Man United ta saka Hojlund a kasuwa kan fam miliyan 30
Manchester United ta saka Rasmus Hojlund a kasuwa kan farashin fam miliyan 30 ga duk ƙungiyar dake son sayen ɗan wasan.
Ɗan wasan tawagar Denmark ya ci ƙwallo biyu a wasan da United ta kara da Bournemouth a Chicago ranar Laraba.
United na fatan sayen ɗan wasan RB Leipzig, Benjamin Sesko, wanda Newcastle United itama ke son ɗauka.
An kuma samu labarin cewar Sesco na son komawa Old Trafford da taka leda.
Sai dai koda United za ta sayi Sesco ya zama wajibi ta sayar da wasu ƴan wasanta, domin kashe kuɗi daidai samu, wato financial fair play.
Idan har United ta sayar da Hojlung kan fam miliyan 30 kenan ta faɗi kasuwanci, bayan da darajarsa ta kai fam miliyan 43, wanda yake da sauran yarjejeniyar kaka biyu a Old Trafford.
Kawo yanzu United ta kashe fam miliyan 130 a bana wajen sayen Bryan Mbeumo da kuma Matheus Cunha.