Akwai yiwuwar cewa Rodrygo zai taka leda a Gasar Premier Ingila a kaka mai zuwa yayin da wasu ƙungiyoyi ke nuna sha'awar ɗaukar ɗan wasan, ita kuwa Real Madrid a shirye take ta sayar da shi.
Ɗan wasan bai taka rawar gani a kakar da aka kammala ba kuma ya zura ƙwallo ɗaya ne kawai cikin wasanni 22 tun daga watan Fabrairu zuwa yanzu.
An kuma fitar da shi a hutun rabin lokaci a wasan ƙarshe na gasar Copa del Rey a kakar - lamarin da bai cika faruwa ba.
Bayan zuwan sabon koci Xabi Alonso ƙungiyar, Rodrygo ya kasa samun damar buga wasa inda wasa ɗaya kaɗai ya fara cikin shida a gasar Club world Cup.
Rodrygo ya bayar da ƙwallo aka ci a wasansu da Al-Hilal, amma idan yana buga gefen dama, shi da Alexander-Arnold na kawo cikas a ɓangaren tsaron bayan Real Madrid.
Ɗan wasan kuma ya fi son buga gefen hagu inda Vinicius har da ma Mbappe suka fi son bugawa, duk da cewa Mbappe ma lamba tara yake bugawa.
Yawan ƙwallayen da ya ci a kakar da aka kammala bai kai na Mbappe da Vinicius yawa ba duk da cewa a wasu alƙaluma irin ƙwace ƙwallo, ya fi ƴan wasan biyu.