Za mu fitar da matsayarmu kan ko za mu shigar wa Isra'ila yaƙi nan da mako biyu - Trump

Asalin hoton, Getty Images
Shugaba Trump ya ce sai nan da mako biyu zai yanke hukunci kan ko zai shigar wa Isra'ila yaƙin da take yi da Iran ko kuma akasin haka.
A wata sanarwa da sakatariyar yaɗa labaran fadar gwmanatin Amurka ta karanto, Shugaban ya ce akwai yiwuwar a zauna a teburin sulhu.
Kafin wannan sanarwa, mataimakin ministan harkokin wajen Iran, Saeed Khatib-zadeh ya fada wa BBC cewa ba su da matsalar tattaunawar diflomasiya idan aka daina jefa musu bama-bamai.
Ya kuma ce duk da Iran a shirye take ta shiga tattaunawar diflomasiya - babu batun ragawa Isra'ila.
Kuma illahirin yankin zai shiga cikin bala'i muddin Amurka ta yi ƙoƙarin shiga yaƙin.























