnatin Najeriya ta gurfanar da Sanata Natasha a gaban kotu

    Ƴar Majalisar Dattawan Najeriya mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta gurfana a gaban babbar kotun tarayya a ke Abuja, saboda zargin ɓata suna.

    Gwamnatin Najeriya ce ta shigar da ƙarar Sanata Natasha bisa zarge-zarge uku da suka ƙunshi zargin ɓata sunan shugaban majalisar dattawan ƙasar, Sanat Godswill Akpabio da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.

    An tsaurara matakan tsaro a harabar kotun, yayin da ƴar majalisar ta isa tare da mijinta da wasu mutane da ke goyon bayanta ciki har da tsohuwar ministar ilimin ƙasar ne, Oby Ezekwesili da ƴar gwagwarmaya Aisha yesufu

    Gwamnatin Najeriya na zargin ƴar majalisar da furta wasu kamalam ''ɓatantanci yayin da take da yaƙinin cewa irin waɗanan kalamai ka iya shafar ƙimar mutumin da aka furta su a kansa.

    A watan Maris ne dai Majalisar Dattawan Najeriya ta dakatar da yar majalisar na tsawo wata shida, kan zarginta da aikata wasu abubuwa da suka saɓa ƙa'idar majalisar.

    Ƴar majalisar dai ta zargi shugaban majalisar dattawan ƙasar da yunƙurin cin zarafinta ta hanyar lalata, zargin da Mista Akpabio ya sha musantawa.

  17. Har yanzu duniya na jiran matakin da Trump zai ɗauka kan Iran

    Shugaban Amurka, Donald Trump dai har yanzu ya ƙi bayyana ko Amurka za ta shiga hare-haren Isra’ila kan Iran yayin da duniya ke jiran matakin da zai ɗauka.

    A lokacin da aka tambaye shi a filin Fadar White House jiya, Trump ya ce, “Zan iya shiga kuma zan iya ƙi."

    Bayan haka, rahotanni sun ce Trump ya amince da shirin kai hari amma yana jiran ko Iran za ta yi watsi da shirin nukiliyarta.

    Iran ta shaida wa Majalisar Dinkin Duniya cewa ba za ta yi sulhu a karkashin matsin lamba ba.

    Tsohuwar mai ba da shawara kan tsaron ƙasa ta Trump, KT McFarland, ta ce Trump zai iya yanke shawara dab da lokacin da za a ƙaddamar da harin.

  18. Iran ta sha alwashin koya wa duk wanda ya taɓa ta darasi

    Mataimakin ministan harkokin wajen Iran, Kazem Gharibabadi ya yi gargaɗi ga Amurka yayin da Shugaban ƙasar, Donald Trump ke la'akari da yiwuwar tallafa wa Isra'ila a yaƙin da take yi da Iran.

    Kafafen watsa labaran gwamnati Iran sun ruwaito Gharibabadi yana cewa: “Idan Amurka ta yanke shawarar tsoma baki kai tsaye domin tallafa wa Isra’ila baya, to Iran ta sha alwashin koya musu darasi da kuma kare kanta.”

    Ya ƙara da cewa: “Shawararmu ga Amurka ita ce ko su tsaya a gefe idan har ba za su dakatar da Isra’ila daga kai hare-hare ba,” ko kuma Iran ta tanadi duk wata hanya da za su iya bi domin kare kansu.

  19. Ban fita daga PDP ba - Namadi

    Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Mohammed Namadi Sambo, ya ƙaryata jita-jitar da ke cewa ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC, yana mai jaddada cewa har yanzu shi mamba ne na jam’iyyar PDP.

    A wata sanarwa da tsohon mai taimaka masa a harkar yaɗa labarai, Umar Sani, ya fitar, Namadi Sambo ya bayyana jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta a matsayin ƙarya mai cike da ruɗani da kuma wata don ɓatar da jama'a.

    Sanarwar ta bayyana cewa hoton da ke yawo da ya tayar da wannan jita-jitar wanda ke nuna Sambo tare da gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, tsohon hoto ne da aka ɗauka shekaru da suka wuce a lokacin da gwamnan ya kai masa ziyara ta jaje a gidansa da ke Abuja, bayan rasuwar ɗan uwansa, marigayi Sani Sambo.

    "Wasu na ƙoƙarin amfani da hoton domin yaudarar jama'a da ƙirƙirar labarin da bai da tushe ne kawai." Sanarwar ta ƙara da cewa

    Haka kuma, sanarwar ta jaddada cewa "halartar da Namadi Sambo zai yi wajen ƙaddamar da gadajen asibiti 300 a Kaduna a ranar 19 ga watanYunin 2025, ba ya nufin ya sauya sheƙa ko ya nuna goyon bayan siyasa ga wata jam’iyya."

    Sanarwar ta bayyana cewa shi ne ya fara aikin wannan asibiti tun a lokacin da yake ofis, kuma hakan wani ɓangare ne na gudummawarsa ga ci gaban Jihar Kaduna da hidimar jama'a.

    “Babu wani yunƙuri daga Namadi na sauya sheka zuwa kowace jam’iyya,” in ji sanarwar.

  20. 'Aƙalla mutum 65 ne suka jikkata a Isra'ila'

    Hukumomin agajin gaggawa na Isra’ila sun ce jimillar mutane 65 ke samun kulawa saboda raunukan da suka samu a sabbin hare-haren da Iran ta kai a sassa daban-daban na ƙasar.

    Cikin waɗanda suka jikkata akwai wani mutum ɗan shekara 80 da mata biyu ƴan shekaru 70 da kuma wasu mata biyu masu shekaru 80 da ke cikin matsanacin hali.

    Haka kuma akwai mutum 42 da suka samu ƙananan raunuka, da wasu 18 da suka jikkata sosai yayin da suke ƙoƙarin kauce wa bama-bamai.